SHIN AN YI WA MANZON ALLAH ﷺ SIHIRI? KUMA SHIN SIHIRIN YA KAMA SHI? Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.


     Wannan tambaya ce da wasu suke yawan yi: 
        "Shin da gaske an yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri? Idan an yi masa, ta yaya ya kasance?

       Amsa ita ce: Eh, an yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri, kuma wannan ya tabbata a cikin ingantattun hadisai. Amma sihirin bai shafi isar da saƙon Allah da wahayi ba. Wato sihirin ya saka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama rashin lafiyar jiki ne amma ta ɓangaren addini da isar da saƙon Allah komai dede ya ke yi.

        An karɓo daga Nana A’isha رضي الله عنها ta ce:

«سَحَرَ رَسُولَ اللَّهِ ﷺ رَجُلٌ مِنْ بَنِي زُرَيْقٍ يُقَالُ لَهُ لَبِيدُ بْنُ الْأَعْصَمِ»

Ma’ana: “Wani mutum daga ƙabilar Banu Zuraiq, mai suna Labīd ɗan Al-A‘ṣam, ya yi wa Manzon Allah ﷺ sihiri.”

      Hadisin ya bayyana cewa tasirin sihirin ya kai ga Annabi ﷺ yana tsammanin ya aikata wani abu alhali bai aikata shi ba. Daga baya Allah Ya sanar da shi abin da ya faru, kuma Ya ba shi lafiya. Sahihul Bukhari, Kitābuɗ ɗibbi, Bābus-Siḥri, hadisi na 5763.

Haka kuma, hadisin yana cikin Sahih Muslim, hadisi na 2189.

      A cikin hadisin, an bayyana cewa sihirin yana cikin wata rijiya da ake kira Bi’ru Dharwān (بِئْرِ ذَرْوَانَ). An kuma bayyana kayan da aka yi sihirin da su, waɗanda suka haɗa da matajin kai, gashin da ya rage bayan tsefewa da kuma murfin huda na dabino namiji.

      Shin sihirin ya shafi wahayi da saƙon Annabi ﷺ?

    A’a. Wannan shi ne muhimmin bambanci da ya kamata mu fahimta.

Sheikh Ibn Bāz رحمه الله ya ce:

«سُحِرَ وَعَافَاهُ اللَّهُ، فَالسِّحْرُ لَمْ يُؤَثِّرْ عَلَى رِسَالَتِهِ وَعَلَى تَبْلِيغِهِ»

Ma’ana: “An yi masa sihiri, Allah kuma Ya ba shi lafiya. Sihirin bai shafi manzancinsa ko isar da saƙonsa ba.”

Madogara: مجموع فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز، mujalladi na 8, shafi na 117.

    Saboda haka, faruwar wannan abu ba ta nufin cewa wahayi ya rikice ko cewa Annabi ﷺ ya isar da wani abu ba daidai ba daga Allah. Allah Ya kiyaye shi wajen isar da saƙon addininsa.

Ga ruwayar Hadisan.

    An karɓo daga Nana A'isha Allah Ya ƙara yarda a gareta, ta ce

       " Manzon Allah (SAW) ya yi rashin lafiya mai tsanani. Har ta kasance sai ya dinga ganin kamar ya aikata wani abu alhali kuma bai aikata ba.

        Ta ce wata rana yana dakina da daddare, yana ta addu'a, sai ya kwalla min kira ya ce "Albishirinki
ya A'isha, Allah ya sanar da ni abinda ke damu
na"

    Ya ce "Mala'iku biyu ne suka zo min, daya ya
tsaya a saitin kaina, dayan kuma a saitin kafa ta.    Sai na saitin kafar tawa ya ce da na saitin kan nawa 

    "Me yake damun wannan mutumin ne? "

   Sai ya ce masa "An yi masa tsibbu ne"

 Sai ya ce "Menene tsibbu? " 

Sai ya ce "Sihiri kenan".

Sai ya kuma ce masa "Wa yay masa sihirin? ".

  Sai ya ce " Wani Bayahude ne mai suna Labiydu binil A'asam, daga qabilar Baniy Zuraiƙin.

  Sai ya sake ce masa " To yanzu ina (aka binne)
asirin? "

Sai ya ce "A cikin rijiyar Zarawana."

  Daga nan sai Manzon Allah (SAW) ya aika Ammar bin Yasir da wasu mutane, su ka je rijiyar.

   B Sai su ka shiga cikinta, ruwan rijiyar gaba ďaya ya koma ja saboda bala'in sihiri. Su ka kwashe ruwan rijiyar, sai su ka samu an danne asirin ne da wani katon dutse. Suka dauke dutsen sannan suka fito
da Kullin sihirin.

     Da suka kawo wa Manzon Allah (SAW) sai ya warware shi, sai ga shi ashe an hada shi ne da
hudar ÿaÿan dabino namiji, masu kama da kan shaidanu. An yi qulle-qulle ne har guda goma sha daya.

     Sai Manzon Allah (SAW) ya karanta surorin Falaƙi da Nasi. Falaƙi aya biyar Nãsi aya
shida, goma sha daya kenan. In yakaranta duk aya daya sai ya tofa a qulli daya, sai qullin ya kwance da kansa, har dai ya gama gaba daya. Daga nan sai aka qona layoyin aka binne. Sai Manzon Allah (SAW) ya samu lafiya, kamar bai ta6a yin cuta ba.

    Wannan Hadisi na Nana A'isha (RA) ya zo da ruwayoyi da dama, mai son ganin wadannan Hadisai ka iya duba Littafin Šahiyhul Bukhãriy, Kitãbuɗ ɗubbi, Bãbus sihri, hadisi mai lamba ta 5763.

Sauran ɓangarorinsa kuma :- 5766, 5765, 3268,
3175.

Tuhfah:- 16928, 17022, 17134, 17145.

    A wasu riwayoyin an ce an haɗa baki ne da wani yaro Bayahude da ke shiga gidan Manzon Allah (SAW), ya samo musu gashin kan Annabi (SAW) a jikin matajin da Annabi (SAW) ya ke take kai da shi, sannan ya kakkaryo musu kan matajin sai aka haɗa sihirin da su.

        Kuma wannan hujja ce mai karfi da ke nuna cewa ana yin sihiri don a cutar da mutum. Sannan
babban darasi ne da ke nuna cewa ko kai wanene, komai girmanka, komai tsarkin ka komai
matsayinka agun Allah za a iya yi ma Asiri kuma
ya kama ka in Allah Ya so. 
          Sannan hujja ce da ke nuna cewa lallai ana iya karya sihiri bayan an yi shi kuma wanda akay wa ya samu lafiya.

     
   Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙiyyah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
 Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts