ASIRIN HANA MA'AURATA KUSANTAR JUNANSU WATO SIHRUR RABƊI (سِحْرُ الرَّبْطِ) Daga shafin Bashir Halilu.Lambar waya 08134434846.
Asirin ɗaure namiji daga kusantar matarsa, wato mutum ya kasa saduwa da matarsa alhali in ya je wajen watar matar kuma sai lafiyarsa ta dawo, wato sihirin da ake yi domin hana mutum iya saduwa da matarsa, ko hana ma'aurata jin daɗin saduwa da juna.
Wannan nau'in sihiri yana da alaƙa da abin da wasu malamai suka kira
سحر الصرف
Sihirus-Sarfu, wato sihirin karkatar da mutum daga abin da yake so, musamman dangane da sha'awar saduwa da iyalinsa.
NAU'O'IN SIHIRIN RABƊI
A cikin littafin
الحذر من السحر
na Dr. Khālid bin Abdur-Rahmān Al-Juraysī, da kuma littafin
الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار
na Sheikh Waheed Abdus-Salam Bāli, an yi bayanin wasu nau'o'in sihirin rabɗu da yadda ake iya samun tasirinsa ga wanda aka yi wa.
Ga wasu daga cikin siffofin da aka ambata:
1. رَبْطُ الرَّجُلِ عَنِ امْرَأَتِهِ
Wato ɗaure namiji daga saduwa da matarsa, ta yadda yake samun matsala wajen saduwa da ita duk da yana da sha'awa da lafiya da kuzari amma sai ya rasa me ya ke hana shi.
2. رَبْطُ الْعُنَّةِ
Wato samun rashin ƙarfin mazakuta a lokacin da mutum yake son saduwa da matarsa, alhali ba lallai ne ya kasance yana fama da wannan matsalar a sauran lokuta ba. Ko kuma gaban mutum ya ƙi tashi a lokacin, in kuma ya haƙura da saduwar sai gaban ya dawo da ƙarfinsa.
3. رَبْطُ الْقَذْفِ
Wato saurin saurin inzali a lokacin saduwa, ta yadda mutum ba ya iya kammala saduwar yadda ya kamata.
4. رَبْطُ الشَّهْوَةِ
Wato gushewar sha'awar saduwa da abokin zama, ko mutum ya kasance ba ya jin sha'awar matarsa duk da yana son ta amma yana sha'awar wasu matan, ko kuma ita mace ta ji ba ta sha'awar mijinta amma tana sha'awar wasu mazan.
5. رَبْطُ النَّفْرَةِ
Wato sanya ƙyama da ƙauracewa tsakanin ma'aurata, ta yadda mutum yake jin tsanar kusantar matarsa ba tare da sanin dalili ba ko kuma ita matar ta ke tsanar mijinta ba dlili.
6. رَبْطُ الْبُرُودِ
Wato sanya mace ta kasance ba ta jin daɗin saduwa da mijinta, ko kuma ta kasance tana jin wani irin sanyi da rashin sha'awa yayin saduwa.
7. رَبْطُ التَّصْفِيحِ
Wannan sihiri ne musamman da ake yi wa mace domin hana mijinta iya saduwa da ita a daren farko na aurensu.
ALAMOMIN SIHIRUR RABƊI
Wato Asirin Hana Ma'aurata Mu'amamalar aure.
1. عَدَمُ قُدْرَةِ الرَّجُلِ عَلَى الْجِمَاعِ
Namiji ya kasa saduwa da matarsa a lokacin da yake son hakan.
2. ضَعْفُ الِانْتِصَابِ عِنْدَ الرَّجُلِ
Mazakuta ta kasa tsayuwa a lokacin da mutum yake son saduwa da matarsa.
3. زَوَالُ الشَّهْوَةِ عِنْدَ اقْتِرَابِ الرَّجُلِ مِنِ امْرَأَتِهِ
Mutum ya kasance yana jin sha'awar saduwa, amma da zarar ya kusanci matarsa sai sha'awar ta gushe.
4. النُّفُورُ مِنْ مُقَارَبَةِ النِّسَاءِ بِغَيْرِ سَبَبٍ ظَاهِرٍ
Jin ƙyamar kusantar mata ba tare da wani dalili bayyananne ba.
5. الشُّعُورُ بِالضِّيقِ وَالنُّفُورِ عِنْدَ دُخُولِ غُرْفَةِ النَّوْمِ مَعَ الزَّوْجَةِ
Miji ya kasance yana jin daɗin zama da matarsa, amma da zarar sun shiga ɗakin kwana sai ya ji wani irin damuwa ko ƙin kusantarta.
6. نُفُورُ الْمَرْأَةِ مِنْ مُجَامَعَةِ زَوْجِهَا بِغَيْرِ سَبَبٍ تَعْرِفُهُ
Mace ta kasance tana jin ƙyamar saduwa da mijinta ba tare da wani dalili da ta sani ba.
7. عَدَمُ اسْتِمْتَاعِ الْمَرْأَةِ بِالْجِمَاعِ مَعَ مَحَبَّتِهَا لِزَوْجِهَا
Mace ta kasance ba ta jin daɗin saduwa da mijinta ko da kuwa tana son shi.
8. حُدُوثُ الْمُشْكِلَةِ خَاصَّةً عِنْدَ إِرَادَةِ الْجِمَاعِ
Matsalar ta kasance tana faruwa ne musamman a lokacin da mutum yake son saduwa da abokin zamansa.
MAGANAR WASU MALAMAN AHLUS-SUNNAH A KAN SIHIRIN RABƊI
Wato Sihirin Hana Ma'aurata Mu'amamalar Aure.
1. Sheikh Abdul-Aziz bin Abdullahi Ibn Bāz
An tambayi Sheikh Ibn Bāz game da wani sihiri da ake kira الربط, wanda ake yi wa ango domin ya kasa saduwa da amaryarsa a daren aurensu.
Sai ya amsa da cewa:
"Ba lallai ne hakan ya kasance yana faruwa a kowane lokaci ba, amma yana iya faruwa. Wasu mutane 4dz su iya fuskantar jarabawar da wani zai yi musu sihiri wanda zai hana su kusantar matansu".
Ya ci gaba da bayanin yadda ake yin ruƙiyyah da Fātiha, Ayatul Kursiyyu, ayoyin karya sihiri, Suratul Ikhlās da Mu'awwizataini.
Duba: مجموع فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز، 8/116.
2. Dr. Khālid bin Abdur-Rahmān Al-Juraysī.
A cikin littafinsa الحذر من السحر, ya yi bayanin cewa sihirin rabɗu yana da siffofi daban-daban, ciki har da wanda yake shafar ƙarfin saduwa da sha'awa, da kuma wanda yake haifar da ƙyama tsakanin ma'aurata.
Ya kuma yi gargaɗin cewa wasu cututtuka na jiki ko na tunani za su iya haifar da irin waɗannan matsaloli, saboda haka bai kamata a yi gaggawar hukunta cewa sihiri ne ba kafin a duba lafiyar mutum.
3. Sheikh Waheed Abdus-Salam Bāli.
A cikin littafinsa الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار, ya yi bayanai a kan sihiri da ake amfani da shi wajen cutar da zamantakewar ma'aurata, da kuma hanyoyin da shari'a ta yarda da su wajen neman waraka daga sihiri.
Ya kamata a lura cewa rashin ƙarfin mazakuta, rashin sha'awa, saurin inzali da sauran matsalolin saduwa suna iya kasancewa sakamakon cututtuka kamar ciwon suga, matsalar jijiyoyi, canjin sinadaran jiki, matsalar hormones, damuwa da sauran cututtukan lafiya. Saboda haka, wajibi ne mutum ya nemi shawarar likita domin a bincika lafiyarsa, kada ya jingina matsalar kai tsaye ga sihiri. Saidai idan matsalar ta gagara ko kuma an kasa shawo kanta sai a nemi waraka ta hanyar addu'o'i da magunguna na karya asiri da sauran matsalolin Aljanu.
Ya Allah Ka raba mu da sharrin masihirta da mahassada da dukkan masu sharri.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment