ASIRIN HAUKA. Asirin da aka yiwa mutum don a Haukata shi
ALAMOMIN SIHIRIN HAUKA
========================
.
Sihirin da aka yiwa mutum don a Haukata ta shi.
.
.
أعوذ بالله من الشيطان الرجيم
بسم الله الرحمن الرحيم
.
.
Kamar yadda mu ka sha bayani a baya cewa mutane (bokaye) su kan hada ba ki da Aljani su tura shi jikin wani mutum ko wata mata don su cutar da su. Wato Asiri kenan ko Sammu.
.
A baya na yi bayanin nau‘in wasu cututtuka da Shaidanun Aljanu ke sakawa mutane
Yau kuma insha Allahu zan yi bayani ne a kan
Yadda mutum zai gane an yi ma sa sihirin Haukatarwa.
.
Wato an tura masa Aljani don ya raba shi da hankalinsa.
.
.
1- Kai tsaye Aljanin kan sa zai dosa ya zauna a cikin ‘kwa‘kwalwar sa, don haka zai iya sarrafa kowace ga6a ta jikin mutum yadda ya ga dama. Yadda mutum zai magana bai san yana yi ba. Ko yay tafiya bai san yana yi ba.
.
2- A zahiri sai Mutum ya ga kamar wasu mutane sun zo za su yi ma sa duka ko suna zagin sa ko kuma suna gaya ma sa wani abu; sai ka ji shi ma yana ba da amsa ko yana zage-zage.
.
3- Mutum zai ga kamar kwarkwata tana zubowa daga jikinsa ko tsutsotsi ko macizai suna hawa kansa. Sai kaga mutum yana ta karkade jikinsa.
.
4- Mutum zai dinga yawan dimuwa, da ya bar gida sai ya 6ata har sai an nemo shi. Wani ma sai yay kwanaki kafin a ganshi.
.
5-Yawan tunane-tunane marasa ma'ana. Da tunanin sa6o da shakka akan samuwar Ubangiji da makamantansu.
.
6-Tsananin shirme. Kamar kuna hira da mutum sai ka ji yana kawo wata magana wadda bata da alaqa da zancen.
.
7- Rashin zama guri daya, da yawon tsiya mara amfani.
.
8-Rashin gudanar da takamaiman aiki mai ma'ana
.
9-Rashin tsaftar jiki da ta kaya.
.
10- Son zama a inda mutane suke kauracewa, kamar duhu ko bandaki ko bola ko cikin tsakar rana.
.
11- Yin dariya ko kuka haka kawai, ko maganganu marasa kan kado.
.
12- Mutum zai ji ana kiran sa ko a ce ya yi wani aiki amma ba tare da ya ga kowa ba.
.
13- Mutum zai dinga mafarkin ana bin sa da gudu ko suna kokawa da wani.
.
14- Mutum zai dinga mafarki kamar zai fado daga wani tsauni ko zai fada cikin kogi.
.
15- yawan mafarkin wasu dabbobi kamar karnuka ko kuraye su na so su cinye ka.
.
16- Matsanancin ciwon kai da zazzarewar idanuwa su yi tulu-tulu.
.
17- Jin haushin mutane haka kawai da muguwar qullata.
.
18- ‘kin cin abinci ko ci ya shige ‘kima ga kuma tsananin rama.
.
Da dai sauran su.
.
.
Magance wanan matsala da yaddar Allah
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
.
.
-Sauraron karatun Alqur‘ani da kuma karantawa.
.
-Zama da alwala da kuma yin addu‘o‘in kanciya bacci.
.
-Shan ayoyin rukiyya a cikin zuma.
.
-shafe jiki da ayoyin Rukiyyah.
.
-Yin hayaki da ‘kwayoyin Habbatussaudaa.
.
.
-Idan kuma abin ya yi ‘karfi to sai a kai mutum wajen mai rukiyya.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah, mai rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya
.
08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment