WAJE KO MUHALLIN DA YA KAMATA A YI RUƘIYYAH A CIKINSA DA KUMA WAJEN DA BAI KAMATA BA. Daga Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.


     Ina nufin muhalli, inda za a iya zama a yi wa mara lafiya Ruƙiyyah a ciki.
 ZA MU KASA MUHALLIN ZUWA KASHI BIYU

KASHI NA FARKO: wajen da za a yi Rukiyyah idan lalurar gaggawa ta samu. Misali a ce Aljani ya buge mutum a kan hanya ko a makaranta ko kasuwa ko wajen aiki ko kuma acikin gidansa da makamantan haka.

     NA BIYU: ɗaki ko kuma wajen da aka tanade shi musamman don a dinga yin Ruƙiyyah a ciki ga waɗanda suka mayar da abun sana'a ko kuma aiki na yau da kullum.

      Rashin zaɓar guri mafi dacewa domin a gudanar da Ruƙiyyah na sa wa Aljanin ya samu damar yawo da hankalin mutane, kin kamuwa, komawa jikin wani ko guduwa ko kuma kin magana ko ma kin bayyana gaba ɗaya.


1- ZAƁAR WAJEN DA ZA A YI WA MUTUM RUƘIYYAH IDAN LALURAR GAGGAWA TA SAMU

    1- A guji guri mara tsafta: kamar bakin kwata, wajen da ake fitsari, kofar bandaki, wajen bola, waje mai duhu, bakin rami, wajen shara da duk wani wajen ƙazanta da aka san Shaiɗanu suna zama. Domin idan ana yin Ruƙiyyah a irin wannan waje to ƴan uwansa za su zo su ƙwace, ya gudu ko kuma su rikita wajen gaba ɗaya.

      2- A guji cinkoson mutane. Wani sa'in idan aka kiraka yin ruƙiyyah wani gida sai mutanen gidan su zo, su cika muku waje, musamman mata da ƙananan yara. Cinkoson jama'a na sa wa Aljanin yay ta faɗar maganganu waɗanda za su haɗa fitina, kamar ya ce wane ne ya turo shi. Haka nan suna iya komawa jikin ƴan kallo, musamman yara ko matan da ba su sitirce jikinsu sosai ba ko kuma wanda ya zo wajen ba shi da tsarki. Sannan idan akwai mai Aljanu ko mai sihri a jikinsa shi ma zai iya faɗuwa. Don haka ka umarci mutane su ragu, abar mutum biyu ko makamantan haka.

     3- Wajen hayaniya ko surutu. Kamar yadda mu ka karanta a baya, ita Rukiyyah karatun Alkur'ani ce da addu'o'i. Don haka ana bukatar yin shiru da samun nutsuwa yayin karatun Alkur'ani. Yin surutu yana hana karatun yay wa Aljanin tasiri, wani sa'in ma in kana karatun sai ya dinga binka ko ya dinga yi ma ka dariya. Aljani yana iya komawa jikin masu surutun, musamman waɗanda suke ƙundumawa Aljanin zagi da kuma masu cewa 'ƙona shi', 'kashe shi' da sauran masu yi wa Aljanu jafa'i lokacin ruƙiyyah.

      SAI KASHI NA BIYU

YADDA YA KAMATA ƊAKI KO OFFICE ƊIN RUƘIYYAH YA KASANCE


      1- Kayan ado a cikin ɗaki.
   Kada ka liƙa hotunan mutane ko dabbobi ko ajjiye buɗaɗɗen madubi a ciki ɗaki. A cire duk wani abu mai kawo shaiɗanu ko wanda shaiɗanu suke so. Barin irin waɗannan abubuwan na sa wa Aljanu su samu wurin zama a ɗakinka. Duk wanda ka cirewa Aljani sai Aljanin yay zamansa a ɗakin.

      2- Ɗakin da ake yin bori ko tsafi ko ajjiye kayayyakin su.
  Ba a yin Ruƙiyyah a ɗakin da ake aikin bori, sihiri ko tsafe-tsafe. Saboda shi kansa ɗakin matattarar shaiɗanu ce.

       3- Ana so dakin da ake yin Ruƙiyyah ya kasance matsakaici ba ƙaton ɗaki ba sannan ya zama akwai wadatar haske da iska. Haske idan mara lafiya lokacin ruƙiyyah yana raunata Aljanin. Ganin wawaken fili na ƙarawa Aljanin izza da fitina, ahi ya sa ake son karamin daki.

       5- kada a tara shirgi ko kayayyaki marasa ma'ana a cikin ɗakin. Saidai magunguna ko kayan aikin Ruƙiyyar kawai.

         6- Ana so ya zama ana karatun Alkur'ani a ɗakin don tsaftace shi daga Shaiɗanu.

Daga shafin Bashir mai ruƙiyyah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts