SIHIRIN SAKAWA MUTUM RASHIN LAFIYA SIHRUL MARADH (سِحْرُ الْمَرَضِ) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Dr. Khalid bin Abdur-Rahman Al-Juraishi ya kawo bayani akan wannan nau'in sihiri a cikin littafinsa
الحذر من السحر
inda ya yi amfani da sunan
سحر المرض أو الإمراض
wato sihirin cuta ko sihirin jawo cuta.
Haka nan a cikin littafin
«الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار»
na Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, an kawo bayani a kan wannan nau'in sihiri da ake kira Sihrul Maradh (سِحْرُ الْمَرَضِ), wato sihirin cuta.
Wannan suna 'Suhrul Maradh', yana nufin wani nau'in sihiri da ake yin sa domin a cutar da mutum ta fuskar lafiyar jikinsa, kamar haifar masa da ciwo ko wata matsala a wani sashe na jikinsa.
Abu ne sanane cewa Shaiɗan ko Aljani na iya sakawa mutum cuta a jikinsa, saidai hakan zai iya faruwa ta hanyar sihiri ko ba ta hanyar sihiri ba, sannan cutar tana iya tasiri idan Allah Ya so.
A cikin Alkur'ani mai girma, suratu Sād, ayah ta 41, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa
وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَى رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الشَّيْطَانُ بِنُصْبِ وَعَذَابٍ.
Ma'ana:
41. Ka kuma tuna BawanMu Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa (yana cewa): "Lalle ni Shaiɗan ya shafe ni da wata wahala da azaba."
(Tafsiri)
A wadannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) tana tunatar da Annabi () labarin bawansa Annabi Ayyub (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) lokacin da ya kamu da wata matsananciyar rashin lafiya, amma ya yi hakuri ya jure bai koka wa wani abin da yake ciki ba sai Allah, yayin da ya yi addu'a ya roke shi cewa, Shaidan ya shafe shi da wata cuta mai wahalarwa da azabtarwa. Ya kuma rasa iyalansa da dukiyarsa bayan ya kasance mutum mai yawan dukiya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya amsa masa rokonsa ya umarce shi da ya hauri kasa da kafarsa. Da ya aikata hakan sai ruwa ya bubbugo daga cikinta wanda ya rika sha yana wanka da shi har cutar da ke tare da shi ta gushe.
(Fassarar Hausa da tafsiri: Prof. Sani Umar Rijiyar Lemo. Ban ƙara komai ko canja wani abu acikin bayaninsa ba).
Wannan na tabbatar da cewa Shaiɗan ko Aljani na iya sakawa mutum cuta a jikinsa, saidai hakan zai iya faruwa ta hanyar sihiri ko ba ta hanyar sihiri ba, sannan cutar tana iya tasiri idan Allah Ya so.
Hadisin da aka ruwaito daga Nana A'isha (R.A.) game da yadda aka yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sihiri, Alƙāḍī ‘Iyāḍ (القاضي عياض)
a cikin littafinsa إكمال المعلم بفوائد مسلم,
da kuma bayanin da Imam Nawawi ya kawo daga gare shi a
شرح صحيح مسلم,
Alƙāḍī ‘Iyāḍ ya ce:
وَقَدْ جَاءَتْ رِوَايَاتُ هَذَا الْحَدِيثِ مُبَيِّنَةً أَنَّ السِّحْرَ إِنَّمَا تَسَلَّطَ عَلَى جَسَدِهِ وَظَوَاهِرِ جَوَارِحِهِ، لَا عَلَى عَقْلِهِ وَقَلْبِهِ وَاعْتِقَادِهِ.
Ma’ana:
“Ruwayoyin wannan hadisi sun bayyana cewa sihirin ya shafi jikinsa da gaɓoɓinsa na zahiri, ba hankalinsa, zuciyarsa da imaninsa ba.”
A nan, Alƙāḍī ‘Iyāḍ yana tabbatar da cewa tasirin sihirin ya shafi jikin Annabi ﷺ, ba kawai tunaninsa ba.
A cikin شرح صحيح مسلم, Imamun Nawawi ya kawo bayanin Alƙāḍī ‘Iyāḍ cewa sihirin ya shafi jikin Annabi ﷺ da gaɓoɓinsa na zahiri, ba hankalinsa da imaninsa ba. Ya kuma kawo bayanin malamai game da tasirin sihiri da iyakokinsa.
YADDA AKE GANE ALAMOMIN SIHIRIN CUTA A JIKIN MUTUM
1. الْأَلَمُ الْمُسْتَمِرُّ فِي عُضْوٍ مِنَ الْجَسَدِ
Ciwo mai ɗorewa a wani sashe na jiki.
Wato mutum ya dinga fama da wani dauwamammen ciwo a jikinsa, wanda ba ya sauka ko da yausje yana tare da shi.
2. نَوَبَاتُ الصَّرْعِ وَالتَّشَنُّجَاتُ
Farfaɗiya da jijjigar jiki.
Wato mutum ya dinga samun matsalar jijjigar jiki, karkarwa ko wani yanayi mai kama da farfaɗiya.
3. شَلَلُ عُضْوٍ مِنْ أَعْضَاءِ الْجَسَدِ
Shanyewar ɓarin jiki.
Wato wani sashe na jikin mutum ya kasa motsi ko ya samu rashin kuzari mai tsanani ko kuma ya bushe, ya dena aiki.
4. الشَّلَلُ الْكُلِّيُّ لِلْجَسَدِ
Shanyewar dukkan jiki.
Wannan yana nufin samun matsala mai tsanani da ta hana mutum motsa yawancin sassan jikinsa, saidai ko harshe ko ido, kamar dai yadda ya zo a ciki ƙissar Annabi Ayyuba (A.S).
5. تَعَطُّلُ إِحْدَى الْحَوَاسِّ عَنْ عَمَلِهَا
Daina aiki ko lalacewar wata gaɓar jiki.
Wato mutum ya samu matsala wajen gani, ji ko wani aikin wata gaɓar jiki musamman wanda ke faruwa kwatsam, ba tare da wani dalili da aka iya ganowa ba.
6. الصُّدَاعُ الشَّدِيدُ الْمُسْتَمِرُّ
Ciwon kai mai tsanani da ɗorewa.
Wato mutum ya dinga fama da matsanancin ciwon kai, akai-akai ko na dogon lokaci wanda aka kasa gano sababbinsa ko yadda za a mgance shi.
7. شُخُوصُ الْبَصَرِ وَزَوَغُهُ
Kallon ido ba tare da natsuwa ba ko karkacewar kallo.
Wato ido ya kasance yana kallon wani wuri cikin yanayin da ba a saba gani ba, ko kuma kallo ya rika kaucewa ba tare da natsuwa ba.
8. النِّسْيَانُ الشَّدِيدُ
Tsananin mantuwa.
Wato mutum ya kasance yana yawan mantawa da abubuwan da yake yi ko waɗanda aka gaya masa.
Saidai ba dukkan wanda yake fama da ciwon jiki, farfaɗiya, shanyewar jiki ko matsalar gabobin ji ne zai iya zama an yi wa sihiri ba, waɗansu matsalolin na iya kasancewa sakamakon cututtukan jiki da dama.
Saboda haka, idan mutum yana fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli, ya kamata ya nemi kulawar likita domin gano ainihin musabbabin cutar sannan a haɗa da neman magani da addu'a da ruƙiyya ta Alƙur'ani da Sunnah, tare da dogaro ga Allah Maɗaukakin Sarki.
WASU DAGA CIKIN ADDU'O'I DOMIN NEMAN TSARI DAGA CUTUTTUKA DA DAMUWA.
Na ɗaya (1): Addu'ar neman tsari daga gazawa da kasala.
An karɓo daga Anas bin Malik رضي الله عنه cewa Annabi ﷺ ya kasance yana cewa:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ، وَالْعَجْزِ وَالْكَسَلِ، وَالْجُبْنِ وَالْبُخْلِ، وَضَلَعِ الدَّيْنِ، وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ».
Ma'ana:
Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga damuwa da baƙin ciki, da gazawa da kasala, da tsoro da rowa, da nauyin bashi da rinjayen mutane a kaina.
Bukhari ne ya rawaito shi.
Na biyu (2): Yin ruƙiyya ta Alƙur'ani da Sunnah.
Musulmi zai iya yi wa kans a ruƙiyya ta hanyar karanta:
1. Suratul Fātiha.
2. Ayatul Kursiyyu — Suratul Baƙara, aya ta 255.
3. Ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baƙara — aya ta 285 zuwa 286.
4. Suratul Ikhlās, Suratul Falaƙ da Suratun Nās.
5. Addu'o'in neman lafiya da kariya da aka tabbatar daga Annabi ﷺ.
Ana yin ruƙiyya tare da kyakkyawar niyya, neman taimakon Allah da tabbatar da cewa waraka tana hannunSa.
Na uku (3): Yawaita addu'a da neman lafiya.
Musulmi ya riƙa roƙon Allah Ya ba shi lafiya, Ya yaye masa damuwa, Ya sauƙaƙa masa wahala, tare da kiyaye salloli da azkāran safe da yamma.
Na huɗu (4): Neman magani da ruƙiyya.
Idan mutum yana fama da cuta, ya nemi kulawar likita domin gano musabbabinta da samun maganin da ya dace amma ba a dace ba, ya kamata a haɗa wannan da ruƙiyya ta shari'a da magungunan Musulunci da na gargajiya.
Daga shafin Dr. Bashir Halilu, mai Ruƙiyya da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment