WAFATIN ANNABI ADAMU (A.S) DA WASIYYARSA GA ƊAN SA SHIYSU (AS).



Daga shafin Bashir Halilu 

   Ya zo acikin littafin 'Albidayah Wan Nihayah' na Ibnu Kasir cewa: an ruwaito cewa Annabi Ādam عليه السلام ya rayu har tsawon shekara dubu (1000).

   Lokacin da ajalinsa ya kusa, sai Mala’ikan Mutuwa ya zo wurinsa. Sai Annabi Adam (AS)  ya ce da shi:
    “Ba sauran shekara arba’in a cikin rayuwata ba?”

Wannan kuwa saboda wata rana Allah Maɗaukakin Sarki Ya nunawa Annabi Adam (A.S.)  tsawon rayuwar zuriyarsa, sai ya ga Annabi Dāwuda عليه السلام yana da gajeriyar rayuwa, shekara 40, sai Annabi Ādam (A.S) ya ce ya ba shi kyautar shekara arba'in daga rayuwarsa.

Amma lokacin da Mala’ikan mutuwa ya dawo domin karɓar ransa, sai Annabi Ādam (AS) ya manta ya ce:

 “Ai ni ban ba shi wani abu daga rayuwata ba!”

Sai Ibn Kathīr ya ce: "Annabi Ādam ya manta, zuriyarsa ma sai suke mantuwaa. Ādam ya musanta, zuriyarsa ma sai suke musu. Ya yi kuskure, zuriyarsa suke yin kuskure".

Lokacin da Annabi Ādam (A.S) ya rasu — kuma hakan ya faru ne a ranar Jumu'a — sai Mala'iku su ka zo masa da turaren jana’iza da kayan suturar jana’iza daga Aljanna, kuma su ka ba da ta’aziya ga ɗansa kuma magajinsa Shīsu (A.S).

   Abdullah ɗan Imam Aḥmad ya ce: Hudbah bin Khālid ya ba da labari, ya ce Hammad bin Salamah ya ruwaito daga Ḥumayd daga Hasan daga Yaḥyā — wanda shine Yaḥyā ɗan Ḍamrah al-Sa‘dī — ya ce:
Na ga wani tsoho a Madīna yana magana, sai na tambaya: "Waye wannan?"

 Aka ce: "Wannan Ubayy bin Ka‘ab ne." Sai ya ce: "Lokacin da mutuwa ta zo wa Annabi Ādam (A.S), sai ya ce wa ‘ya’yansa: 

    "ƴaƴana! ina jin kwaɗayin 'ya'yan itatuwan Aljanna.’”

     Sai su ka tafi neman 'ya'yan itatuwa, to amma sai Mala’iku su ka riske su a hanya suna ɗauke da kayan jana’iza da turaren jana’iza, suna ɗauke da fasassu da fatakai da kwanduna, sai suka ce musu "Ya ƴaƴan Ādam, me ku ke so?, me ku ke nema?"

      Sai su ka ce "Ubanmu yana cikin rashin lafiya, kuma yana ƙaunar ɗanɗanar ƴaƴan itatuwan Aljanna."

   Sai su ka ce musu: "Ku koma, domin an gama da shi, Allah Ya ƙaddara mutuwarsa."

      Sai su ka iso tare, da Hawwa'u ta gan su, sai ta gane su, ta nufi wurin Annabi Ādam (A. S). Sai ya ce mata

   "Kinga ki bar ni, domin fitina ta zo ta hanyarki. Ki barni da mala'ikun Ubangijina (Maɗaukaki)."

  Sai mala'ikun su ka kama shi, suka wanke shi, suka sa masa kayan jana’iza, suka shafa masa turare, sannan suka haƙa masa kabari nau'in lahadu, suka yi masa salla, suka saka shi a cikin kabari, su ka lulluɓe shi.

   Daga nan suka ce "Ya Ƴaƴan Ādam, wannan ce hanyar da za ku bi (sunnar ku kenan).

      Wasu ruwayoyi sun cewa an binne Annabi Adamu (A.S) a dutsen Abī Qubays a Makkah, wasu kuma sun ce a Baytul Maƙdis (wato Ƙudus), wasu kuma sun kawo wurare daban-daban.
     
WASIYYAR ANNABI ADAM (.AS.)

    An karɓo daga Abu Dharr ya ce  "Manzon Allah (S.A.W) ya ce  “Lallai Allah Ya saukar da littattafai guda ɗari da huɗu. Ya saukar wa Shīsu daga cikinsu guda hamsin.”

   (Ahmad ne ya ruwaito shi kuma Albaniy ya inganta shi acikin Silsilah)

    Muhammad bin Isḥāq ya ce "Lokacin da mutuwa ta kusanto Annabi Ādam (A.S), sai ya naɗa ɗansa Shīsu a matsayin Khalifa, ya sanar da shi lokutan dare da rana, da ibadun da ake yi a kowane lokaci daga cikin waɗannan, sannan ya sanar da shi game da zuwan Ruwan Ɗufana bayan wani lokaci.

Malaman tarihi sun ce: dukkan zuriyar Annabi Ādam da ke raye a yau sun fito ne daga Shīsu, zuriyar sauran ‘ya’yansa sun ƙare, sun shuɗe. 

Allah Ne Mafi Sani.

Daga shafin Bashir Halilu

Comments

Popular Posts