TA INDA YA KAMATA ALJANI YA FITA DAGA JIKIN MUTUM. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.


    Sau da dama a yayin Ruƙiyyah idan an baiwa Aljani umarnin fita daga jikin mara lafiya ya kan tambaya cewa ta ina zai fita. Wani kuma ya kan ce zai fita ta inda ya shigo.
      
         Wani Aljanin kuma sai ya ce zan fita amma ta ido, ko wani wajen makamancin haka. 

     Malaman ruƙiyyah sun lura cewa akwai gaɓoɓi da idan Aljani ya fita daga jikin ɗan Adam ta nan ana iya samun matsala, sannan idan ya ce zai fita ta inda ya shigo to nan ma za a iya samun matsala, saboda mai yiwuwa ta inda ya shigo ɗin sai da ya azabtar da mutum sannan idan ya fita ma mutum zai iya azabta.

     GURAREN DA BA A SO ALJANI YA FITA TA NAN

    1- Ido. Idan Aljani ya sha wahala ya fita ta idon mara lafiya ko aka ba shi umarnin fita ta nan, to mutum zai iya makancewa ko ya lalata masa ido. 

       2- Kunne. Mutun zai iya rasa ji. 

      3- Bayan mutum, wato Aljani ya ce zai fita ta dubura, shi ma akwai cutarwa. 

      4- Gaba, kamar Aljani ya ce zai fita ta farjin mace. Wannan zai iya haifar mata da zubar jini ko wasu cututtuka irin na mata. 

      5- Duk wata kafa ko wani waje da Aljani ya ambaci cewa zai fita ta nan to kada ka ba shi umarni indai ka ji cewa akwai shakku ko kuma bai kwanta ma ka a zuciya ba.

   GURAREN DA SU KA FI SAUƘIN FITA BA TARE DA CUTARWA BA. 
     1- Dunduniyar ƙafa. Wato kawai ka ga mutum ya ɗan ɗaga ƙafarsa, shi kenan Aljanin ya fita. 

      2- Gaɓoɓon jiki. Ka ce Aljanin ya rarraba kan sa, ya fita ta gaɓoɓin jikin mara lafiyar. 

       3- Attishawa. Wato mutum yay attishawa, Aljanin ya fita. Saidai a irin wannan wani yana yin gigitacciyar atishawa, wani kuma yana iya yin atishawa daga uku zuwa goma kafin ya iya fita. Wani ma zai yi ya gama, ya kasa fita. 

      4- Hamma. Wato mutum ya buɗa baki, sai Aljanin ya bi iska ya fita. Shi ma yana da sauƙi amma in ba ai sa'a ba Aljanin yana iya barin cuta a bakin mutum. 

     
   Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
    Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts