ASIRIN KASHE AURE KO HANA MA'AURATA ZAMAN LAFIYA. WATO SIHRU TA‘AƊIYĪLIZ-ZAWĀJ (سِحْرُ تَعْطِيلِ الزَّوَاجِ) Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
A cikin Alkur'ani mai girma, suratul Baƙarah, ayah ta 102, Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi bayani akan sihiri da ake yi domin raba ma'aurata. Duk mai buƙata zai iya duba wannan ayah da fassararta da bayaninta domin samun ilimi akai. Na sha kafa hujja da ita wajen kawo bayanin sihiri don haka ba sai ma maimaita ta anan ba. Ayar da ta fara da 'Wattaba'uw'.
MA’ANAR SIHRU TA'AƊIYLIZ ZAWAJ
Malam Wahid bin Abdussalam Bali a cikin littafinsa
الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار
ya yi bayanin sihirin raba ma’aurata, inda ya kawo maganar Hafiz Ibn Kathir cewa:
«وَسَبَبُ التَّفْرِيقِ بَيْنَ الزَّوْجَيْنِ بِالسِّحْرِ: مَا يُخَيَّلُ إِلَى الرَّجُلِ أَوِ الْمَرْأَةِ مِنَ الْآخَرِ مِنْ سُوءِ مَنْظَرٍ أَوْ خُلُقٍ، أَوْ نَحْوِ ذَلِكَ مِنَ الْأَسْبَابِ الْمُقْتَضِيَةِ لِلْفُرْقَةِ».
Ma’ana: Dalilin raba ma’aurata ta hanyar sihiri shi ne a sanya wa miji ko mata tunanin ganin ɗayan a mummunar sura ko munanan ɗabi’u, ko wasu abubuwan da za su iya jawo rabuwa tsakaninsu.
Malamai da suka yi bayani a kan nau’o’in sihiri sun bayyana cewa da akwai wani nau'in Sihiri da ake yinsa wanda ya shafi raba ma’aurata, sanya ƙiyayya tsakanin ma'aurata da kuma sihirin ɗaure mutum daga saduwa da matarsa, da sauran matsaloli waɗanda suke da alaƙa da haka.
ALAMOMIN ASIRIN KASHE AURE KO HANA MA'AURATA ZAMAN LAFIYA.
WATO SIHRU TA‘AƊIYĪLIZ-ZAWĀJ (سِحْرُ تَعْطِيلِ الزَّوَاجِ)
1. تَحَوُّلُ الْمَحَبَّةِ إِلَى الْكَرَاهِيَةِ
Sauyin soyayya zuwa ƙiyayya.
Miji ko mata ya fara jin ƙyamar ɗayan ba zato ba tsammani, alhali a baya akwai soyayya da fahimtar juna.
2. كَثْرَةُ الشَّكِّ وَسُوءُ الظَّنِّ
Yawan shakku da mummunan zato.
Ma’aurata su riƙa yawan zargin juna ba tare da hujja mai ƙarfi ba, har hakan ya zama sanadin rikice-rikice a tsakaninsu.
3. عَدَمُ التَّسَامُحِ بَيْنَ الزَّوْجَيْنِ
Rashin yafiya ko afuwa tsakanin ma’aurata.
Ɗaya daga cikinsu ya kasa yafe wa ɗayan, ko da kuwa laifin ƙarami ne, kuma ya riƙa tuna tsofaffin saɓani.
4. تَضْخِيمُ الْمَشَاكِلِ الصَّغِيرَةِ
Girmama ƙananan matsaloli.
Ƙaramin saɓani ya riƙa zama babban rikici, har ya kai ga faɗa ko barazanar kashe aure.
5. تَشَوُّهُ صُورَةِ أَحَدِ الزَّوْجَيْنِ فِي نَظَرِ الْآخَرِ
Ganin abokin aure a mummunar sura.
Wato Miji ya riƙa ganin matarsa ba ta da kyau ko tana da munanan ɗabi’u, ko kuma mata ta riƙa ganin mijinta haka, ba tare da wani haƙiƙanin dalili bayyananne ba.
6. النُّفُورُ مِنَ الْمُعَاشَرَةِ الزَّوْجِيَّةِ
Ƙyamar kusantar juna a aure.
Ɗaya daga cikin ma’aurata ya riƙa jin ƙyamar kusantar abokin aurensa, duk da cewa a baya ba haka lamarin yake ba.
7. الرَّغْبَةُ فِي الِابْتِعَادِ عَنِ الزَّوْجِ
Son nisantar abokin aure.
Ɗaya ya riƙa son zama nesa da ɗayan, ya guji zama tare da shi, ko ya zama yana jin daɗi ne kawai idan ba sa tare.
8. كَثْرَةُ النِّزَاعِ وَالْخِصَامِ
Yawaitar saɓani da husuma.
Rikici ya yawaita a tsakanin ma’aurata, har sukasa samun kwanciyar hankali da fahimtar juna.
9. الْغَيْرَةُ الْمُفْرِطَةُ
Kishin da ya wuce kima ko kishin hauka.
Ɗaya ya riƙa tsananin kishi da zargi ba tare da hujja mai ƙarfi ba, har hakan ya zama sanadin faɗa da rashin zaman lafiya.
10. التَّفْكِيرُ الْمُتَكَرِّرُ فِي الطَّلَاقِ
Yawan tunanin kashe aure.
Ɗaya ko duka biyun su riƙa tunanin rabuwa a kai a kai, ko da kuwa ba a daɗe da fara zaman aure ba.
11. زَوَالُ الرَّغْبَةِ عِنْدَ الِالْتِقَاءِ بَعْدَ الشَّوْقِ فِي الْغِيَابِ
Idan ba sa tare suna sha’awar juna amma idan sun haɗu sai sha’awar ta ɗauke.
Wato mutum na son ya kusanci matarsa, ita ma tana son hakan, amma da zarar sun haɗu sai kowa ya ji sha’awar ta fita daga ransa.
12. الْعَجْزُ الْجِنْسِيُّ عِنْدَ مُعَاشَرَةِ الزَّوْجَةِ
Gushewar kuzarin namiji ga matarsa.
Namiji yana da kuzari a wajen wata matar, amma idan ya je wajen matar da aka yi musu sihirin sai gabansa ya ƙi aiki.
13. الشُّعُورُ بِرَائِحَةٍ كَرِيهَةٍ مِنَ الزَّوْجِ أَوِ الزَّوْجَةِ
Jin wari marar daɗi daga juna.
Haka kawai namiji ya ji matarsa tana yi masa wani wari da ba ya so, ko kuma ita ta riƙa jin haka daga gare shi, alhali babu warin a zahiri.
A shawarce, idan ma'aurata su ka fara samun matsaloli a tsakaninsu waɗanda su ka kasa gane asalinsu ko yadda za a magance su, to ya kamata su tuntuɓi magabatansu don a taimaka musu gyara zamantakewarsu. Idan haka ya ci tura to su dinga neman shawarwarin Malamai da masana, sannan a nemi Malaman sunnah don neman magani da addu'o'i don tsari daga sharrin masihirta da mahassda da kuma sharrin shaiɗanun Aljanu.
Daga shafin Bashir Halilu mai ruƙiyyah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846

Comments
Post a Comment