YADDA ZA KA SAMU GAFARAR ZUNUBANKA CIKIN SAUƘI

Daga shafin Bashir Halilu

عَنْ أَنَسٍ رَضِي اللهُ عَنْهُ قالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقولُ: 

{قَالَ اللهُ تَعَالَى: يَا ابْنَ آدَمَ , إِنَّكَ مَا دَعَوْتَنِي وَرَجَوْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ عَلَى مَا كَانَ مِنْكَ وَلاَ أُبَالِي، يَا ابْنَ آدَمَ , لَوْ بَلَغَتْ ذُنُوبُكَ عَنَانَ السَّمَاءِ ثُمَّ اسْتَغْفَرْتَنِي غَفَرْتُ لَكَ، يَا ابْنَ آدَمَ , إِنَّكَ لَوْ أَتَيْتَنِي بِقُرَابِ الأَرْضِ خَطَايَا ثُمَّ لَقِيتَنِي لاَ تُشْرِكُ بِي شَيْئًا لأََتَيْتُكَ بِقُرَابِهَا مَغْفِرَةً}. 

رواهُ التِّرْمِذيُّ , وقالَ: حديثٌ حَسَنٌ صحيح.

    An karɓo daga Anas bin Malik (RA) ya ce: 

     "Na ji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya na cewa:

    "Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

       "Ya kai Ɗan-Adam! Haƙiƙa matuƙar ka roƙe Ni kuma ka sa rai da samun buƙatarka a wajeNa to Zan gafarta ma ka abinda ke kanka kuma ba Zan damu ba. Ya kai Ɗan'Adam, ko da zunubanka sun kai cikin sama sannan ka nemi gafaraTa to Zan gafarta ma ka. Ya kai Ɗan'Adam, da za ka zo Min da zunubi cikin duniya sannan ka gamu da ni ba ka taɓa yin shirka ba to ni kuma tabbas sai Na zo ma ka da gafara cikin ta (duniya).

     Tirmiziy ne ruwaito shi kuma ya ce hadisi ne Hasanun Sahihun.

★Wannan hadisi yana nuna mana girman rahamar Allah da falalarSa. 

★Allah Yana gafarta dukkan zunubi muddin bawa ya koma gare Shi da gaskiya.

★Idan mutum ya nemi gafara da kyakkyawar zuciya, ba zai taɓa shan wahalar samun gafarar Allah ba.

★Babban sharaɗi shi ne: kada a yi wa Allah shirka. Idan mutum ya tsarkake tauhidi, komai yawan zunubansa, zai samu gafara idan ya nema.

  ★Kada mutum ya karaya daga rahamar Allah, ya ci gaba da roƙon gafara tare da tsarkake imani.

    Allah Ya ba mu ikon tuba kuma ya gafarta mana zunbanmu.

   Daga shafin Bashir Halilu.

Comments

Popular Posts