MA'ANAR RUƘIYYAH A WAJEN WASU DAGA MALAMAN MUSULUNCI BISA SUNNAH, SUNAYENSU DA LITATTAFANSU. Daga shafin Dr. Bashir mai magani. Lambar waya 08134434846


1. Shaykh Dr. Sa’id bin Wahf al-Ƙahɗani

A Littafinsa التحصين من كيد الشياطين
'Attahsinu min kaidish shayaɗiyni'

 Ya ce "Ruƙiyyah ita ce tsari na kariya daga sharrin shaiɗanu da aljanu, ta hanyar amfani da ayoyin Al-Ƙur’ani da addu’o’in da Annabi ﷺ ya koyar.
2. Shaykh Wahid Abdussalam Bāli

Littafi القول المفيد في علاج الصرع والسحر والعين
'Alƙaulul mufiydi fiy ilajis sar'i was sihri wal ayni'

Ya ce "Ruƙiyyah ita ce karatun ayoyin Al-Ƙur’ani da wasu addu’o’i bisa ka’idojin shari’a domin warkar da sihiri, shigar aljanu da illar kambun ido.

3. Shaykh Muhammad bin Saalih al-Uthaymeen

Littafi الرقية الشرعية
'Arruƙ'yatush shar'iyyah'

Ya ce "Ruƙiyyah ita ce karatun abin da ya halatta daga Al-Ƙur’ani ko addu’o’in Annabi ﷺ don neman warkarwa daga ciwo ko tsari daga sharri, bisa ƙa’idar tauhidi da shari’a.

4. Shaykh Wahid Abdussalam Bāli

A littafin الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار
'Assarimul battar fit tasaddiy lis saharatil ashrar'.

Ya ce "Ruƙiyyah hanya ce ta shari’a wacce ake amfani da ita don yaƙar sihiri da sharrin bokaye, ta hanyar karatun ayoyi da addu’o’in da suka tabbata daga Annabi ﷺ.

5. Fatawowi daga Ibn Baz, Albani, Ibn Uthaymeen da sauransu

Littafin فتاوى العلماء في الرقية الشرعية
'Fatawil ulama'i fir ruƙ'yatish shar'iyyah'.

Su ka ce "Ruƙiyyah ita ce karatun Al-Ƙur’ani da addu’o’in da aka karɓo daga Annabi ﷺ bisa tauhidi domin warkarwa daga cututtuka, sihiri, da sharrin aljanu.

6. Shaykh Dr. Sa’ad bin Nasirish Shithri

Littafin الكشف عن حقيقة الرقية وما يتعلق بها
 'Alkashfu an haƙiyƙatur ruƙ'yati wama yata'allaƙu biha'.

Ya ce "Ruƙiyyah a shari’ance ita ce hanyar neman warkarwa da tsari ta hanyar karatun abin da ya tabbata daga Al-Ƙur’ani da Sunnah, tare da guje wa bidi’a da shirka.

7. Shaykh Muhammad al-Khudhoyri

Littafin السحر: حقيقته، أثره، علاجه
'Assihr: haƙiƙatuhu, asaruhu, ilajuhu.

Ya ce "Ruƙiyyah hanya ce ta halal da shari’a ta tanadar don magance sihiri da aljanu ta amfani da ayoyi da addu’o’in da ke da tushe daga Annabi ﷺ.

8. Shaykh Wahid Abdussalam Bāli

Littafi وقاية الإنسان من الجن والشيطان
'Wiƙayatil insani minal jinni wash shaiɗan'

Ya ce "Ruƙiyyah tsari ne na shari’a wanda ke kare mutum daga sharrin aljanu da shaiɗanu ta hanyar karatun ayoyi da azkar da aka shar’anta.

9. Shaykh Abdul Aziz bin Baz

Littafin التحذير من الذهاب إلى السحرة والمشعوذين
 'Attahziyru minaz zahabi ilas saharatil musha'awwiziyna'

Ya ce "Ruƙiyyah hanyar warkarwa ce ta shari’a bisa karatun Al-Ƙur’ani da addu’o’in Annabi ﷺ, saɓanin sihiri da aikin bokaye.

10. Shaykh Dr. Khalid al-Hibshi

Littafin الرقية الشرعية وأثرها في علاج السحر والعين والمس
'Arruƙ'yatish shar'iyyati wa asaruha fiy ilajis sihri wal ayni wal massi'

Ya ce 'Ruƙiyyah ita ce mafita ta shari’a don magance sihiri, kambun ido da shigar aljanu ta hanyar karatun ayoyi da azkar da aka tabbatar daga Annabi ﷺ.

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.


Comments

Popular Posts