ABUBUWA GUDA UKU DA SU KA SAKA SHAIƊAN KUKA Daga Shafin Bashir Halilu
قَالَ ابْنُ أَبِي الدُّنْيَا، حَدَّثَنَا إِبْرِاهِيمُ بْنُ رَاشِدٍ، حَدَّثَنَا دَاوُدُ بْنُ مِهْرَانَ، حَدَّثَنَا يَعْقُوبُ الْقُمِّيُّ، عَنْ جَعْفَرٍ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ، قَالَ: : لَمَّا لَعَنَ اللَّهُ تَعَالَى إِبْلِيسَ تَغَيَّرَتْ صُورَتَهُ عَنْ صُورَةِ الْمَلائِكَةِ، فَجَزِعَ فَرَنَّ رَنَّةً فَكُلُّ رَنَّةٍ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مِنْهَا.
قَالَ سَعِيدٌ: وَلَمَّا رَأَى النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَائِمًا يُصَلِّي بِمَكَّةَ رَنَّ رَنَّةً أُخْرَى.
قَالَ سَعِيدٌ وَلَمَّا افْتَتَحَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَكَّةَ رَنَّ رَنَّةً أُخْرَى اجْتَمَعَتْ إليه ذريته.
فقال: ايأسوا أَنْ تَرُدُّوا أُمَّةَ مُحَمَّدٍ إِلَى الشِّرْكِ، وَلَكِنِ افْتِنُوهُمْ فِي دِينِهِمْ، وَأَفْشُوا بَيْنَهُمْ النَّوْحَ وَالشِّعْرَ.
Ibrāhīmu bin Rāshid ya ba mu labari, ya ce: Dāwūd bin Mihrān ya ba mu labari, ya ce: Ya‘aqūbul-Qummī ya ba mu labari daga Ja‘far, daga Sa‘īd bin Jubayr, ya ce:
Lokacin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya la'anci Iblīs, surarsa ta canza daga irin surar Mala'iku. Sai Iblīs ya firgita ƙwarai, ya saki wani irin kuka mai ƙarfi. Kuma kowane irin wannan kuka da zai yi har izuwa ranar Alƙiyama tana da tushe daga wannan rana."
Sa‘īd ya ce:
Lokacin da Annabi ﷺ ya tsaya yana sallah a Makka, nan ma Iblīs ya saki wani irin kuka mai ƙarfi."
Kuma ya ce:
Lokacin da Annabi ﷺ ya ci nasarar buɗe birnin Makka, sai Iblīs ya kuma sakin wani irin kuka mai ƙarfi, inda ‘ya’yansa su ka taru kusa da shi. Sai ya ce musu: 'Ku yanke ƙauna daga mayar da al’ummar Muhammad (ﷺ) zuwa ga shirka! Amma ku ɓatar da su cikin addininsu, ku yaɗa kuka da faɗin baitocin waƙa (shagube da zubar da hawaye) a cikinsu.'"
Duba littafin Maka'idish Shaiɗan na Ibni Abid dunya.
Daga Shafin Bashir Halilu
Comments
Post a Comment