SIHIRIN RABA KAUNA. ASIRIN RABA SOYAYYA

SIHIRIN RABA QAUNA
==================
السحر التفريق
.

Sihirin da ake yi domin raba masoyi da masoyinsa.
.
.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islmiyyah, masu yin ruq'yah da harhada magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
.
.
Wannan nau'in Sihiri a Larabce ana kiransa da suna "Sihrut Tafriyq السحر التفريق"
Wato sihirn raba kauna da yaren Hausa. Ana kuma kiransa da "Firaqu" ko kuma "Farraqu".
.
Wannan nau'in sihiri dadaddene sosai a duniya kuma  ya yadu a tsakanin mutane, inda yawancin bokaye wannan nau'in sihiri shi su ka fi alfahari da shi wajen iya aiki sannan Sihrul Mahabba wato sihirin hada soyayya wanda mukay bayaninsa kwanakin baya.
.
Sihrut Tafriyq wato sihirin raba kauna, ana yinsa ne domin raba tsakanin masoyi da masoyinsa, a saka gaba da kiyayya a tsakaninsu, ta yadda dayan zai dinga jin cewa zai iya kashe dayan ko yay sanadin ajalinsa.
Duk irin soyayyar da mutum yakewa dan uwansa da kaunar da take tsakaninsu, to matukar akay musu sihrut tafriyq wato sihirin raba kauna, indai yay tasiri a tsakaninsu to lallai gaba da kiyayya za ta kullu a tsakaninsu kuma za su rabu da junansu.
.
Allah Madaukakin Sarki Ya yi magana akan wannan nau'in Sihiri a Alqur'ani kuma shi ne nau'in Sihiri da Allah Madaukakun Sarki ya fara magana a kansa, a cikin suratul Baqarah, ayah ta 102.
.

ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰٰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ۖ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَٰﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧْﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ۚ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰٰ ﻳَﻘُﻮﻟَﺎ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ۖ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ۚ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻀَﺎﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻟَّﺎ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ۚ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﻨْﻔَﻌُﻬُﻢْ ۚ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍ ﻟَﻤَﻦِ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻠَﺎﻕٍ ۚ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ ﺷَﺮَﻭْﺍ ﺑِﻪِ ﺃَﻧْﻔُﺴَﻬُﻢْ ۚ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ
102 ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ.
.
.
NAU'O'IN SIHRUT TAFRIYQ
.
Wannan nau'in sihiri na raba kauna, ba kawai ana yinsa ne tskanin ma'aurata ba, sedai wanda ake yi a tsakanin ma'aurata shi ya fi tasiri da kuma yaduwa a tsakanin al'umma saboda mugun kishi da mata suke da shi.
.
Amma daga cikin nau'o'insa akwai

1) Raba kauna tsakanin 'yan uwa. Wa da qani ko kuma ya da qanwa. Mafi yawa wannan sihiri ana yinsa domin a hada gaba a tsakanin yan uwa ta yadda ba za su hada kansu ba ballantana su iya morawa kan su wani abin alkhairi. Galibi ana yinsa idan ana yiwa mahaifinsu hassadar da Allah Yay masa ta samun yaya, don haka sai a raba masa kansu. Wani lokacin kuma mata ne sukeyi domin su raba kan yayan abokiyar zamansu.
.
Na san wasu yan uwa da akay musu irin wannan asirin kuma dukkansu dattawa ne, babban ya kai shekara sittin, karamin kuma ya kai arba'in da wani abu. Karamin yake ba ni labari, ya ce Sun ta6a haduwa a makabarta, sun je kaiwa kabarin mahaifinsu ziyara amma a makabartar ba wanda yay wa wani maganaa gaban kabarin mahaifinsu, saboda tsabar gaba. Sedai daga baya Allah Ya taimakesu sun shirya kafin babban ya rasu kuma Aljanin da aka hada abin da shi a gabana ya zo ya ba shi hakuri amma lokacin karamin ne kawai yake da rai.
.

2)Raba kauna tsakanin mutum da iyayensa. Kamar mutum da mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko kuma mace da mahaifinta ko mahaifiyarta.

An fi yin wannan sihiri tsakanin namiji da iyayensa, sa6anin mace da iyayenta, duk da dai shi ma ana samu.

Wannan nau'in sihiri akan yi ne idan an ga Allah Ya yiwa yarin arziki, sai a hada shi gaba da iyayensa ta yadda ba zai dinga taimaka musu ba.

Wani lokaci kuma mata ne suke yiwa mazajensu, ta yadda zai zama su kadaine suke iya juya mai gidan, yadda ko iyayensa zai zama ba ya jin maganarsu ba ya tausaya musu sai abinda matarsa ta ce.

Akan samu mutum ya daina zuwa wajen iyayensa, ya daina taimaka musu kuma ba ya sauraronsu. Sai ka ga mutum ya yi shekara guda ba ya yiwa mahaifiyarsa magana kuma suna gida daya. Ko ka samu in yaga mahaifinsa sai ya canja hanya.

Nau'i na biyu na wannan sihiri kuma shi ne a samu su mahaifan ne suke gaba da dan nasu. Sedai shi ma an fi samu mahaifin yana gaba da yayansa amma ta 6angaren mahaifiya bai fiye tasiri ba.

Za ka samu mutum ya tsani yayansa, ba ya son ganinsu, ba ya daukar nauyinsu, ba ya sauraron matsalarsu, har wani lokaci ma ya dinga inkarin kasancewarsu yayansa amma dai a zuciyarsa ya san tabbas yayansa ne, sedai ya dinga fada saboda tasananin yadda yake ji ba ya kaunarsu.

Shi ma irin wannan sihiri mafi yawanci mata ne suke aikatawa abokan zamansu.
.
.
3)Raba kauna tsakanin aboki da abokinsa. Sawa'un abokin kasuwanci ne ko abokin karatu ko kuma abokin sauran harkoki.

Shi kuma wannan sihiri ana yinsa ne domin a raba kauna tsakanin mutum da abokan cinikinsa wato 'customers'.

Kuna harkokin ciniki da mutum lafiya lau, sai ka ga ya daina zuwa wajenka, ko kuma duk wanda kuka kulla wata harka da shi sai ya dawo ya ce ya fasa ko kuma wadanda suke ba ka kaya haka kawai sai su daina.

Shi wannan nau'in sihiri mafi yawa abokan kasuwanci ne suke yiwa mutum saboda hassada.

Ana kuma yinsa domin a raba mutum da abokan huldarsa na karatu. Sedai wani lokaci wasu iyayen da kansu suke sa wa ay wa yayansu saboda a raba su da abokan banza da suke yawo da su.
.
.
4) Raba kauna tsakanin miji da mata. Wannan shahararrene kuma sananne a tsakanin mutane.
.
Amma mata ku ji tsoron Allah, saboda yawancin asiri mata ne suke biyan bokaye kudi suna aikatawa sedai kuma maza ku ji tsoron Allah saboda yawancin bokaye maza ne, matan kadan ne sosai.
bashirhalilu.xtgem.com

ALAMOMIN SIHIRIN RABA KAUNA
.
Yadda za ka gane an yi maka Sihirin raba kauna tsakaninka da wani.

1)Jin kiyayyar mutum a zuciyarka ba tare da ya  aikata maka wani laifi ba, alhali kuma da kana kaunarsa. Ko kuma shi kaga ya juya maka baya yana kinka ba gaira da dalili.
.
2)Za ka ji koda yaushe kana so ka nisanci inda mutum yake. Saboda duk lokacin da ku ka hadu da wanda aka raba ku da shi ta hanyar sihiri, kuna haduwa sai kanka ya kama ciwo ko gabanka ya dinga faduwa ko kuma ka ji ka rikirkice. Idan kuma abin ya fi tasiri a jikin dayan to shi ne hakan za ta dinga faruwa da shi.
.
3) Yawan samun rikici da mutum.

A mafi yawan lokuta kuma karamin abu ne yake hada fadan amma sai kowa ya dauki abin da zafi, maganar tayta dagulewa.
.
4) Ganin mutum a wata mummunar siffa. Idan akay muku sihirin raba kauna tsakaninka da wani to a duk lokacinda ka kusanto shi sai ya dinga ganinka kamar wani dodo ko kamar wata dabba. Wata matar idan mijinta zai kusanceta sai ta ga ya zama kare ko kansa ya koma kan jaki. Shi ma namijin wani lokaci sai ya ga ta koma siffar wata dabba.
.
5) Jin wari mara dadi a tare da mutum.

Misali, idan akaywa budurwa irin wannan sihirin, to duk namijin da ya zo wajenta da niyyar aure sai ya ji tana warin ja6a ko ya ji doyi yana tashi daga jikinta ko bakinta.
.
Wani mutum ya ta6a zuwa wajena da matarsa akan ba ta yadda da shi a wajen kwanciya. Sai na tambayeta, sai ta ce idan ya zo wajenta sai ta ji bakinsa yana wari kuma duk jikinsa doyi yake sannan wani lokaci sai ta gan shi kamar wani dodo ko mahaukaci, ga shi wani lokacin yana hantararta.

Da na tambayeshi mai yasa yake hantararta?!, sai ya ce gaskiya shi ma wani lokaci sai ya ji tana wari kamar ba ta wanka, shi in ya kalleta ma zuciyarsa ta ke.
.
Irin wannan matsalar ta ma'aurata mun ganta ba iyaka. Amma cikin ikon Allah idan aka warware sihirin shikenan sai su zauna lafiya.
.
Alamomin wannan sihiri suna da yawa, sun kai guda hamsin amma za mu takaita a guda biyar saboda kada rubutun yay yawa. Yanzu za mu kawo muku
.
.
YADDA AKE WARWARE SIHRUT TAFRIQ
.
Na farko dai yana da kyau ka nemi shawarar Malamai masana harkar magunguna da Ruqiyyah idan kana zaton an yi maka ko an yi miki sihirin raba kauna da ma kowane irin sihiri.

Yana da kyau ka samu Malami masani Ahlisunnah, ko da dai acikin masu kiran kansu Ahlissunnan ma akwai wadanda ba su yarda ana iya yiwa mutum sihri ko kuma Aljanu suna shiga jikin mutumba. Sedai tunaninsu 6ataccene, domin kuwa Allah Ya yi bayanin sihiri a Alqur'ani, Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
ya yi bayani, tare da maganganun Sahabbai da manyan Malaman Sunnah magabata.

A shafinmu na Tarbiyyah Islamiyyah mun kawo cikakken bayani akan haka, acikin rubutun da mu kay mai taken "YADDA AKA YI WA MANZON ALLAH
صلى الله عليه وسلم
SIHIRI"
da kuma rubutunmu mai taken "ASALIN TSAFI".

Don haka yana da kyau ka samu Malami wanda yake da ilimi akan harkar magungunan musulunci.

Domin ana samun matsala, idan mutum yana zargin an yi masa sihiri ko Aljanu sun shafe shi, sai ya bugawa wani Malami da yake jinsa a rediyo waya, yana ganin ya samu babban Malami, shi kuma sai ya ce masa karya ne ba wani asiri. Sai kaga mutum ya ci gaba da zama a cikin wahala da azabar sihiri ko Aljanu amma wani Malami ya ce masa ba shi da matsala sannan kuma bai ba shi wata mafitar ba.

Wallahu a'alamu alaiHit taklan.
.
YADDA MAI RUQIYYAH ZAI WARWARE SIHRUT TAFRIYQ
.
1) Na farko dai ka bukaci su ma'auratan su zo tare, saboda kowa yay bayani a gaban dan uwansa. Wani lokaci daga bayanin ma sihirin yake warwarewa, domin idan kowa yay bayani kai kuma zaka tabbatar musu da cewa sihiri ne a tsakaninsu.

Wasu Aljanun idan suka ji an tona musu asiri shikenan sai su gudu, wasu kuma sai su bige daya su fadi suna kuka suna ba da hakuri.
.
2) Ka yi wa ma'auratan nasiha akan su dogara ga Allah kuma su cire tsoro daga zuciyarsu sannan su daina daukarwa kansu hukunci lokacin fushi.
.
4)Idan wanda akaywa sihirin an yi masa ne akan abokan cinkinsa, ko akan mahaifansa, ko kuma ba zai yiwu su zo tare ba, to sai a aiwatar masa da Ruqiyyah shi kadai sannan a ba shi shawarwari, a ba shi magunguna.
.
.
5) Ka karantawa mai matsalar Ruqiyyah cikakkiya. A wannan nau'in sihiri, dayan uku zai fatu yayin aiwatar da Tuqiyyar:, kodai Aljanin ya buge mutum yay magana da bakinsa ko kuma mutum ya fita daga hayyacinsa ba tare da Aljanin ya buge shi ba kokuma ka ga ba abinda ya canja a tare da mutum. Daga nan sai a samu Za'afaran a karanta

i) Ayah ta 102, cikin suratul Baqarah

ii) Ayatal Kursiyyu da Ayoyi biyu da suke bayanta.

iii) Ayoyin karshe na Suratul Baqarah (Amanar Rasuwlu).

iv) Ayoyin 6ata Sihiri.

v) Suratul Kafirun (Qul yaa).

vii) Suratul Falaq.

vii) Suratun Nas.

Sai mai larurar ya dinga zuba wannan Za'afaran din a ruwa yana sha, ya zama wannan shi ne ruwan shansa. Sedai zai fi kyau a samu ciyawar Za'afaran din a jikata a ruwa, sai a dinga tofa ayoyin a ciki.
.
A sake karanta wadannan ayoyi gaba dayansu a cikin man Zaitun, sai a baiwa mai lalurar ya dinga shafe jikinsa da shi kullum sau daya.
.
A samu ruwa acikin kwarya ko kuma kowane irin mazubi, sai a zuba ganyen magarya guda bakwai a ciki, zuba kanwa da gishiri kadan-kadan a ciki, sai mai lalurar ya saka hannuwansa a cikin ruwan. A tofa Ayoyin karya sihiri a ciki da Ayatush shifa'i. Sai mutum ya dinga kara ruwa yana sha kadan-kadan.
.
Sannan mutum ya dinga yawan karanta
وقل رب أعوذ بك من همزات الشياطين، وأعوذ بك رب أن يحضرون
Wato "Wa qur Rabbi a'uzu biKa min hamazatish shayatiyn, wa a'uwzu biKa Rabbi an yahburuwni"

da suratul Falaqi da Nasi.
.
Yana da kyau kuma mutum ya dinga yawan karanta Suratul Baqarah ko ya dinga kunnawa a kaset yana saurara.
.
Allah Ya shiryar da mu, Ya raba mu da sharrin masu sihiri.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
.
Face book
https://m.facebook.com/Sunnah-Medicine-1354761231309468/
.
Blog
bashirhalilu.xtgem.com

magunguna.wordpress.com
.
Email
bashirhalilu1989@gmail.com
.
WhatsApp
https://chat.whatsapp.com/GMZnAyhTm4C4afsZ5jZIXJ
.
Messanger
http://m.me/tarbiyyah.islamiyyah.3
.
Phone number 08162600700 , 08134434846

Comments

Post a Comment

Popular Posts