SIHIRIN JIN MAGANGANU KO MURYOYIN MUTANE KUMA BA A GANINSU SIHRUL HAWATIF (سِحْرُ الْهَوَاتِفِ) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
A cikin rubutun Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, mai taken
«سحر الهواتف (أعراضه - كيف يحدث؟ - علاجه)»,
ya yi bayani a kan wannan nau'in sihiri da ake kira 'Sihrul Hawatif'
A bayanin da wannan malami ya kawo, wannan nau'in sihiri yana saka mutum yawan mafarkai masu ban tsoro, jin muryoyin mutane suna maga kuma ba a ganinsu, yawan wasuwasin zuciya da shakku a kan abokai da masoya.
YADDA ALAMOMIN SIHRUL HAWATIF SU KE. GA MUTUM.
Ga wasu alamomi da abubuwan da aka ambata a cikin bayanin Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali, tare da ƙarin bayani domin sauƙin fahimta.
1- الْأَحْلَامُ الْمُفْزِعَةُ
Mafarkai masu ban tsoro.
Mutum ya dinga yawan yin mafarkai masu tayar da hankali, tsoratarwa ko firgici, har ya dinga tashi daga bacci cikin razana, wani ma yana zurawa da gudu ko ihu bayan ya farka.
2- سَمَاعُ مَنْ يُنَادِيهِ فِي الْمَنَامِ
Mutum ya dinga jin kamar wani yana kiransa a mafarki.
Mutum yana iya yin mafarki kamar wani yana kiransa da sunansa ko yana magana da shi, amma idan ya farka sai ya fahimci cewa mafarki ne.
3- سَمَاعُ أَصْوَاتٍ فِي الْيَقَظَةِ دُونَ رُؤْيَةِ أَحَد
Mutum ya dinga jin muryoyi kuma ba ya ganin masu su yayin farke.
Mutum yana iya jin kamar ana kiransa, ana magana da shi ko ana yi masa magana daga wani wuri, amma bai ga wanda yake magana ba. A fili ba a mafarki ba.
4- كَثْرَةُ الْوَسَاوِسِ
Yawan waswasin zuciya.
Mutum ya dinga yawan shiga tunani mai tayar da hankali, shakku ko fargaba, har hakan ya rinjayi natsuwarsa da ayyukansa na yau da kullum.
5- كَثْرَةُ الشُّكُوكِ فِي الْأَصْدِقَاءِ وَالْأَحْبَاب
Yawan shakku a kan abokai da masoya.
Mutum yana iya fara yawan zargin mutanen da yake ƙauna ko amincewa da su ba tare da hujja bayyananniya ba, har hakan ya kawo matsala a tsakaninsu ta zahiri.
6- رُؤْيَةُ السُّقُوطِ مِنْ مَكَانٍ عَالٍ فِي الْمَنَام
Mafarkin faɗowa daga wani wuri mai tsawo.
Mutum ya dinga yawan mafarkin yana faɗowa daga bene, dutse ko wani wuri mai tsawo, daga nan ya farka cikin firgici.
7- رُؤْيَةُ الْحَيَوَانَاتِ الَّتِي تُطَارِدُهُ فِي الْمَنَامِ
Mafarkin dabbobi suna binsa.
Mutum ya dinga yawan
mafarkin dabbobi masu ban tsoro suna binsa, suna neman su kama shi ko su farmake shi, har ya dinga jin tsoro idan lokacin bacci ya yi.
8- الْأَرَقُ وَاضْطِرَابُ النَّوْمِ
Rashin samun bacci mai daɗi
A wasu lokuta, yawan mafarkai masu ban tsoro da fargaba na iya sa mutum ya kasa samun isasshen bacci ko ya dinga farkawa akai-akai cikin dare.
9- الْقَلَقُ وَالْخَوْفُ الْمُتَكَرِّرُ
Yawan damuwa da jin tsoro.
Mutum ya zama cikin fargaba, musamman idan ya ji wani sauti da bai fahimci inda ya fito ba. Wannan na iya shafar natsuwarsa da gudanar da rayuwarsa.
10- الشُّعُورُ بِأَنَّ أَحَدًا يُخَاطِبُه
Jin kamar wani yana magana da shi.
Mutum yana iya jin kamar ana yi masa magana ko ana kiransa, ko da yake babu wani mutum a kusa da shi da yake magana a zahiri.
11- صُعُوبَةُ التَّرْكِيزِ بِسَبَبِ الْقَلَقِ
Wahalar mayar da hankali saboda damuwa.
Mutum na iya samun wahalar mai da hankali kan karatu, aiki ko sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsa.
12- تَكْرَارُ الْكَابُوسِ وَالْفَزَعِ مِنَ النَّوْمِ
Maimaituwar mafarkai masu firgitarwa da farkawa cikin razana.
Mutum ya dinga yawan farkawa daga bacci cikin tsoro.
13- الِانْشِغَالُ الْمُفْرِطُ بِالْأَصْوَاتِ وَالْوَسَاوِس
Yawan shagaltuwa da muryoyi da waswasin zuciya.
Mutum yana iya dinga tunanin muryoyin da ya ji ko abubuwan da suka firgita shi, har hakan ya rage masa natsuwa da shagaltuwa da al'amuran rayuwarsa.
Da dai sauransu.
Abin lura. Alamomi bakwai na farko su ma samo daga littafin Assarimul battar, sauran kuma na samo su ne daga wasu Malaman daban.
Samun ɗaya ko fiye daga cikin waɗannan alamomi ba ya tabbatar da cewa mutum yana da sihiri ko aljanu.
Jin muryoyin da babu mai magana a zahiri na iya kasancewa da alaƙa da rashin bacci, tsananin damuwa, wasu matsalolin kwakwalwa ko lafiyar jiki, ko kuma illolin wasu magunguna da sauran dalilai.
Saboda haka, idan mutum yana yawan jin muryoyin da wasu ba sa ji, yana samun mafarkai masu tsanani ko yana fuskantar tsoro da shakku da suka fara hana shi gudanar da rayuwarsa, ya kamata ya nemi likita domin a bincika dalilin matsalar.
Idan muryoyin suna umartar mutum ya cutar da kansa ko wani, ya kamata a nemi taimakon gaggawa. Sai kuma a haɗa da Ruƙiyyah da sauran magunguna da addu'o'i na Musulunci don magance matsalar.
MAGANCE MATSALAR TA HANYAR RUƘIYYAH
Mutum zai iya yin ruƙiyya ta Alƙur'ani da addu'o'in da aka tabbatar a Shari'a, tare da neman taimakon Allah da kyautata tawakkali gare Shi.
Daga cikin abin da za a iya karantawa akwai:
1. Suratul Fātiha.
2. Ayatatul Kursiyyu — Suratul Baƙara, aya ta 255.
3. Ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baƙara (Amanar Rasuwlu)— ayoyi na 285–286.
4. Suratul Ikhlās, Suratul Falaƙ da Suratun Nās.
5. Ayoyin da suka zo a kan warware sihiri:
- Suratul A'arāf, ayoyi na 117–122.
- Suratu Yūnus, ayoyi na 81–82.
- Suratu Ɗāhā, aya ta 69.
Ana iya karanta waɗannan ayoyi domin ruƙiyya, tare da yin addu'a da neman tsari daga Allah. Haka kuma mutum zai iya yi wa kansa ruƙiyya ko ya nemi taimakon amintaccen mai ruƙiyya wanda yake bin Alƙur'ani da Sunnah, ba tare da tsafe-tsafe, neman taimakon aljanu ko zargin mutane ba tare da hujja ba.
Ya kamata a haɗa ruƙiyya da binciken lafiya idan akwai alamomin da suke buƙatar hakan. Ba daidai ba ne a bar maganin asibiti saboda zaton cewa sihiri ne kaɗai yake haddasa matsalar.
Sihrul Hawatif suna ne da wasu masu ruƙiyyah suke amfani da shi wajen bayyana yanayin jin muryoyin da ba a ganin masu su, mafarkai masu ban tsoro da yawan wasuwasi.
Daga shafin Bashir Halilu, mai Ruƙiyya da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment