YADDA AKE FARA RUƘIYYAH Wato Abubuwan da za ka fara yi a Ruƙiyyah Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
1. Shirya Kai da Tsarkake Niyya.
Alwala: Akwai buƙatar Mai ruƙiyyah da mara lafiya su yi alwala, in da hali.
Dalili: Annabi ﷺ ya ce:
> "Tsabta rabin imani ce." (Muslim, Hadisi na 223)
Don haka yin Ruƙiyyah cikin tsarki da tsafta na ƙara baiwa mara lafiya da mai Ruƙ'yar kariya kada Aljanin ya koma jikinsu.
Niyya: A nufi neman waraka daga Allah, ba sihiri ko neman kuɗi ba.
Wannan bayani ya fito daga Ibnu Qayyimil -Jawziyyah, a cikin Zādul-Ma‘ād fī Hadyi Khayril-‘Ibād.
2. Addu’ar Tsari Kafin a Fara.
Mai ruƙiyyah ya yi addu’ar neman tsari ga kansa da sauran wadanda suke wajen kada Aljani ko sihirin da suke cirewa ya koma jikinsu. Misali, mutum zai iya karanta
“Bismillāhi alladhī lā yaḍurru ma‘a ismihi shay’un fī l-arḍi wa lā fī s-samā’i wa huwa s-samī‘u l-‘alīm”
(Tirmidhi, 3388, sahihi).
Karanta Ayatal Kursiyyu (Baqarah: 255) don tsari.
Hadisi: "Duk wanda ya karanta Ayatal Kursiyyu da dare, Allah zai yi masa mai tsaro, shaiɗan ba zai kusanto shi ba har safiya." (Bukhari, 2311).
Imamuz Zhahabī, a cikin littafins Ɗibbun-Nabawī.
3. Shirya Mara Lafiya.
Ka fara yi wa mara lafiya bayani cewa ba kai ne mai ba da lafiya ba, komai na Allah ne. Ka sa shi cikin tawakkali da kwarin guiwa.
Annabi ﷺ ya ce:
> “Ku yi ruƙiyyah, babu laifi da ruƙiyyah muddin ba ta kunshi shirka ba.” (Muslim, 2200).
Jalālud-Dīn as-Suyūɗīy, a cikin littafinsa ar-Ruqā wa’l-ʿAwādh da al-Ḥāwī li’l-Fatāwī.
4. Inda Za a Kalla.
Mara lafiya zai kalli mai ruƙiyyah ko ya runtse idanu yana saurare.
Dalili: A lokacin da Annabi ﷺ yake yi wa Sahabbai ruƙiyyah, sukan saurare shi. (Muslim, 2192).
Shaykh ʿAbdullāh ibn Jibrīn.
Mara lafiya zai zauna a gabanka ya kalle ka, ko ya juya bayansa, ko kuma ya kalli damanka. Abu mafi muhimmanci dai shi ne ya zamto karatunka yana shiga kunnensa da sauti sosai.
5. Ɗora Hannu a Jikin Mara Lafiya.
A ɗora hannun dama a wurin ciwo ko a ƙirjin mara lafiya.
Dalili: Anas bn Malik ya ce:
> "Annabi ﷺ ya ce: Ka dora hannunka a kan inda kake jin ciwo ka ce: Bismillāh sau uku, sannan ka ce: A‘ūdhu billāhi wa qudratihi min sharri mā ajidu wa uḥādhiru sau bakwai." (Muslim, 2202).
Idan yaro ne za ka ɗora hannunka akan kirjinsa, idan babba ne namiji za ka ɗora hannunka a kansa ko ka riƙe goshinsa. Idan mace ce babba sai mijinta ko maharraminta ya ɗora hannunsa a kanta, kai kuma ka yi karatun.
6. Sai ka fara karanta Alƙur'ani da wasu daga addu'o'in Manzon Allah (SAW) waɗanda ka sani.
7.
Ga misalin Ayoyi da addu'o'in da za ka iya yin Ruƙiyyah da su.
1. Fātiḥa
﴿بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ الْـحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ﴾
2. Al-Baqarah: 1–5
﴿الم ذَٰلِكَ الْكِتَابُ لَا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ وَالَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِالْآخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ أُو۟لَـٰئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ﴾
3. Ayatul Kursiyy (Al-Baqarah: 255)
﴿اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْـحَيُّ الْقَيُّومُ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾
4. Suratul Baqarah: 285–286
﴿آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ ۚ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ ۚ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ...﴾
5. Suratul A‘rāf: 117–122 (Ayoyin da suka yi nasara akan sihirin Fir’auna)
﴿وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ فَوَقَعَ الْـحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانقَلَبُوا صَاغِرِينَ وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ رَبِّ مُوسَىٰ وَهَارُونَ﴾
6. Suratus-Saffāt: 1–10
﴿وَالصَّافَّاتِ صَفًّا فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًا فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًا إِنَّ إِلَٰهَكُمْ لَوَاحِدٌ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِ إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِ وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍ لَا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْـمَلَإِ الْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ إِلَّا مَن خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌ﴾
7. Suratul Jinn: 1–9
(Domin kariya daga sharrin aljanu)
8. Suratul Ikhlāṣ, Falaq da Nās
Ikhlāṣ: ﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ اللَّهُ الصَّمَدُ لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُوًا أَحَدٌ﴾
Falaq: ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ مِن شَرِّ مَا خَلَقَ وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ﴾
Nās: ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ مَلِكِ النَّاسِ إِلَٰهِ النَّاسِ مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْـخَنَّاسِ الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ﴾
WASU DAGA ADDU'OÇIN MANZON ALLAH (SAW) DA AKE YIN RUƘIYYAH DA SU.
🔹 1. Ruƙ’iyyah don Ciwon Jiki ko Raɗaɗi.
An karɓo daga Usman bn Abil-‘Ās رضي الله عنه cewa ya zo wajen Annabi ﷺ yana da ciwo a jikinsa, sai Annabi ﷺ ya ce:
> ضَعْ يَدَكَ عَلَى الَّذِي تَأَلَّمَ مِنْ جَسَدِكَ، وَقُلْ: بِسْمِ اللَّهِ (ثَلَاثًا)، وَقُلْ سَبْعَ مَرَّاتٍ: أَعُوذُ بِاللَّهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ
Ma’ana: “Ka ɗora hannunka inda kake jin ciwo a jikinka, ka ce Bismillāh sau uku, sannan ka ce sau bakwai: A’ūzu billāhi wa qudratihi min sharri mā ajidu wa uḥādhir.”
(Hadisi a Muslim, 2202)
🔹 2. Ruƙ’iyyah ga wanda ya kamu da hasada ko kambun ido.
Annabi ﷺ ya ce:
> بِسْمِ اللَّهِ أُرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، وَمِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنٍ حَاسِدٍ، اللَّهُ يَشْفِيكَ، بِسْمِ اللَّهِ أُرْقِيكَ
Ma’ana: “Da sunan Allah nake yi maka ruƙiyya, daga duk abin da zai cutar da kai, daga sharrin kowace rai ko idanun mai hassada, Allah ne zai warkar da kai, da sunan Allah nake yi maka ruƙiyya.”
(Hadisi a Muslim, 2186)
🔹 3. Ruƙ’iyyah da Suratul Ikhlāṣ, Falaq da Nās
A kowane dare Annabi ﷺ ya kan haɗa hannayensa ya hura musu ya karanta:
Qul huwa Allāhu Aḥad, Qul a’ūzu birabbil-falaq, Qul a’ūzu birabbin-nās sannan ya shafe jikinsa gaba ɗaya da su.
(Hadisi a Bukhari, 5017; Muslim, 2192)
🔹 4. Ruƙ’iyyah da Fātiḥa
Sahabbai sun yi ruƙiyya da Suratul Fātiḥa ga wani da maciji ya cije shi, sai ya warke. Annabi ﷺ ya ce:
> وَمَا يُدْرِيكَ أَنَّهَا رُقْيَةٌ؟
“Yaya ka san Fātiḥa ruƙiyya ce?”
(Bukhari, 5736; Muslim, 2201)
🔹 5. Addu’ar Ruƙ’iyyah ga marar lafiya.
Annabi ﷺ idan ya ziyarci mara lafiya sai ya ce:
> اللَّهُمَّ رَبَّ النَّاسِ، أَذْهِبِ الْبَأْسَ، اشْفِ أَنْتَ الشَّافِي، لَا شِفَاءَ إِلَّا شِفَاؤُكَ، شِفَاءً لَا يُغَادِرُ سَقَمًا
Ma’ana: “Ya Allah, Ubangijin mutane, ka ɗauke cuta, ka warkar. Kai ne Mai warkarwa, babu warkarwa sai naka, warkarwa wadda ba za ta bar ciwo ba.”
(Bukhari, 5743; Muslim, 2191)
🔹 6. Addu’ar Ruƙ’iyyah gaba ɗaya (ta kariya).
Annabi ﷺ ya kan ce:
> أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ
Ma’ana: “Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga duk shaiɗan da kowace halitta mai cuta, da kuma daga kowace idanu mai cutarwa.”
(Bukhari, 3371)
7). Amfanin Masu Taimaka ma ka wajen Ruƙiyyah.
Su taimaka mara lafiya idan yana karkarwa ko motsi saboda aljanu.
Su amsa da “Āmīn” yayin da ake karatu.
Dalili: Annabi ﷺ ya yi ruƙiyyah, Sahabbai suna kusa suna amsa masa. (Abu Dawud, 3904).
Masu taimakawa su ne za su riƙe mara lafiya idan yana buge-buge ko yana ƙoƙarin guduwa. Kada a bari mara lafiya yana dukan ƙasa ko bango ko yana dukan jikinsa. Domin zai iya illata kansa ko ma rasa rai gaba ɗaya.
8- Amfanin kayan aikin da ka tanada.
Mun ambaci cewa za ka tanadi ruwan Ruƙiyyah, man Ruƙiyyah, turaren hayaƙi. Za ka yi amfani da su ne wajen shafawa da zubawa a jikin mara lafiya idan Aljani ya yi ma ka taurin kai.
A darasi na gaba kuma za mu koyarda yadda ake haɗa ruwan ruƙiyyah da man ruƙiyyah da turaruka da dai sauransu.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment