MUTANE GOMA WAƊANDA ALLAH BA YA SON SU
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ambaci waɗansu halaye a cikin Alƙur'ani, inda Ya bayyana ƙarara cewa ba Ya son mutanen da ke aikata su. Yi ƙoƙari kada ka zama ɗaya daga cikinsu.
Daga Shafin Bashir Halilu.
1. الكافرون KAFURAI
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْكافِرِينَ﴾
[آل عمران: 32]
Haƙiƙa Allah ba Ya son kafurai.
Ayah ta 32, suratun Nisa'i
2. الظالمون AZZALUMAI
> ﴿وَاللَّهُ لا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ﴾
[آل عمران: 57، 140]
Kuma Allah ba Ya son azzalumai.
Suratu Ali Imran ayah ta 140 da kuma ta 157.
3. المعتدون MASU ƘETARE IYAKA KO KARYA DOKOKI.
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ﴾
[البقرة: 190]
Haƙiƙa Allah Ba ya son masu ƙetare iyaka (masu kawo tashin hankali acikin jama'a).
4. المفسدون MAƁARNATA
> ﴿وَاللَّهُ لا يُحِبُّ الْفَسَادَ﴾
[البقرة: 205]
﴿إِنَّهُ لا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ﴾
[القصص: 77]
Kuma Allah ba Ya son ɓarna.
Suratul Baƙarah, ayah ta 205.
Haƙiƙa Shi (Allah) ba Ya son maɓarnata.
Suratul Ƙasasi, aya ta 77.
5. المستكبرون MASU GIRMAN KAI
> ﴿إِنَّهُ لا يُحِبُّ الْمُسْتَكْبِرِينَ﴾
[النحل: 23، لقمان: 18]
Haƙiƙa Shi (Allah) ba Ya son masu griman kai (waɗanda ba son a gaya musu gaskiya kuma suke wulaƙanta mutane).
Suratun Nahli, aya ta 23 da kuma Suratu Luƙman aya ta 18.
6. الخائنون MASU HA'INCI
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ مَنْ كَانَ خَوَّانًا أَثِيمًا﴾
[النساء: 107]
Lallai Allah ba Ya son wanda ya ke cin amanar mutane kuma mai yawan laifi.
Suratun Nisa'i, aya ta 107.
7. الفرحون MASU ALFAHARI
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْفَرِحِينَ﴾
[القصص: 76]
Haƙiƙa Allah ba Ya son masu alfahari (masu cika baki da wani abun duniya da suke da shi don su munantawa mutane ba don godiya ga Allah ba).
Suratul Ƙasasi, aya ta 76.
8. المختال الفخور MASU YIN FARIYA
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ مَنْ كَانَ مُخْتَالًا فَخُورًا﴾
[النساء: 36]
Lalle kuma Allah ba ya son wanda ya kasan mai girman kai, mai fariya.
Suratun Nisa'i aya ta 36
﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَالٍ فَخُورٍ﴾
[لقمان: 18]
Lalle Allah ba Ya son dukkan mai girman kai mai fariya.
Suratu Luƙman ayay ta 18
9. أثيمًا MASU YAWAN AIKATA LAIFUKA
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ مَنْ كَانَ خَوَّانًا أَثِيمًا﴾
[النساء: 107]
Haƙiƙa Allah ba Ya son wanda ya kasance mai wuce haddi kuma mai ƙarya ko yaudara.
Suratun Nisa'i 107
10. الخائنين MASU HA'INCI
> ﴿إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْخَائِنِينَ﴾
[الأنفال: 58]
Haƙiƙa Allah ba Ya son maha'inta.
Muna roƙin Allah Ya tsare mu daga aikata waɗannan laifuka da ma sauran dukkan abinda Allah ba Ya so.
Daga shafin Bashir Halilu.


Comments
Post a Comment