YADDA AKE ƊAURE ALJANI A YAYIN RUƘIYYAH


Daga shafin Bashir Halilu 
Lambar waya 08134434846.
    Akwai al'amari mai abun takaici, wato yadda Aljani kan sulale, ya bar jikin mutum, ya gudu lokacin da ake yin ruƙiyyah alhali mai ruƙiyyar bai sallame shi ba ko kuma ba a tabbatar ya bar jikin mara lafiyar ba.

   Wannan ya sa mutane da dama ke son sanin ko akwai wata hanya wacce ba ta saɓawa shari'a ba wacce za a iya amfani da ita wajen hana Aljani fita a karan kan sa, har sai an ba shi umarni ko an sallame shi.

    Ga wasu hanyoyi masu sauƙi da za ka yi amfani da su wajen hana Aljani tafiya, waɗanda babu wata shubuha akai ko kokwanton yin shirka ko saɓawa shari'a.
    Waɗannan hanyoyi mun fahimce su ne a sakamakon jarraba su lokacin Ruƙ'yah da kuma yadda mu ka ga suna tasiri sosai.

        1- Dafa kan mara lafiya. 
  Wato mai ruƙiyyar ya ɗora hannunsa a kan mara  lafiyar lokacin da ya ke magana da Aljani. A wannan lokacin ko da ya ce Aljanin ya fita to ba zai iya fita ba sai ya sauke hannunsa tukuna.

    2- Riƙe goshin mara lafiya. 
    Wato mai Ruƙ'yar ya riƙe masa goshi irin yadda ake yi wa mutum idan yana ciwon kai.

      3- Dafa ƙirjin mara lafiya, musamman idan yaro ne, shi ma yana hana Aljani guduwa, sai an ba shi umarni.

     4- Riƙe babban ɗan yatsan hannu. 
    Wato ka riƙe babban ɗan yatsan Hannun mara lafiyar a lokacin da kake karatu kana magana da Aljanin. Hakan yana hana Aljani guduwa kuma yana sa shi shan wahala sannan ya fi fadar gaskiya da rashin taurin kai.

     5- Riƙe babban ɗan yatsan ƙafa. 
     Shi ma yana azabtar da Aljani kuma yana sa shi fadar gaskiya da kasa tafiya har sai an sake shi.

     6- Riƙe hannuwan mara lafiya ta baya. 
   Wato a haɗa hannuwan mara lafiya, sai a riƙe su ta baya kamar yadda ake sakawa mutum ankwa, wannan na rage buge-bugen Aljani kuma yana hana shi guduwa.

     7- Wasu suna ɗaure babban ɗan yatsan  hannu ko na ƙafa da tsumma, don hana Aljanin guduwa amma gara ka riƙe da hannun don gudun kwaikwayon bokaye.

   Amma a sani, dukkan wadannan hanyoyi za su taimaka ne kawai idan ka cigaba da karanta Alƙur'ani, ba a dena karatu ko a bari hira tay nisa. 

   Sanna wani zai iya taimaka ma ka, ya riƙe ma ka mara lafiyar ko ya dafa kan sa, kai kuma kanai masa tambayoyi. 

     Ya zama dole dukkan wanda zai taimakawa mai ruƙiyyah wajen riƙe Aljani ya zama shi ma yana karanta Alƙur'ani.

   Ba ɗaure Aljani da azabtar da shi ce manufar Ruƙ'yah ba. Manufar ita ce neman waraka daga wajen Allah Maɗaukakin Sarki. 

   Don haka ba ɗaure Aljani ake nufata ba, abinda ake buƙata shi ne a ɗan tsayar da Aljani don a yi masa nasiha kuma a gargaɗe shi cewa ya tabbatar ya bar jikin mara lafiya da alƙawarin rashin dawowa jikinsa ko bar masa cuta.

      Idan Aljani ya ƙi tsayawa a yi magana da shi kada a damu, a cigaba da yin Ruƙ'yah lokaci zuwa lokaci, ba tare da tsanantawa ko wahalar da mai larurar ba.

    Waɗannan su ne wasu hanyoyi da mu ka sani, waɗanda ba su da wahala kuma ba su saɓawa shari'a ba. 

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts