YADDA ZA KA YI MAGANA DA ALJANI MUSULMI ALJANI KO KAFIRI DA ALJANI MAI GARDAMA KO MAI SAUƘIN KAI. Daga shafin Dr. Bashir Halilu Lambar waya 08134434846.
Azabtar da Aljani ko kashe shi ba ita ce manufar yin ruƙiyyah ba. Don haka a cikin ruƙiyyah, bai kamata malami ya yi mu’amala da aljani cikin fushi, zalunci, cin mutunci ko abin da ya saɓa wa Shari’a ba.
Manufar ita ce karanta Alƙur’ani da addu’o’in da su ka halatta, yin nasiha, kira zuwa ga Allah, da neman waraka.
Kuma bai kamata a ɗauki duk wata magana ko da’awar aljani a matsayin gaskiya ba.
Aljanu ba su taru sun zama ɗaya ba, suna da banbancin addinai, ɗabi'u da al'adu da sauran abubuwan da su ka bambanta mutane. Don haka ga bayani akan yadda za ka mu'amalanci Aljani musulmi da kafiri, da kuma Aljani mai taurin kai ko mara gardama idan su ka bayyana a gare ka yayin da kake yin ruƙiyyah.
1. YADDA ZA KA MU'AMALANCI ALJANI MUSULMI IDAN YA BAYYANA KO YA CE SHI MUSULMI NE.
1). Duk Aljanin da ya gabatar da kan sa a matsayin Musulmi, to tashin farko ka ce ya yi ma ka kalmar shahada ka ji, don kada arnen Aljani ya yaudare ka.
2) Ka yi masa nasiha da tunatarwa da Allah cikin nutsuwa, a matsayinsa na ɗan uwanka Musulmi.
3) Ka tunasar da shi cewa zaluntar mutum ko shiga jikinsa ba tare da hakki ba abu ne da ya saɓawa Allah Maɗaukakin Sarki.
4) Ka umarce shi ya bar jikin mara lafiya kuma kada ya sake cutar da shi ko dawowa jikinsa.
5) Ka tunasar da shi da ayoyi da hadisai game da tsoron Allah, tuba da barin zalunci.
6) Kada malami ya yi masa alkawarin wani abu ko ya kulla wata yarjejeniya da shi. Misali ya ce dole a ɗena batawa matar da ya shiga jikinta rai, ko kuma ya ce dole a dinga yin sadaka da dai sauransu.
7) Idan ya fita, a ci gaba da karatun ruƙiyyah da addu’a domin kare mara lafiya.
8) Ba a bukatar malami ya yi doguwar muhawara da shi ko ya nemi bayanan sirri daga gare shi sai kawai abinda ya zama lalura.
2. YADDA ZA KA MU'AMALANCI ALJANI KAFIRI.
Idan aljani ya bayyana yana cewa shi kafiri ne:
1) Ka yi masa da’awa zuwa ga Musulunci cikin hikima da nasiha.
2) Ka bayyana masa tauhidi, da cewa ibada ta Allah kaɗai ce, Allah kaɗai ake bautawa.
3) tunasar da shi sakamakon kafirci da muhimmancin tuba zuwa ga Allah.
4) Idan Aljani ya karɓi Musulunci, kada ka ɗauki maganarsa a matsayin hujja cewa shikenan ba matsala; a maida hankali kan cewa lallai ya bar jikin mara lafiyar. Domin wani Aljanin yana yarda ya musulunta amma ya ce ba zai bar jikin mutum ba.
5) Idan ya ƙi, malami ya ci gaba da ruƙiyyah da karatun Alƙur’ani da addu’o’in kariya, ba tare da shiga zagi ko tsinuwa mara dalili ba.
Manufar ita ce da’awa da kubutar da mara lafiya, ba nuna iko ko wahalar da aljani ba.
3. YADDA ZA KA MU'AMALANCI ALJANI MAI TAURIN KAI
Wannan nau'in Aljani shi ne wanda yake ƙin fita, yana gardama, yana barazana ko yana ƙoƙarin hana yin ruƙiyyar.
A irin wannan yanayin:
1) Malami ya kasance mai nutsuwa, kada ya fusata.
2) Ka ƙara dagewa da karatun Alƙur’ani da addu’o’in ruƙiyyah na shari’a.
3) Ka umarce shi ya bar jikin mara lafiya kuma ya daina cutar da shi.
4) Kada ka yi amfani da kayan tsafi, sihiri, layoyi, ko kalmomin da ba a san ma'anarsu ba, ko wata hanyar haram.
5) Kada a yi wa mara lafiya dukan tsiya, ko shake shi, ko ƙona shi, ko cutar da jikinsa saboda wai ana azabtar da aljani.
6) Idan ta kama za a daki Aljani ajikin mara lafiya to a dake shi a tafin hannu ko tafin ƙafa. Kada ayi dukan da mutum zai cigaba da jin zafi bayan an gama ruƙiyyar
7) A yi amfani da turarukan hayaƙi ko na shafawa ko ruwan ruƙiyyah, amma kada a yi amfani da su a yanayin tsanantawa sosai.
8) Idan al’amari ya zama mai haɗari, to a dakatar da abin da zai iya cutar da mara lafiya, sai a baiwa mutum magunguna da addu'o'i ya yi amfani da su, a sake yin ruƙiyyar wani lokacin daban.
4. YADDA ZA KA MU'AMALANCI ALJANI MARA GARDAMA.
Wato Aljanin da ya bayyana ba tare da tashin hankali ba, idan an tambaye shi yana amsawa cikin natsuwa kuma ya yarda ya bar jikin mara lafiya.
1) Ka yi masa nasiha cikin nutsuwa.
2) Ka umarce shi ya fita ba tare da cutar da mara lafiyar ba.
3) Kada malami ya ci gaba da tsawaita hira da shi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
4) Kada ka nemi jin ko sanin wasu sunaye, bayanan sirri, ko labaran wasu mutane daga gare shi.
5) Bayan haka a ci gaba da ruƙiyyah da addu’a domin tabbatar da cewa mara lafiyar ya samu nutsuwa da kariya.
6) Kada a yi gaggawar tabbatar wa mara lafiya cewa “aljani ya fita” bisa ga magana ko wani motsi kawai da Aljanin ya yi, a duba halin mara lafiya a tabatar fita.
Kuma babbar ƙa’idar ita ce: ruƙiyyah ta shari’a ba ta dogara da tattaunawa da aljani kawai ba; tana dogara ne da karanta Alƙur’ani, addu’o’in da su ka halatta, da tawakkali ga Allah.
Daga shafin Dr. Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment