MAKIRCIN SHAIƊAN MAFI GIRMA GA ƊAN ADAM
Daga shafin Bashir Halilu.
- ﴿ مكيدة الشيطان الكبرى ﴾
قَالَ ابْنُ أَبِي الدُّنْيَا : حَدَّثَنَا أَبُو سَلَمَةَ الْمَخْزُومِيُّ، حَدَّثَنَا ابْنُ أَبِي فُدَيْكٍ، عَنِ الضَّحَّاكِ بْنِ عُثْمَانَ، عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ، عَنْ أبيه، عن عائشة رضي الله عَنْهَا : عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
إِنَّ الشَّيْطَانَ يَأْتِي أَحَدَكُمْ فَيَقُولُ مَنْ خَلَقَكَ؟
فَيَقُولُ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى.
فَيَقُولُ مَنْ خَلَقَ اللَّهَ؟
فَإِذَا وَجَدَ أَحَدُكُمْ ذَلِكَ فَلْيَقُلْ:
آمَنْتُ بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ فَإِنَّ ذَلِكَ يُذْهِبُ عَنْهُ.
Ibnu Abid-Dunyā, a cikin littafinsa Maka'idush Shaiɗan, ya ruwaito cewa: Abū Salamatal -Makhzūmīy ya ba mu labari, ya ce: Ibnu Abī Fudayk ya ba mu labari daga Ḍhaḥḥāk bin ‘Usmān daga Hishām bn ‘Urwah daga mahaifinsa (Urwah), daga Nana A’isha – Allah ya yarda da ita – ta ce:
Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Lallai Shaiɗan yana zuwa wurin ɗayanku ya ce masa: Waye ya halicce ka?
Sai ya ce: Allah Mai girma da ɗaukaka.
Sai ya ce masa: To wa ya halicci Allah?”
*To idan ɗayanku ya sami irin wannan (waswasi), to ya ce: "Amantu billahi wa RasuwliHi" domin lallai wannan yana kore (waswasi) daga gare shi.”
❋・────━【❆】━────・❋
Daga shafin Bashir Halilu
Comments
Post a Comment