YA KAMATA KU KULA DA WAƊANNAN KA'IDODI IDAN ZA A YIWA ƊAN UWANKU RUKIYYAH. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
SHARUƊƊAN DA ƳAN UWAN MARA LAFIYA YA KAMATA SU KIYAYE
Wani sa'in idan mutane za su kai ɗan uwansu wajen mai ruƙiyya sai su yo zuga. Mata da masu goyo da ƙananan yara. Musamman kuma idan a gidansu ne ake yin ruƙiyyar sai su taru suna kallo wasu ma suna saka muku baki ko kuma suna ƙoƙarin koya ma ka yadda za ka yi aikinka.
Daidai ne, ba laifi ba ne ƴan uwan wanda za a yi wa Ruƙiyyah su tsaya amma ba kamar masu kallon wasan kokawa ba, akwai abubuwan da ya kamata su kiyaye.
1- A janye ƙananan yara, don kada Aljani ya shafi yaro ko kuma yaron ya zo yana firgita daga baya. Kuma a tarbiyyah mai kyau ma ba komai ake gabatarwa a gaban yara ba.
2- Wacce ta san ba ta da tsarki ko mai janaba bai kamata su tsaya kallon ruƙiyyah ba saidai in ya zama dole. Akwai bukatar shi wanda zai rukiyyar da masu taimaka masa su yi alwala, in da hali, don su zama cikin cikakken tsarki. Dalili shi ne Aljani na saurin shiga jikin mutum mara tsarki kuma yana wahalar iya shiga jikin mutum mai tsarki musamman kariya irin ta alwala.
3- Suturce jiki. Ba daidai ba ne mata su zauna ba hijabi ko cikakkiyar sutura a wajen da ake yin Ruƙiyyah. A ɗaura ɗankwali, a guji fito da mama ana baiwa yara da ko zaman da bai dace ba.
4- A guji yin surutu ko shiga aikin mai Ruƙ'yah. Wasu za su zauna ana ruƙiyya amma suna ba da labarai na wasu masu lalurar daban. Wasu ma suna gayawa mai Ruƙ'yah cewa ga yadda ake yi. Wannan yana taimakawa Aljanin wajen kawo ruɗu ko rikita lissafin mai Ruƙiyyar.
5- Yin zagi ko tsinewa Aljani da la'antarsa. Wanda ya ke wurin da ake yin Ruƙiyyah kamata yay ya dinga karanta Alƙurani da add'o'in tsari don kare kansa. Amma in ya shagala da zage-zage to Aljanin zai iya komawa jikinsa.
6- A matsayinka na ɗan kallo ko wakili, ka guji jefawa Aljani tambaya ba tare da izinin mai ruƙiyyah ba kuma ka guji ƙarasawa Aljani maganarsa. Misali masu cewa Aljani "Waye ya turo ka?"
Ko kuma "Ku faɗi abunda kuke so a ba ku ku tafi".
Da masu cewa "Mu dai muna neman sulhu"
da makamantan haka.
Duk waɗannan tambayoyin ba dede ba ne kuma suna sa wa Aljani ya fahimci cewa ba ku san abinda kuke ba.
7- Abinda ya sa ake so ya zama masu hankali ne za su tsaya saboda ba dukkan abinda Aljani zai faɗa ne gaskiya ba. Yana iya yin ƙarya ko haɗa fitina ko barazana. Wannan zai ta da hankalin mai raunin tunani. Don haka dole a matsayinka na wakili ka ɗauka cewa dukkan abinda Aljanin ke faɗa ƙarya ne, saidai in shi mai ruƙiyyah ne ya tabbatar ma ka cewa haka ne.
8- Kada ka ɗauka cewa dole sai Aljani ya yi magana ko kuma mutum ya fita daga hayyacinsa sannan ya tabbata cewa ruƙiyyar ta yi. Ita ruƙiyyah addu'a ce, don haka kar ka zaci mai ruƙiyyar ne bai iya ba shi ya sa ba ka ga wani abu ya faru ba.
9- Ka yarda cewa waraka da lafiya a hannun Allah suke. Mai ruƙiyyah yana addu'a ne kawai, kai kuma ka yi fatan Allah Ya amsa. Amma kada ka ɗauka cewa dole ne a samu lafiya don an yi ruƙiyyah.
10- Ba a ruƙiyyah ɗaya kawai ake tabbatar da cewa mutum ba shi da Aljani a jikinsa ba. Ana maimaita ruƙiyyah kamar sau uku ko bakwai ko sama da haka, a kullum-kullum ko sati-sati ko makamancin haka, har a tabbatar. Don haka kuskure ne mutum ya ce ai ni an taɓa yi min ruƙiyyah amma ba abinda ya faru da ni.
A daure a cigaba da zuwa ruƙiyyah zuwa wani lokaci.
Allah Ya sa mu dace, Amiyn.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment