YADDA ZA KA GANE ALJANI YA BAYYANA A JIKIN MARA LAFIYA LOKACIN DA AKE MASA RUƘIYYAH. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.

   Idan ana gabatar da Ruƙ'yah, wani sa'in Aljani kan ji tsoro, ya gudu kafin yay magana. Wani yana laɓewa, ya ƙi yin magana saboda taurin kai. Wani kuma ya kan ɓadda kama, don kar a gane ya bayyana, sai ka ji ana cewa ai ba Aljanu bane. Wani Aljanun kuma yana bayyana amma mai Ruƙ'yar sai ya kasa gane cewa Aljani ya bayyana ko bai bayyana ba. Akwai kuma masu yin kuskure suna dukan mara lafiya ko kuma yi masa tsawa, suna zaton Aljani ne ya bayyana a jikin mara lafiya, alhali ba Aljanin ba ne.
GA WASU ALAMOMI DA ZA KA GANE ALJANI YA BAYYANA YAYIN RUƘ'YAH

1-   Idan aka fara karatu, Aljani kan iya bayyana da tsananin rawar jiki ko karkarwa. Wato jikin mara lafiya ya kama rawa. Tana iya yiwuwa bai fita daga hayyacinsa ba amma zai ji jikinsa yana rawa, ba ya iya sarrafa kan sa. Idan ba ka ga rawar jikin ta bayyana ba za ka iya tambayarsa shin yana jin jinkinsa yana rawa?!

2- Canjawar murya. 
      Za ka iya dinga yin karatun kana tambayar mara lafiya shin ko yana jin wani yanayi a jikinsa, ko kuma ka sa shi ya karanta ma ka wata aya ta Alkur'ani. Idan ka ji muryarsa na rawa ko ta canja zuwa wani yanayi daban to da alama ya fita daga hayyacinsa kuma Aljani ya bayyana.

 3- Yin ihu ko kururuwa. 
       A mafi yawan lokuta Aljanu kan bayyana ta hanyar kururuta ihu da bakin mara lafiya, musamman idan sun ji azabar karatu ko ta magunguna.

 4- Kuka ko zubar da hawaye. 
      Da zarar an fara karatu sai mara lafiya ya fashe da kuka ko ya kama zubar da hawaye.

 5- Ƙoƙarin hana mai Ruƙ'yar yin karatu ko jin karatun. 
     Wani sa'in idan Aljani ya bayyana sai ya dinga kokarin toshe bakin mai karatun da hannunsa ko kuma ya rufe kunnuwansa don kada karatun ya shiga kunnensa.

6- Rufe fuska da ƙanƙame jiki saboda zafin karatu ko na magunguna.

7- Ƙoƙarin guduwa ko shure-shure da buge-buge idan ana karatu. 
    Wani ma yana kai duka ko cizo ga mai karatun.

 8- Faɗuwa ko ƙoƙarin yin bacci.
    Wani sa'in Aljani na faɗuwa ƙasa, ya kwanta saboda zafin karatu. Wani kuma yana kokarin saka mara lafiyar bacci don kada karatun ya shige shi.

9- Juyewar idanu ko ƙafewa. 
     Wato ka ga idanun mara lafiyar sun ƙame, ba ya ƙiftawa ko kuma ka ga ƙwayar idonsa ta kalli ƙasa. Wani Aljanin ba ya iya hada ido da mutane, wani kuma in ya ƙura ma ido ko ƙiftawa ba ya yi.

10- Yin amai ko dalalar da miyau ko sakin tusa ko hamma ko atishawa akai-akai.

11- Jin kaikayi ko radadi a jiki. 
       Da zarar ka fara karatu, in ka ga mara lafiyar yana sosa fatar kan sa ko yana soshe-soshen jikinsa to da alama Aljani ya bayyana.

12- Surutai barkatai ko magana da wani yare mara ma'ana. 
    Wani Aljanin in yana so ya raina ma ka hankali sai ya kama yin wani yare wanda ba a fahimtar me ya ke cewa. Ko kuma yaren da shi mara lafiyar bai iya ba.

13- Wani Aljanin na bayyana da yin sallama, ko ambaton sunansa ko kuma ya nemi a tsaya ya yi magana. Wani kuma yana bayyana da barazana, rashin kunya ko zage-zage. Yayin da wani ke fara bin ka idan kana karatu, kuna yi tare.

14- Nuna ƙarfin jiki fiye da karfin maralafiyar. Wato Aljanin ya bayyana da kuzari da nuna karfi fiye da kimar karfin wanda akewa karatun.

15- Kin ambaton Allah ko kin karatun Alkur'ani. Idan ka kasa gane cewa Aljanin ya bayyana ko bai bayyana ba, sai ka ce maralafiyar ya yi ma ka kalmar shahada ko ya karanta ma ka wata Ayah ta Alkur'ani.  Idan Aljani ne zai ki karantawa ko kuma ya dinga karantawa da kuskure.

16- Tsananin gumi. 
    Wani mutumin ya kan jike da gumi idan Aljanin ya bayyana.

17- Cajawar kalar idanu su yi ja sosai

18- Kumburar jijiyar wuyar mutum.

19- Bugawar zuciya da karfi, ta yadda in ka taɓa kirjin mara lafiya za ka ji bugun zuciyarsa ya ƙaru. Za kuma ka iya tambayar maralafiyar ko yana ji gabansa yana faɗuwa.

 Waɗannan su ne wasu daga cikin hanyoyin da mai Ruƙ'yah zai fahimci cewa Aljani ya bayyana a jikin mara lafiya.

    Daga shafin Dr. Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts