ABUBUWAN DA YA KAMATA KA TAMBAYI ALJANI IDAN KA GAMU DA SHI A YAYIN RUƘIYYAH. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846


    Kamar yadda mu ka sha yin bayani a lokuta da dama, yin magana da Aljani ko bayyanar Aljani ba ita ce manufar yin ruƙiyyah ba kuma ba ta haka ake gane cewa an samu waraka ko ba a samu ba. Ba dole sai an yi magana da Aljani idan ya bayyana a jikin mara lafiya ba, za a iya cigaba da karatu har ya fita. Kawai ana magana da Aljani ne in ta zama dole ko kuma shi Aljanin yana neman taimakon yadda , zai fita.

      YIN MAGANA DA ALJANI A YAYIN RUƘIYYAH TANA DA AMFANI DA KUMA RASHIN AMFANI

      Amfaninta

       1) Wani Aljanin yana so a saurare shi don a ba shi damar ya fita, rashin hakan na iya sa wa Aljanin ya mutu ko kuma ya fita ta inda mara lafiyar zai iya cutuwa. 

       2) Wani sa'in magana da Aljanin na taimakawa mai ruƙiyyah wajen sanin adadin A'janun a jikin mara lafiya da wasu abubuwa da za su taimaka don ya ƙara fahimtar matakan da ya kamata ya ɗauka. 

     3) Wani sa'in magana da Aljanin na taimakawa wajen ilmantar da mara lafiyar ko iyalansa wajen sanin abubuwa da ke jawo Aljanu don su kiyaye. 

     4) Mai Ruƙ'yah na ƙara fahimtar yanayin Aljanun, ko na asiri ne, ko masu taurin kai ne da kuma sanin ko sun yi wa mutum ajjiya a jikinsa. 
        Da dai sauransu

 RASHIN AMFANIN HIRA DA ALJANI. 

     Ba magana da Aljani ce matsala a yayin ruƙiyyah ba, hira da shi, tambayarsa abubuwan da bai kamata ba da kuma ba shi dama yai ta bayanai su ne matsalar. 

       1- Yawancin abinda Aljanin zai gaya ma ka ƙarya ne. Sunansa, adadinsu, dalilin shigarsu, zai fita ko ba zai fita ba, duk yawanci ƙarya zai ma ka. 

       2- Aljani na iya kama sunan wasu mutane ya ce su su ka turo shi jikin mara lafiyar. 

     3- Aljani na ɗauke hankalin mai Ruƙ'yah da surutu, ya dena karatu, yana saurarensa. Daga nan sai ya koma jikin mai ruƙiyyar ko ya ɓata masa aikinsa. 

       4- A wajen hira da Aljani ne ya ke iya faɗin cewa indai ana so mara lafiyar ya samu waraka to dole sai an yi yanka ko shirka. Wani sa'in indai iyalin mara lafiyar sun ji haka to ko ka hana su sai sun yi. 

        5- Akwai shubuhohi da haɗarin faɗawa bokanci wajen hira da Aljani, don yana iya gaya muku wasu abubuwa masu kama da gaibu, wanda yawanci ƙarya ne.

 ABUBUWAN DA YA KAMATA KA TAMBAYI ALJANI
     In ta kama dole za ka yi magana da Aljani a jikin mara lafiya, to ka tambaye shi

    1- Sunansa. Saboda in ya sake dawowa za ka gane kun taɓa magana da shi. 

    2- Musulmi ne ko arne. Don ka san ta yadda ya kamata ka bi da shi. 

    3- Adadinsu a jikin mara lafiyar. 

    4- Tsawon lokacinsu ko shekarunsu a jikin mara lafiyar. 

       5- Su gaya ma ka ta inda suke shiga jikin mara lafiyar, misali baki ko kunne da kuma inda suke zama a jikinsa, misali ciki ko ƙirji ko kai, don in ka tashi haɗa magani ka haɗa mai alaƙa da wajen.

     6- Ka tambayesu guraren da su ka ajjiyewa mara lafiyar cuta a jikinsa. 

    7- Ka tambaye shi yanzu bayan shi Aljanu nawa ne su ka rage ba su fita ba. 

   Daga nan ka yi masa nasiha, ka sallame shi.

   ABUBUWAN DA BAI KAMATA KA TAMBAYI ALJANI BA

      1- Kada ka tambaye shi "Wa ye ya turo ku?!". Yin hakan zai sa su ambaci wanda faɗar sunansa zai iya zama fitina.

     2- Kada ka tambayi Aljani me ya ke so a yi masa don ya fita. Yin hakan zai sa ya fahimci kana tsoronsa ne kuma kana jiran umarninsa. 

       3- Kada ka tambaye shi wasu abubuwan da su ka faru a ɓoye. Misali wasu kaya da su ka ɓata, ko kuma halin da wani mutum ya ke ciki a wani waje.

        A taƙaice dai, zai fi kyau a yi ruƙiyyah ba tare da an yi magana da Aljani ta sigar tambaya da amsa ba. 

   Ya fi kyau mu tsaya akan irin ruƙiyyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, wato a baiwa Aljani umarni ya fita ba tare da an yi hira da shi ba.

عن يعلى بن مُرّة رضي الله عنه قال:
أنَّ امرأةً جاءت إلى النبي ﷺ معها صبيٌّ لها به لَمَمٌ، فقال النبي ﷺ: «اخْرُجْ عَدُوَّ اللهِ، أَنَا رَسُولُ اللهِ». قال: فَبَرَأَ، فأهدت إليه كبشين، وشيئًا من أَقِطٍ، وشيئًا من سَمْنٍ، قال: فقال رسول الله ﷺ: «خُذِ الأَقِطَ والسَّمْنَ وأَحَدَ الكَبْشَيْنِ، وَرُدَّ عَلَيْهَا الآخَرَ».
رواه الإمام أحمد في المسند (17563)

Ma'ana:

   An ruwaito daga Ya‘ala bin Murrah (R.A) ya ce:

    Wata mata ta zo wajen Annabi ﷺ, tare da wani ɗanta wanda yake fama da rikitacciyar cuta ko wata damuwa da ta shafe shi. Sai Annabi ﷺ ya ce:

 “Fita ya maƙiyin Allah! Ni Manzon Allah ne.”

   Sai kuwa  yaron ya warke.

   Sai matar ta ba Annabi ﷺ raguna biyu, da ɗan aqit (busasshen madarar raƙumi ko tumaki), da kuma man shanu.

Sai Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ka ɗauki aqiṭ ɗin da man shanun, da ɗaya daga cikin ragunan biyu, ka mayar mata da ɗayan.”

   Imam Ahmad ya rawaito shi a cikin Musnad, lamba 17563.

     
Daga shafin Dr. Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. 
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts