YAƘIN UHUDU
Yaƙi na biyu da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya je da kansa Daga Shafin Bashir Halilu. A cikin babban littafin tarihin nan mai suna 'Albidayah Wannihayah' wanda Shaihun Malami Ibnu Kasir ya wallafa, ya kawo cewa: Bayan an gama yaƙin Badar, wanda jama'ar musulmi su ka yi ƙoƙarin tare tawagar dukiyar Ƙuraishawan Makkah; dukiyar da aka tabbatar cewa dukiyar musulmai ce da su ka bari a Makkah Ƙuraishawa su ka deɓe musu, suke kasuwanci da ita. A ƙarshe ƙwace dukiyar bai samu ba domin Abu Suf'yan da ke jagorantar tawagar dukiyar ya gane ana bibiyarsa, don haka ya canja hanya, ya gudu. Duk da ba a samu ƙwace dukiyar ba, Ƙuraishawa sun fito, inda aka haɗu a Badar aka gwabza yaƙi kuma Musulami su ka samu gagarumar nasara. Wannan ya sa Ƙuraishawa su ka sake shiri bayan shekara ɗaya da wannan yaƙi, su ka sake dawowa domin ɗaukar fansar abinda Musulmai su ka yi musu a yaƙin Badar. Daga cikinsu akwai Abū Sufyān, wanda ya ...