SHARAƊAN ZAMA CIKAKKEN MAI RUƘIYYAH
Daga shafin Dr. Bashir mai magani
Lambar waya 08134434846.
Idan kana so ka zama cikakke mai ruƙiyyah wanda ya amsa sunansa, to ga sharaɗai masu sauƙi da Malamai su ka yi bayani domin ka kiyaye.
1. Dole Mai Ruƙiyyah ya kasance Musulmi ne, mai tauhidi, mai tsoron Allah daidai gwargwado.
Ba a yarda kafiri ko mai shirka ya yi ruƙiyya ba, sai mutum mai tsarkin zuciya da tsoron Allah, wanda ke bin koyarwar Qur’ani da Sunnah.
2. Ya kasance yana karanta ruƙiyya ne da Qur’ani ko da sunayen Allah ko da addu’o’in da su ka fito daga Annabi ﷺ. Ruƙiyya ta halal dole ne ta kasance daga:
Qur’ani mai girma, sunayen Allah (Asma’ul Husna) da Addu’o’i na Annabi ﷺ.
Ba a yarda da rubuce-rubuce ko kalmomi marasa ma’ana ko "salati" na bidi’ah ba.
3. Dole ne ya yi ruƙiyya da harshen da ake fahimta – kamar Hausa ko Larabci. Idan ya yi da kalmomin da ba a san ma’anarsu ba, to ruƙiyyar ba ta inganta da suna Ruƙiyyah ta musulunci ba.
4. Ya yarda cewa ba ruƙiyya ke warkarwa ba, sai Allah Ne kadai Ke bayar da lafiya. Ruƙiyya sababi ce kawai, warkarwa daga Allah ta ke.
5. Ya zama mutum ne da yake da ingantacciyar akida, ba mai bidi’ah ba.
Wanda zai yi ruƙiyya dole ya kasance: Ahlus-Sunnah, mai tsoron aikata bid’a, Ba ya haɗa Allah da wani wajen aikinsa.
6. Ya kamata mai ruƙiyyah ya san yadda ake ruƙiyya da hukuncinta da ayoyin da suka dace. Ya san yadda ake yin ruƙiyyar:
Idan ciwon ido ne, ko sanyi, ko sihiri, ko aljanu, ko hassada misali, bai kamata ya yi ta karanta ayoyi kawai ba tare da fahimta da tsari ba.
7. Bai kamata ya taɓa mace ko ya keɓanta da ita ba. Wannan haramun ne, kuma yana iya janyo aikata laifi.
Idan mace ce, ya fi kyau ta je wajen mace mai ruƙiyya, ko ya zama akwai muharramanta a kusa.
8. Kada ya riƙa karɓar kuɗi da yawa ko ya wuce gona da iri.
Akwai halaccin karɓar ɗan abu bayan ruƙiyya, amma ba a yarda da tsada da ha’inci ba. Kada ya juya ruƙiyya kamar sana’ar haɗa kuɗi kawai. Ya kamata mai Ruƙiyyah ya yarda cewa taimako ya ke yi wa al'uma don Allah Ya ba shi lada.
9. In da hali ya zama yana da aure.
Don hakan zai ƙara masa mutunci kuma zai taimaka masa wajen kare mutncinsa da addininsa.
10. Ya zama ya iya karatun Alkur'ani da Tajwidi.
Yin karatun Alkur'ani da kuskure yayin Ruƙ'yah na sa wa Aljanin ya kangare kuma Ruƙiyyar ba ta tasiri.
11- Ya zama yana da ilimin sanin lalurori da bambance cututttuka. Domin zai gane lalurar da zai yi ruƙiyyah da kuma wacce zai ce a je asibiti.
Waɗannan su ne shawarwari da za mu bayar ga masu son su mayar da Ruƙiyyah aikinsu na sosai.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment