YADDA ZA KA GANE ALJANI YA FITA DAGA JIKIN MUTUM BAYAN RUƘIYYAH. Daga Dr. shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.


  Wani sa'in akan yi alƙawari da Aljani cewa zai tafi daga jikin mara lafiya kuma a ba shi umarni ya fita nan take, amma in bai yi niyyar fita ba sai ya laɓe a jikin mara lafiya, a zuwan ya tafi. Wani kuma ana cikin gudanar da Ruƙiyyar sai Aljanin yay lamfo, sai a ɗauka ya gudu ne, alhali yana na. 

     Ga wasu daga cikin alamomin da za ka iya ganewa idan Aljani ya fita ko kuma laɓewa ya yi.
     1- Raguwar ƙarfi ko kasala nan take. Wato idan Aljanin mai azababben ƙarfi ne ko yana buge-buge, idan ya fita za ka ga jikin mutum ya yi lakwaf, kamar an zare jijiyoyin jikinsa.

   2- Bacci na ɗan lokaci. Musamman idan Aljanin ya kasance a ƙwaƙwalwar mutum ya ke zama, da zarar ya fita sai mutum ya kwanta, ya yi bacci na ƴan mintuna nan take sannan ya farka, ya cigaba da harkokinsa.

   3- Dawowa cikin hayyaci. Za ka ga mutum ya dawo cikin hayyacinsa nan take har ma yana tambayar wa ya kawo shi nan wajen ko kuma me ya faru da shi.

   4- Hamma ko Atishawa. Wani Aljanin ya kan yi hamma ko atishawa idan zai fita, musamman idan an ba shi umarnin fita ne ta baki.

        ABIN LURA

      Duk da waɗannan alamomi, wani Aljanin yana iya kwaikwayon dukkanin waɗannan abubuwan domin a yi zaton ya fita amma yana nan. 

Ga hanyoyin da za ka bi domin gano ƙaryar Aljani wajen fita. 

1- Ka ce mai lalurar ya kalli cikin idonka, kai ma ka kalli ƙwayar idonsa, ka ƙura masa ido. Idan ka ga ya kasa kallonka, ko yana ƙiƙƙifta ido, ko ya zura maka ido yanai ma ka kallo mara kan gado, to da alama Aljanin bai fita ba.
    
        2- Ka ce ya ɗaga hannunsa, idan ka ga jikinsa yana rawa to Aljanin yana nan.

        3- Ka umarce shi ya karanta ma ka wata aya ko sura daga Alƙur'ani, mara wahalar karantawa. Misali Fatiha ko Ayatal Kursiyyu ko Falaƙi da Nasi. Idan ya ƙi karantawa ko kuma yana karatun ba daidai ba to da alama Aljanin yana nan bai tafi ba.

        4- Ka ɗauko ruwan ruƙiyyar da ka haɗa ko man ruƙiyyah, ka baiwa mara lafiyar, ka ce ya karɓa da hannunsa, ya sha kuma ya shafa a jikinsa. Kada kowa ya yi masa. Idan ya ƙi karɓa ko ya watsar da ruwan to Aljanin yana nan.

      5- Ka baiwa mara lafiyar ruwa, ka ce ya yi alwala. Kada kowa ya taya shi. Idan ya tashi da kan sa ya yi ɗauki ruwan ya yi alwalar har ya gama ba su sake buge shi ba to da alama Aljanin ya tafi.

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts