ASIRIN MALLAKA

ASIRIN MALLAKA     السحر المحبة
=========================
Sihirin Soyayya da yadda ake 6ata shi

.
.

Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruqiyyah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08134434846, 08162600700.
.

أعوذ بالله من الشيطان الرجيم
بسم الله الرحمن الرحيم
صلى الله على النبي الكريم

Sihirin Mallaka ko Sihirin Hada Soyayya, a Larabce ana kiransa da Sihrul Mahabbah السحر المحبة
ko a ce Sihrut Tiwalah
السحر التولة.

Wannan nau'in Sihiri, ana yinsa ne don wani mutum ya mallaki zuciyar wani mutum, ta yadda zai dinga sa shi ya aikata masa duk abinda yake so.

Wannan nau'in Sihiri sananne ne kuma shahararre wanda ya yadu a tsakanin mutane.

Mafi yawa Sihrul Mahabbah ana yin sa ne ta hanyar Sihrul Ma'akuwli wanda mukay bayaninsa jiya.
.
.
HANYOYIN DA BOKAYE SUKE BI DOMIN YIN SIHRUL MAHABBAH.

1- Idan mace tana so ta mallake zuciyar mijinta, ta dinga juyashi yadda take so. Bokan zai iya cewa ta kawo jinin hailarta, ya rubuta ayoyin Alqur'ani da shi. Sai ya wanke ya bata ta zubawa mijinta a abinci. Ko kuma ya bata Rubutun Qur'ani ya ce ta wanke gabanta da shi, indai mijinta ya sadu da ita to Sihirin ya kama shi. Da dai makamantansu.

Wannan hanya ana kiranta Tariyqatun Najasati طريقة النجاسة.
.

2- Idan mutum yana so ya mallaki zuciyar mutane, kamar mai neman farin jinin shugabanci ko kasuwanci da dai suransu. Bokayen sukan iya sa shi ya siyo wata dabba ya yanka a wani lokaci sananne sannan su hada masa magani ya dinga wanka da jinin. Wannnan hanya ana kiranta Tariyqatuz Zab'hi طريقة الذبح.
.
3- Akwai wadanda suke rubuta wasu ayoyi na Alqur'ani, sai a bude wasu haruffan daga ciki, misali harafin 'ة' ko 'م', sai a buda shi yay qato sosai. Sai a rubuta sunan wanda ake so a mallaka a ciki.

Wasu kuma suna ra6a sunan wanda ake so a mallaka ne a karshen kowace aya ko ay hatimi da ayar sannan a rubuta sunan mutum a ciki, sai a baiwa wanda yake so ya mallake shi ya shanye rubutun ko yay wanka da shi. Wannan hanyar sihiri ita ake kira Tariyqatul Tankiysi طريقة التنكيس.
.
4- In za ay Sihrul Mahabba dai, wani Matsafin yana cewa a kawo masa wani 6angare na tufafin wanda za ay wa sihirin, kamar rigarsa ko gashin wani 6angare na jikinsa ko kudinsa ko kuma dukkan wani abu da ya je hannunsa. Sai Bokan ya kar6a ya hada wasu abubuwa ya tsafe mutum da su. Wannan hanya ana ce nata Tariyqatul Asari طريقة الأثر.
.
4- Wasu sukan baiwa mutum wani ruwan rubutu ko ruwan magani, sai su ce ya bari sai wata ya fito ya yi haske sosai, sai ya fito cikin hasken watan yay wanka da shi. Wannan ita ce Tariyqatut Tanjiymi طريقة التنجيم.
.
5- Wani Bokan ya kan hada wasu turaruka na sihiri yay musu karance-karance. Sai ya baiwa mace ya ce ta shafa a jikinta, indai mijinta ya ji kamshin to shikenan ta mallakeshi. Ko kuma yace tay masa turaren hayaqi a dakinsa. Haka ma maza masu son duniya, Bokaye suna ba su irin wannan sihrin.
Wannan hanya ana ce mata Tariyqatut Tabakhkhur طريقة التبخر.
.
Hanyoyin suna da yawa sosai, wadansu ma ba su da dadin fada.
.
.
YADDA MUTUM ZAI GANE AN YI MASA SIHRUL MAHABBAH, WATO SIHRIN SOYAYYA

1- Soyayya mara misaltuwa, mara iyaka akan mutum  kuma kullum soyayyar karuwa take, tare da cewa ba wani dalili da yasa kake kaunar mutum. Ma'ana shi ba kyautata maka yake ba kuma ba wani halin kirki ne da shi ba wanda yasa kake kaunarsa.
.
2- Idan namiji ne, akoda yaushe zai ji ba shi da bukata kamar yay jima'i da matar. Haka ma in mace ce, zata ji kullum tana so tay jima'i da wanda ya mallaketa, ko da ba mijinta bane.
.
3- Mutum zai ji ba ya iya hakuri akan matar, zai iyay mata kuka ko ya bata duk abinda ta nema akan tay masa abinda yake so.
.
4- A duk lokacin da ka ga wanda ya mallakeka sai gabanka ya fadi kuma ka dimauce, yay maka kwarjini, ya zamto ba wanda kake fuskanta sai shi.
.
5- Makauniyar biyayya. Wanda akaywa Sihrul Mahabbah yanay wa wanda ya mallake shi makauniyar biyayya. Zai iya yi masa kome ya nema, koda kuwa ya sa6awa Allah ko kuma zai 6ata da iyayensa ko yan uwansa.
.
6- Rashin ganin laifin mutum da goyon bayansa akan rashin gaskiya kuma duk wanda ya ke aibata shi zaka ji ka tsane shi, koda gaskiya yake fada.
.
7- Indai soyayyar da kakewa mutum ta Sihiri ce, to watarana hankalinka zai dawo jikinka, ka gane cewa lallai soyayyarku da wane akwai matsala kuma za kay tunanin ba shi da gaskiya akan abubuwa dayawa da ka goyi bayansa amma kuma za ka kasa yi masa magana ko nuna masa kuskurensa.
.
8- Yawan ganin mutum a mafarki, wani lokacin saikai mafarkinsa sau uku ko sama da haka a rana daya.
.
9- Za ka iya ganin wani mutum wanda baka san shi ba, yana gaya maka cewa in kana so ka samu nasara a rayuwarka sai kai wa wane biyayya.
.
10- Yawan rashin lafiya, kamar ciwon kai in baka ga mutum ba, ba kuma wani abun kirki mutumin zai ma ka in ka gan shi ba.
.
11- Wanda yay maka Sihrul Mahabbah za ka ga yana ba ka umarni na kai tsaye bisa gadara, irin umarnin da bai kai matsayin da zai ba ka shi ba. Zai dinga neman abubuwa a wajenka wadanda ba hakkinsa ba sannan za ka ji duk ba ka damuwa da hakan, koda ka damu kuma sai kai masa abinda ya nema.
.
.
MATSALOLIN DA AKE ASAMU IDAN AKAYWA MUTUM SIHRUL MAHABBAH

Shi wannan nau'in Sihiri yana da 6angarori guda biyu ne, 6angare na farko zai raba mutum da duk wani wanda yake alaqa da su, ya zamto ba ya ganin mutuncinsu ba ya jin maganarsu har iyayensa da 'yan uwansa. Bangaren Sihirin na biyu kuma zai sa mutum ya kaunaci wanda yay masa Sihirin ya zamto ba ya ganin kimar kowa sai shi.
.
To akan samu matsala

1- Zai iya yiwuwa 6angaren sihirin na farko yay aiki amma 6angare na biyu bai tasiri ba. Sai ya zamto mutum baya ganin mutuncin kowa, ya zama duk ya tsani mutane. Sai ya zamto har wanda yay masa sihirin ya tsane shi,  bai kaunace shi ba.

Akwai wata mata da taywa mijinta irin wannan sihrin, karshe mijin ya saki ragowar matansa, ya rabu da ÿaÿansa da iyayensa, a karshe itama ya sake ta. Da ta koma wajen Bokan da yay mata asirin don ya karya sai ta tarar Bokan ya mutu.
.
2- Wannan Sihiri yana iya sa wanda akaywa rashin lafiya, kamar Ciwon zuciya da Hawan jini da ciwon Kai da dai sauransu. Ta na iya kai mutm ma ga haukacewa.
.
3- Tana iya yiwuwa lokacin da mutum yake rashin lafiyar ya dinga ambaton sunan wanda yay masa sihirin yana cewa ga shi nan yana zuwa wajensa, amma wani lokacin Shaidanu suna yin hakadon su hada fitina.
.
.
ABUBUWAN DA SUKE SA WA AY SIHRUL MAHABBAH

1- Yawan fada tsakanin miji da mata, yana sawa wata matar tay tunanin mallakar mijinta don a zauna lafiya, ko kuma shi mijin yay tunanin mallakarta.
.
2-Akwai mata kwadayayyu, masu son mallake mazajensu don su mallake dukiyar mijin.
.
3- Wata matar tana yi ne don kada mijinta yay mata kishiya.
.
4- Wasu mazan Azzalumai ne, kwata-kwata ba su san haqqin matansu ba, ba sa fita haqqinsu na ciyarwa da shayarwa da tufatarwa, tun matar tana haquri har karshe ta fara tunanin fadawa cikin bokaye da harkar tsafi.
Don haka duk mai so kada matarsa bokaye su dinga zina da ita ko su dinga bata guba tana zuba masa a abinci, to ya dinga ba ta haqqinta da Allah Ya dora masa.
.
5- Akwai wanda zai ga yarinya yana son ta, ita kuma ba ta son sa, sai yay mata sihiri ya aureta. Saidai irin wannan sihrin yana da saurin karyewa kuma mummunar kiyayya yake zama.
.
6- Ana iya yi wa mutum wannan Sihri don a damfari dukiyarsa, kamar abokan kasuwanci da dai sauransu.
.
7- Wasu kuma suna yi ne don a dora mutum akan wata hanya mara kyau, kamar idan ana so a saka shi a wata kungiya ta azzalumai.
.
Da dai dalilai da yawa.
.
.
YADDA AKE LALATA SIHRUL MAHABBAH

A karantawa mara lafiyar wannan Ayah

: ﴿ ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺇِﻥَّ ﻣِﻦْ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻭْﻟَﺎﺩِﻛُﻢْ ﻋَﺪُﻭًّﺍ ﻟَﻜُﻢْ ﻓَﺎﺣْﺬَﺭُﻭﻫُﻢْ ﻭَﺇِﻥْ ﺗَﻌْﻔُﻮﺍ ﻭَﺗَﺼْﻔَﺤُﻮﺍ ﻭَﺗَﻐْﻔِﺮُﻭﺍ ﻓَﺈِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻏَﻔُﻮﺭٌ ﺭَﺣِﻴﻢٌ * ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺃَﻣْﻮَﺍﻟُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻭْﻟَﺎﺩُﻛُﻢْ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋِﻨْﺪَﻩُ ﺃَﺟْﺮٌ ﻋَﻈِﻴﻢٌ * ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣَﺎ ﺍﺳْﺘَﻄَﻌْﺘُﻢْ ﻭَﺍﺳْﻤَﻌُﻮﺍ ﻭَﺃَﻃِﻴﻌُﻮﺍ ﻭَﺃَﻧْﻔِﻘُﻮﺍ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻟِﺄَﻧْﻔُﺴِﻜُﻢْ ﻭَﻣَﻦْ ﻳُﻮﻕَ ﺷُﺢَّ ﻧَﻔْﺴِﻪِ ﻓَﺄُﻭﻟَﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ ﴾ ‏[ ﺍﻟﺘﻐﺎﺑﻦ : 14 - 16 ‏] .

.
.

2- A irin wannan lalurar Aljani ba bayyana yake yayin Ruqiyyah ba, sedai mutum yay amai, ko ya ji 6acin rai ya cika masa qirjinsa, ko ya kama karkawa, ko kuma sauran alamomi da mukay bayani a cikin ASSIHRUL MA'AKUL.

I dan kaga haka sai ka karantawa mutum ayoyin Ruqiyya a ruwa ka ba shi ya sha a gabanka. Idan yay baqin amai ko ja ko yalo, to sihrin ya 6aci kenan.
Idan kuma bai amai ba, to sai ka hada masa ruwan Rukiyyah ya dinga sha har tsawon sati uku insha Allahu Sihrin zai karye.

Wadannan su ne Ayoyin da za ka karanta

﴿ ﻗَﺎﻝَ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻣَﺎ ﺟِﺌْﺘُﻢْ ﺑِﻪِ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﺳَﻴُﺒْﻄِﻠُﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻟَﺎ ﻳُﺼْﻠِﺢُ ﻋَﻤَﻞَ ﺍﻟْﻤُﻔْﺴِﺪِﻳﻦَ * ﻭَﻳُﺤِﻖُّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﺤَﻖَّ ﺑِﻜَﻠِﻤَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺮِﻩَ ﺍﻟْﻤُﺠْﺮِﻣُﻮﻥَ ﴾ ‏[ ﻳﻮﻧﺲ : 81 ، 82 ‏] .

﴿ ﻭَﺃَﻭْﺣَﻴْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻰ ﻣُﻮﺳَﻰ ﺃَﻥْ ﺃَﻟْﻖِ ﻋَﺼَﺎﻙَ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻫِﻲَ ﺗَﻠْﻘَﻒُ ﻣَﺎ ﻳَﺄْﻓِﻜُﻮﻥَ * ﻓَﻮَﻗَﻊَ ﺍﻟْﺤَﻖُّ ﻭَﺑَﻄَﻞَ ﻣَﺎ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻤَﻠُﻮﻥَ * ﻓَﻐُﻠِﺒُﻮﺍ ﻫُﻨَﺎﻟِﻚَ ﻭَﺍﻧْﻘَﻠَﺒُﻮﺍ ﺻَﺎﻏِﺮِﻳﻦَ * ﻭَﺃُﻟْﻘِﻲَ ﺍﻟﺴَّﺤَﺮَﺓُ ﺳَﺎﺟِﺪِﻳﻦَ * ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺁﻣَﻨَّﺎ ﺑِﺮَﺏِّ ﺍﻟْﻌَﺎﻟَﻤِﻴﻦَ * ﺭَﺏِّ ﻣُﻮﺳَﻰ ﻭَﻫَﺎﺭُﻭﻥَ ﴾ ‏[ ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ : 117 ، 122 ‏] .

﴿ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺻَﻨَﻌُﻮﺍ ﻛَﻴْﺪُ ﺳَﺎﺣِﺮٍ ﻭَﻟَﺎ ﻳُﻔْﻠِﺢُ ﺍﻟﺴَّﺎﺣِﺮُ ﺣَﻴْﺚُ ﺃَﺗَﻰ ﴾ ‏[ ﻃﻪ : 69 ‏] .

ﺁﻳﺔ ﺍﻟﻜﺮﺳﻲ ‏[ 5 ‏].
Daga Shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.

https://plus.google.com/103289796355839003804/posts/Xp8pzriNSRr
.
WhatsApp & call 08134434846, 08162600700

Comments

Popular Posts