YADDA ZA KA BAMBANCE MAI LALURAR DA YA KAMATA KA YIWA RUƘIYYAH DA WANDA BA ZA KA YI WA RUƘIYYAH BA Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
A cikin ilimin ruƙiyyah shar’iyyah, malamai na sunnah sun fayyace cewa ba kowanne mai ciwo ake yi wa ruƙiyyah ba. Wasu cututtuka ne suke fitowa daga iska (aljanu), sihiri, ido ko hassada, waɗanda ake buƙatar ruƙiyyah, yayin da wasu cututtuka na zahiri ake nema musu magani a asibiti ko ta wata hanya ta halal.
Ga hanyoyi guda goma da malamai suka bayyana a littattafansu, kan yadda ake bambance mara lafiya da ya kamata a yi masa ruƙiyyah da wanda ba a yi masa:
1- Alamomin da ke nuna sihiri ko aljanu.
Yawan mafarkai masu ban tsoro (dabbobi, faɗowa daga tudu mai nisa, mafarkin tsoro, mafarkin mutane suna bin sa).
Gushewar hankali ko rashin kuzari ba tare da dalilin likita ba.
Wannan ya zo a littafin "Al-Farƙu bayna Auliya’ir Rahman wa Auliya’ish-Shayɗan" Na Ibnu Taymiyyah.
2- Wanda aka samu da Kambun ido (al-‘Ayn).
Mutum yana jin rashin lafiya kwatsam bayan kallon wani abu ko bayan an yaba masa akan wani abu.
Zai dinga fama da ciwon kai, kasala ko rashin nishaɗi.
An kawo wannan a littafin "Zaadul Ma’ad" na Ibnul Qayyimil Jauziyyah, (rahimahullah).
3- Wanda aka samu da cuta amma aka kasa a gano kan ta a asibiti.
Idan likitoci sun yi gwaji amma ba su gano asalin cutar ba, sannan kuma cutar ta ci gaba.
Wannan alamu ne na sihiri ko aljanu.
In ji Sheikh Ibn Baz (rahimahullah). Ya yi bayani a cikin fatawoyin sa "Fatāwā ibnu Baz"
4- Wanda yake jin ƙiyayya ko rikici tsakaninsa da matarsa ko mace take jin ƙiyayyar mijinta ba tare da dalili ba.
Wannan shi ake kira da “sihirin raba aure”.
Allah ya ambace shi a Suratul-Baqarah sura ta 2, ayah 102).
5- Wanda ya ke jin magana a cikin kunnensa ko ya ji kamar wani yana kiransa, amma in ya duba sai ya ga babu kowa.
Wannan yana daga cikin alamun aljanu.
Daga fatawar Ibnu Taymiyyah, ya yi bayani a cikin Majmu’ ul-Fatawa.
6- Wanda ke jin nauyi, kasala ko ciwon jiki a lokacin sallah ko karatun Alƙur’ani.
Wato idan mutum ya ɗauki Alƙur’ani yana karantu, sai ya ji gajiya, bacci ko ciwo. Haka idan yana sallah sai ya kama hamma da jin bacci da kasala.
Wannan alamun aljanu ko sihiri ne.
Shaykh Wahid Abdus-Salam Bali ya kawo shi a littafinsa "As-Sihr wal-‘Ayn wal-Mass".
7- Wanda yake jin ƙamshi ko ɗanɗano mara dalili a bakinsa.
Misali jin ƙamshin turare ko wari a baki yayin da babu shi a zahiri ko kuma babu wanda ya ke ji sai kai kaɗai.
Wannan na iya zama daga sharrin aljanu.
An kawo a littafin "Ɗibbun Nabawi" na Ibnul Qayyim.
8- Wanda yake da yawan bacci ko rashin bacci mara dalili.
Yana iya yin barci na dogon lokaci ko kuma rashin iya bacci gaba ɗaya.
Wannan na iya zama daga sihiri ko hassada.
Wannan an kawo shi a Fatawa Ibn Uthaymin.
9- Wanda yake samun ciwon da yake yawo a jikinsa.
Misali: ciwon da yake sauyawa daga hannu zuwa kafa ko kirji.
Wannan yana daga cikin alamun samuwar aljanu.
An kawo a littafin "Ruquyah Shar’iyyah" na Shaykh Muhammad Al-Wasaabi.
10- Wanda yake da tsananin tsoro ko damuwa ba tare da dalili ba.
Yana jin kamar wani na binsa in yana tafiya shi kaɗai ko yana tsoron duhu ko shiga cikin jama’a.
Wannan alamun sharrin shaidan ko hassada ce.
An bayyana a littafin "Al-Jawabul-Kafi" na Ibnul Qayyim.
A TAƘAICE.
Wanda ya dace a yi masa ruƙiyyah shi ne wanda yake da alamun sihiri, aljanu, kambun ido ko hassada. Wato waɗanda ke fama da cututtukan da ba su da bayani na likitanci ko kuma aka kasa shawo kansu a likitance.
Amma wanda cutarsa ta zahiri ce, kamar: hawan jini, ciwon sukari, ciwon hanta, zazzabi, malaria, typhoid, da dai sauransu, to a fi nema masa magani na asibiti ko na gargajiya ko na ganyayyaki da dai sauransu.
Amma idan mutum yana buƙatar a yi masa ruƙiyyah akan kowace irin lalura ce ana iya yi masa domin neman waraka a wajen Allah, domin ita ruƙiyyah addu'a ce da kuma neman waraka a wajen Allah Shi kaɗai.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na musulunci dana gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment