SIHIRIN SAKAWA MUTUM KASALA DA MUTUWAR ZUCIYA. WATO SIHRUL KHUMUWL. (سِحْرُ الْخُمُولِ) Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846


        Acikin littafin
 «الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار»
na Shaikh Waheed bin Abdus-Salam Baali ya kawo bayani akan wannan sihiri da ake kira Assihrul Khumuwl, wato asirin da ake yi don sakawa mutum kasala da rashin iya aikata abu mai amfani.

    Wannan nau'in sihiri ko tsafi, ana yin sa ne domin a haifar wa mutum da tsananin kasala, gajiyawar jiki, raunin kuzari, dusashewar himma da raguwar sha’awar gudanar da ayyukan rayuwa. Ana danganta wannan yanayi da sauyin halayen mutum, ta yadda zai iya zama mai son kaɗaici, guje wa mutane, ƙin aikinsa ko karatunsa, sakaci da nauyin da ke kansa, yawan bacci, da jin nauyin tashi ko motsa jiki. 
    YADDA ZA KA GANE SIHRUL KHUMUWL
 Wato sihirin sakawa mutum kasala da mutuwar zuciya.

1- الْعَجْزُ وَالْكَسَلُ الشَّدِيدُ

     Kasancewa cikin kasala da gajiya mai tsanani a kowane lokaci, ko da ba a yi wani aiki ba, kuma ba tare da an san wata cuta ko lalura ta zahiri da ke haddasa hakan ba ga mutum ba.

2- ثِقَلُ الْجَسَدِ وَصُعُوبَةُ الْحَرَكَةِ

Jin nauyin jiki da wahalar motsa shi ba tare da wani sanannen dalili ba.

3- ضَعْفُ الْهِمَّةِ وَفُتُورُ النَّشَاطِ

Raunin himma da raguwar kuzari, ta yadda mutum yake ganin ƙoƙarinsa da himmarsa wajen gudanar da ayyuka suna raguwa ba tare da sanannen dalili ba.

4- الْمَيْلُ إِلَى الْعُزْلَةِ وَتَجَنُّبُ النَّاسِ

Son kaɗaici da nisantar mutane, ta yadda mutum zai koma zama shi kaɗai a ɗaki ko wani wuri, yana guje wa cuɗanya da mutane.

5- كَثْرَةُ النَّوْمِ وَالنُّعَاسِ الْمُتَكَرِّرِ

Yawan bacci da yawan jin barci, har ma a kasuwa ko wajen aiki da inda bai kamata mutum ya kasance yana bacci ba.

6- التَّعَبُ وَالْإِرْهَاقُ بِغَيْرِ مَجْهُودٍ

Jin gajiya da kasala ba tare da yin wani aiki mai yawa ko mai wahala ba.

7- النُّفُورُ مِنَ الْعَمَلِ وَالدِّرَاسَةِ

Rashin sha’awar aiki ko karatu. Mutum ya ji sha’awar karatu ko sana’arsa ta fita daga ransa, har idan aka yi masa maganar hakan, sai hankalinsa ya tashi ko hankalinsa ya dinga tashi.

8- إِهْمَالُ الْمَسْؤُولِيَّاتِ وَالْوَاجِبَاتِ

Mutum ya dinga sakaci da nauyin da ke kansa da ayyukan yau da kullum. Wato mutum ya yi watsi da abubuwan da suka wajaba a kansa, kamar kula da iyalansa, ma’aikatansa ko wajen sana’arsa.

9- ضَعْفُ التَّرْكِيزِ وَكَثْرَةُ النِّسْيَانِ

Raunin mayar da hankali da yawan mantuwa. Wato mutum ya dinga shiririta, mantawa da alƙawura ko manta abubuwan da suke da muhimmanci a gare shi.

10- الْمَلَلُ مِنَ الْبَيْتِ وَمَكَانِ الْعَمَلِ

Jin ƙyamar zama a gida, rumfar kasuwa ko unguwarsa ba tare da sanannen dalili ba, har mutum ya dinga jin ya gaji da waɗannan wurare.

11- صُعُوبَةُ الِاسْتِيقَاظِ مِنَ النَّوْمِ

Wahalar tashi daga kan gado ko shimfiɗar bacci. Mutum ya kasa tashi don sallar Asuba, har wani lokaci rana ta yi  amma bai tashi ba, ba tare da sanannen dalili ba.

12- النُّفُورُ مِنَ الْأَهْلِ وَالْأَصْدِقَاءِ

Rashin sha’awar cuɗanya da iyali da abokai. Mutum ya ƙaurace wa matansa, ’ya’yansa, ’yan’uwansa na jini da sauran abokan hulɗarsa ba tare da sanannen dalili ba.

13- الْفُتُورُ عِنْدَ الشُّرُوعِ فِي الْأَعْمَالِ

Jin kasala da raunin kuzari da zarar mutum ya fara ayyukan da ya saba yi, waɗanda a da ba sa yi masa wahala.

      Amma a kula.
       Idan mutum na da wasu daga cikin irin waɗannan alamomi to ya kamata a je asibiti a binciki wasu dalilai masu yiwuwa kamar ƙarancin jini, matsalolin ƙwayar thyroid, rashin isasshen bacci, baƙin ciki mai tsanani (depression), ko illolin shan wasu magunguna ko shan ƙwaya. Sai kuma a dinga haɗawa da maganin karya sihiri da magance matsalolin Aljanu da kuma addu'oi.

     Ba dukkan bayanan da na kawo ne suke daga littafin Assarimul battar ba, na samu wasu alamomin da wasu bayanan ne daga littattafan wasu Malaman daba.

  WASU DAGA CIKIN ADDU'O'I DOMIN NEMAN TSARI DAGA IRIN WANNAN MATSALA.

     Na ɗaya (1). An karɓo daga Anas bin Malik رضي الله عنه cewa Annabi ﷺ ya kasance yana cewa:

«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ، وَالْعَجْزِ وَالْكَسَلِ، وَالْجُبْنِ وَالْبُخْلِ، وَضَلَعِ الدَّيْنِ، وَغَلَبَةِ الرِّجَالِ».
Ma'ana:
    
       Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga damuwa da baƙin ciki, da gazawa da kasala, da tsoro da rowa, da nauyin bashi da rinjayen mutane a kaina.

Bukhari ne ya rawaito shi.
    
        Na biyu (2). Magance matsalar ta hanyar ruƙiyyah.
Mutum zai iya dinga:

1) Karanta Suratul Fātiha.

2) Karanta Ayatal Kursiyyu, wato aya ta 255 a cikin Suratul Baƙara.

3) Karanta ayoyi biyu na ƙarshe na Suratul Baƙara (Amanar Rasuwlu).

4) Karanta ayoyin
    Suratul A’arāf (117–122), Suratu Yunus (81–82), da Suratu  Ɗāhā (69).

5) Karanta Suratul Ikhlās, Suratul Falaƙ da Suratun Nās.

    Sai a dinga yawan karanta su ko a dinga tofawa a ruwa ana sha ana wanka ko shafe jiki ko tofawa a jiki ko rubuta su ana sha.

       Na uku (3)  Yin addu’a da neman tsarin Allah daga gazawa da kasala, tare da kiyaye salloli da azkāran da aka tabbatar a Shari’a.

     Musulmi zai iya yi wa kansa ruƙiyya ko kuma ya nemi taimakon amintaccen mai ruƙiyya wanda yake bin Alƙur’ani da Sunnah, yana guje wa tsafe-tsafe, neman taimakon aljanu da sauran hanyoyin sihiri da bokanci.

   Na huɗu (4).  Haka nan akwai buƙatar a hada magunguna yadda ya kamata ga mutum, kamar magungunan sha da na wanka da na shafawa da na turare da dai sauransu don taimakawa ƙwaƙwalwa da zuciya da kuma karya asiri da magance matsalolin Aljanu. Domin maganin Karya sihr da korar Aljanu yana bukatar magunguna kala-kala don yaƙar matsalar, ba magani guda ɗaya ko biyu ba.

Daga shafin Dr. Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. 
   Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts