ASALIN SIHIRI KO TSAFI. TAFSIRIN WATTABA'UW. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
سُورَةُ الْبَقَرَةِ (١٠٢–١٠٣)
﴿١٠٢﴾ وَاتَّبَعُوا مَا تَتْلُو الشَّيَاطِينُ عَلَىٰ مُلْكِ سُلَيْمَانَ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَٰكِنَّ الشَّيَاطِينَ كَفَرُوا يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ وَمَا أُنْزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ ۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ ۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ ۚ وَمَا هُمْ بِضَارِّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ ۚ وَلَقَدْ عَلِمُوا لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ خَلَاقٍ ۚ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْا بِهِ أَنْفُسَهُمْ ۚ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ ﴿١٠٢﴾
﴿١٠٣﴾ وَلَوْ أَنَّهُمْ آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَمَثُوبَةٌ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ خَيْرٌ ۖ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ ﴿١٠٣﴾
【Tarjama】
102. Sai suka bi abin da shedanu suke karantawa a (zamanin) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai shedanun su ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala'iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun fada masa cewa:
"Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta".
Sai (mutane) suka rika koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da shi. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma hakika sun san cewa, tabbas duk wanda ya zabi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (hakikanin makomarsu).
103. Da a ce su sun yi imani kuma sun yi takawa, hakika da sakamakon (da za su samu) daga Allah shi ne mafi alheri, da a ce sun sani.
*
*
A nan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da ba da labarin halin da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki, bayan sun yi watsi da littafin Allah da koyarwar annabawansu, sai suka rungumi koyarwar shaidanu a madadin haka, wanda sakamakon haka shi ne duk wanda ya bar koyarwar annabawa da ilimi mai amfani, to lalle a madadinsa sai ya rungumi wani ilimi marar kyau mai cutarwa.
Don haka sai Yahudawa suka rungumi ilimin sihiri, kuma suka rika fadar karyar cewa, shi ne ilimin da Annabi Sulaiman yake amfani da shi wajen sarrafa mulkinsa, da shi ne ya mulki mutane da aljannu, har ma da dabbobi. Sai Allah ya karyata su, ya wanke Annabi Sulaiman (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) daga aikata duk wani tsafi, shi kuma ba kafiri ne ba, aikata tsafi kuma kafirci ne.
Don haka shaidanu ne suka kafirta ta hanyar fitowa suna koya wa mutane sihiri domin su batar da su daga kan hanya.
Hakanan Yahudawa suka rungumi sihirin da aka saukar wa wasu mala'iku su biyu, wato Harutu da Marutu a garin Babila da ke kasar Iraki, domin su zama jarraba ga mutane.
Su kuma wadannan mala'iku biyu ba sa yarda su koya wa wani sihirin, har sai sun yi masa nasiha da cewa:
"Mu fa wata jarrabawa ce daga Allah, don haka kada ka yarda ka kafirta ta hanyar koyon wannan sihirin da aiki da shi."
To amma duk da wannan nasihar tasu, sai mutane suka rika koyon sihiri daga wajensu, suna aikata miyagun ayyuka da su, kamar na raba tsakanin ma'aurata biyu masu kaunar juna. Kuma su wadannan matsafa ba su da ikon su cutar da wani da tsafinsu sai da izinin Allah da ganin damarsa.
Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa Yahudawan nan da suka yi watsi da littafin Allah, suka kafirce wa Annabi (3) suka riki tsafi da matsafa bayan sun san cewa, sun yi wa kansu zabin tumun-dare ne, sun saki reshe ne sun kama ganye, domin kuwa ba su da wani rabo a lahira daga gidan Aljanna. To Allah ya yi tir da irin wannan zabi na banza da suka yi wa kansu; da kuma sun san yadda suka sayar da kawunansu da rabonsu na lahira a kan wani abu kankani wanda zai cutar da su duniya da lahira to da ba su aikata haka ba. Kuma da sun nutsu sun tsaya sun zabi imani da tsoron Allah maimakon tsafi, to da Allah ya saka musu da mafificin abin da suke nema a nan duniya na irin amfanin da suke hangowa a cikin koyon sihiri da aiki da shi.
*
*
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1. Allah (Mai tsarki da daukaka) yana iya jarraba bayinsa ta hanyar hore musu wasu hanyoyi na saba masa, don ya tantance mai biyayya na gaskiya daga cikinsu, da wanda zai bijire; shi ne dalilin saukar da wadannan mala'iku guda biyu, Harutu da Marutu a kasar Iraki.
2. Dangane da wadannan mala'iku biyu, an samu ruwayoyi masu yawa, wadanda aka jingina wasu daga cikinsu zuwa ga Annabi (), wasu kuma aka dangana su ga wasu tabi'ai, kamar Mujahid da Suddi da Al-Hasanul Basri da Katada da sauransu. To amma fa babu wani labari da ya inganta cikin irin abin da aka ruwaito; hasali ma da yawa daga ciki an samo su ne daga Banu Isra'ila.
3. Wajibi ne mutum ya yi wa dan'uwansa nasiha da gargadi, ko da kuwa ba zai karba ba.
4. Sababi shi kadai a karan kansa ba shi da wani tasiri sai da izinin Allah (Mai tsarki da daukaka), don haka ya wajaba ga mumini ya rika komawa ga Allah (Mai tsarki da daukaka) ko da yaushe domin neman taimakonsa.
5. Duk mutumin da ya saki koyarwar Allah da Manzonsa, to ba zai zauna hakanan ba sai ka ga ya rike wata koyarwar da za ta cutar da shi, kuma ba za ta amfane shi da komai ba. Kamar yadda Hausawa suke cewa, wanda ya ki sharar masallaci, to ya yi ta kasuwa.
6. Yana daga cikin manya-manyan barnace-barnace da shaidanu suke kokarin bazawa a cikin al'umma, shi ne mace-macen aure. Shi ya sa Annabi () ya fada mana cewa: "Shaidan yakan dora kujerarsa a kan ruwa ya zauna, ya aika mayakansa. To duk wanda ya fi fitina daga cikin sojojinsa, shi ya fi matsayi a wurinsa. Daya daga cikinsu zai zo ga Iblis ya ba shi labarin irin barnar da ya yi a ranar, sai Iblis ya ce, ai bai yi komai ba. Sai kuma wani ya dawo ya ce, bai rabu da wani magidanci ba, har sai da ya ga ya raba shi da matarsa. Sai Iblis ya janyo shi kusa da shi ya ce: "Madalla da irinka." [Muslim #2813].
7. Duk mutumin da yake aiki da iliminsa, shi ne wanda yake guje wa abin da zai cutar da shi. Yayin da Yahudawa suka bar aiki da iliminsu, sai suka fada cikin abin da ya cutar da su duniya da lahira.
(Fassara da tafsiri da bayani daga Prof. Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo (OON), a cikin littafinsa "Fassarar Ma'anonin Alƙur'ani mai girma da bayanin shiriyarsa").
A lura, ni Bashir Halilu ban yi ƙari ko ragi ko gyara wani abu ba daga yadda ya ke a littafin Mallam, na kwafo ne ba tare da editing ba.
Daga shafin Dr. Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment