ASSIHRUL JUNUN السحر الجنون. ASIRIN HAUKATAR DA MUTUM KO RUƊAR DA HANKALIN MUTUM. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Siḥrul Junūn yana nufin sihirin da ake yin sa don saka mutum hauka ko rikicewar hankali ko ruɗewar tunani.
Ibnu Kasir ya kawo a cikin tafsirin suratul jinni cewa, Ibnu Abi Hatim ya ruwaito daga, Ikrimah ya ce:
“Aljanu sun kasance suna tsoron mutane kamar yadda mutane suke tsoronsu a yanzu, ko ma fiye da haka.To idan mutane su ka sauka a wani kwari, aljanu su kan gudu. Sai shugaban mutanen ya ce: ‘Muna neman kariya daga wajen shugaban aljanun wannan kwari.’
Sai aljanun su ka ce: ‘Ashe su ma suna tsoronmu kamar yadda mu ma muke tsoronsu.’
Sai aljanun suka matso kusa da mutane, suka dinga jawo musu rikicewar hankali da ciwon hauka.”
Tafsīrin Ibnu Kathīr, ƙarƙashin Suratul Jinn, aya ta 6.
Akwai kuma wata ruwayar da ta fito kai tsaye daga Ibn Abbas (R.A.) game da ayar, inda ya ce mutanen zamanin jahiliyya sukan kwana a kwari, sai su ce
: «أَعُوذُ بِعَزِيزِ هَذَا الْوَادِي» —
“Ina neman kariya ga mai girman wannan kwari.” An kawo ta a Tafsīrin Ɗabari, ƙarƙashin Suratul Jinn, aya ta 6.
Wannan ya tabbatar da cewa lallai Aljanu kan iya shafar mutane su saka musu ciwon hauka ko rikicewar tunni.
Sannan Hadisin Khārijah ibnis Ṣalt رضي الله عنه
An ruwaito daga Khārijah ibnis Ṣalt, daga baffansa, cewa:
Ya wuce ta wajen wasu mutane, sai suka zo wajensa suka ce:
“Ka zo daga wajen wannan mutumin (Annabi ﷺ) da alheri. Ka yi wa wannan mutumin ruƙiyya.”
Sai su ka kawo masa wani mutum mai matsalar hankali, an ɗaure shi da sarƙoƙi. Sai ya yi masa ruƙiyya da Ummul Qur’ani (Suratul Fātiha) tsawon kwanaki uku, safe da yamma.
Duk lokacin da ya kammala karanta ta, sai ya tara yawu a bakinsa, sannan ya tofa masa a hankali. Sai mutumin ya warke kamar an warware masa ɗaurin da aka ɗaure shi da shi.
Sai su ka ba shi wani abu a matsayin lada. Daga nan ya je wajen Annabi ﷺ ya ba shi labarin abin da ya faru.
Sai Annabi ﷺ ya ce:
“Ka karɓa, ka ci. Na rantse da raina, lallai wanda ya ci lada ta hanyar ruƙiyyar ƙarya ya yi abin da bai dace ba, amma kai ka samu lada ta hanyar ruƙiyya ta gaskiya.”
Duba littafin Sunan Abī Dāwūd da Musnad Aḥmad kuma Shaykh Al-Albānī ya inganta shi.
Hadisin ya tabbatar da cewa mutumin yana da matsalar hauka ne, duk da bai ce asiri aka yi masa ko ba asiri ba amma ya tabbatar da cewa ana yi wa mai matsalar hauka rukiyyah har ma ya samu lafiya.
Sheikh Wahid Baliy ya kawo bayanin irin wannan nau'in sihiri cikin littfinsa 'Assarimul battar..'
A bayanin Waḥīd Bālī, ya ce ana samun Aljani da ake ɗora wa aikin sihiri, wanda ya ke shafar tunani, ƙwaƙwalwa da nutsuwar mutum.
YADDA AKE GANE CEWA AN YI WA MUTUM ASIRIN HAUKATARWA.
1. Yawan shagala da tunani (الشرود).
Wato kullum mutum ya kasance cikin tunani mara anfani ba tare da iya aiki mai ma'ana ba.
2. Yawan rikicewa ko dimuwa (الذهول).
Da zarar mutum ya fara wani abu mai amfani sai lissafi ya rikice masa, ya rasa abinda ya kamata ya yi, ko yawan rikicewa akan abinda ya sani ko ya iya.
3. Tsananin mantuwa (النسيان الشديد).
Wacce ta kan kai mutum ya iya manta ƴan uwansa ko ƴaƴansa ko mutum ya manta hanyar gidansa. Ko mantuwa nan take akan abinda bai jima da faruwa ba ko wanda yake cikin faruwa.
4. Magana mara tsari (التخبط في الكلام).
Wato maganganu barkatai, kamar ana hira da mutum sai ka ji ya kawo wani zance wanda ba shi da muhalli ko kuma zuba zantuttuka marasa fa'ida.
5. Kallon wuri ba tare da natsuwa ba (التَّحْدِيقُ).
6. Idanu suna yawo ba tare da daidaito ba (اِضْطِرَابُ حَرَكَاتِ الْعَيْنَيْنِ).
7. Rashin iya zama wuri guda da yawan yawo ba tare da manufa ba (عَدَمُ الِاسْتِقْرَارِ وَكَثْرَةُ التَّجَوُّلِ).
8. Rashin iya ci gaba da aiki guda (تَشَتُّتُ الِانْتِبَاهِ).
9. Rashin kula da tsaftar jiki da kayan sakawa ko wajen zama, da son kusantar wajen ƙazanta (إِهْمَالُ النَّظَافَةِ الشَّخْصِيَّةِ).
10. Yawan fusata da jin haushin mutane da tsanarsu ba tare da dalili ba (سُرْعَةُ الْغَضَبِ وَالْعَدَاوَةِ).
11. Yawan zargin mutane da ƙin amincewa da ’yan uwa ko iyali da ɗaukarsu a matsayin maƙiya ba tare da dalili ba (سُوءُ الظَّنِّ وَالشَّكُّ فِي الْأَهْلِ وَالْأَقَارِبِ).
Waɗannan su ne alamomin da aka kawo a bayanin wannan nau'i a wasu littattafan ruƙiyya.
Amma yana da kyau alura, waɗannan alamomi ba sa tabbatar da cewa lallai sihiri ne a jikin mutum, saboda cututtukan tunani ko na kwakwalwa na iya haifar da irin su, don haka yana da kyau in mutum ya samu matsalar ya zama ana binciken lafiyarsa a asibitin don gano ko ba laurar sihiri ko Aljanu ba ce.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment