ALJANAR JARIRAI. UMMUL ATFAL. ALJANA MAI SHIGA JIKIN KANANAN YARA
أم الأطفال UMMUL ATFAL
======================
.
.
Aljanar Jarirai.
.
Aljana mai shiga jikin Qananan yara.
. Ummul Atfaal ﺍﻡ ﺍﻻﻃﻔﺎﻝ ko kuma
Inna-Uwa a Hausance .
.Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan musulunci 08162600700.
. اعوذ بالله من الشيطان الرجيم
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ
.
.
A cigaba da kawo muku bayani akan
*Nau'ukan Aljanu da Rabe-rabensu da kuma irin
Cututtukan da suke sakawa mutane da
Magungunansu, yau insha Allahu za muy bayani ne a kan Ummul Atfaal, Aljana me shiga jikin Jarirain mutane.
.
.
.
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dare ya shiga ko kuma kun yamma ta, to ku kame kana nan "YA"YANKU, domin awannan lokacin ne shaidanu suke yaduwa amma idan aka sami kimanin awa daya to kwa iya sakin yaranku. kuma idan zaku kwanta ku rufe kofofinku, idan zaku rufe ku ambaci sunan ALLAH. domin Shaidan ba ya iya bude kofar da aka rufe ta (da sunan Allah).
Kuma ku kife qorukan ku. (jam'in QWARYA) Ku ambaci sunan ALLAH yayin da zaku kife. kuma ku rufe tukwanan ku. ku ambaci ALLAH lokacin da zaku rufe din, ko da wani abu ne ku dora akai. kuma idan zaku kwanta bacci ku kashe wuta" (Sahih Muslim)
ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ:
ﻭﺣﺪﺛﻨﻲ ﺇﺳﺤﺎﻕ ﺑﻦ ﻣﻨﺼﻮﺭ.
ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﺭﻭﺡ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺩﺓ . ﺣﺪﺛﻨﺎ
ﺍﺑﻦ ﺟﺮﻳﺞ . ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﻋﻄﺎﺀ؛ ﺃﻧﻪ
ﺳﻤﻊ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻳﻘﻮﻝ:
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ: ( ﺇﺫﺍ ﺟﻨﺢ ﺍﻟﻠﻴﻞ - ﺃﻭ
ﺃﻣﺴﻴﺘﻢ - ﻓﻜﻔﻮﺍ ﺻﺒﻴﺎﻧﻜﻢ. ﻓﺈﻥ
ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻳﻨﺘﺸﺮ ﺣﻴﻨﺌﺬ . ﻓﺈﺫﺍ
ﺫﻫﺐ ﺳﺎﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻓﺨﻠﻮﻫﻢ.
ﻭﺃﻏﻠﻘﻮﺍ ﺍﻷﺑﻮﺍﺏ . ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ
ﺍﻟﻠﻪ. ﻓﺈﻥ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻻ ﻳﻔﺘﺢ ﺑﺎﺑﺎ
ﻣﻐﻠﻘﺎ. ﻭﺃﻭﻛﻮﺍ ﻗﺮﺑﻜﻢ. ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ
ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ. ﻭﺧﻤﺮﻭﺍ ﺁﻧﻴﺘﻜﻢ.
ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ. ﻭﻟﻮ ﺃﻥ
ﺗﻌﺮﺿﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ. ﻭﺃﻃﻔﺆﺍ
ﻣﺼﺎﺑﻴﺤﻜﻢ Daga wannan hadisi za mu fahimci cewa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yana umartarmu mu kame yaran mu mu kula da su a daidai lokacinda Shaidanu suke yaduwa don kada su shafe su ABUBUWAN DA KE SAKAWA UMMUL ATFAL TA SHIGA JIKI YARA Idan na ce Ummul Atfal ina nufin nau'in Aljanun da ke shiga jikin kanan yara. Aljanun suna iya kasancewa Maza ne ko kuma mata. Amma dai mafi yawan mata ne. Shi ya sa ma ko a Hausa in Aljanu ya kama yaro se a ce INNA UWA ce a jikinsa.
To abubuwan da ke kawo wannan Aljana jikin yara suna da yawa, kamar:- 1- Gado. Idan ya kasance mahaiffiya ta yi lalurar Aljanu lokacin da take da ciki, to za ta iya haifo yaro me lalurar Aljanu. 2-Idan ya kasance gidan da suke zaune a ciki wajen zaman Aljanu ne, to za su iya shafar yaron. 3-Barin yara suna bacci ko suna yawo tsirara ba sutura a jikinsu. 4- Barin yara suna yawo da Magriba, kamar yadda ya zo a Hadisin d a muka kawo. 5- Barin yara suna wasa a guraren zaman Aljanu kamar Bandaki ko wajen shara ko bola ko kuma shuri. 6- Rashin yi wa yara addu'a yayinda za su kwanta bacci ko kuma sauran harkokin rayuwa. 7- Yi wa yara kwalliya irinta Shaidanu. Da dai sauransu. ALAMOMIN DA ZA A GANE JINNUL ATFAL YA SHAFI
YARO :-
.
.
1- Yaro ya dinga firgita shi kadai yana razana.
.
2- yaro ya rika tsalla kuka da tsakar dare kuma ya
ki jin rarrashi.
.
3-Wani lokacin kuma yakan dakile jikin yaro ya
hanashi girma, ya hanashi kuzari . Sai ka dai
kasusuwan yaro duk sun fiffito kamar ka kirga su.
.
4- Yaro ya zama ba ya dariya ko murmushi idan
an yi masa wasa.
.
5-Yaro ya dinga kallon sama shi kadai yana
dariya. Ko kaga yana kallon gefensa kamar ana
daukar hankalinsa.
.
6-Yakan sa yaro ya dinga kallon-ruwa (wato
idonsa ya wurkile). Kwayoyin idonsa su juye
.
7- Galibin yaran sukan zama masu katon kai da
siraran kafafuwa (idan abin yay karfi).
.
8- Yaro zai ta rashin lafiya, in an je Asibiti Likita ya
ce bai ga komai ba.
.
9- Wani lokaci idan Babarsa ta hada jiki da shi sai
ta ji kamar wani abu yanay ma ta 'yummm ' a
jikinta.
.
10- Yaro ya kan zama mai fada da cizon yaran
mutane.
.
11-Yaro yakan zama mara jin magana kuma baya
jin duka, ba ya rabuwa a fada.
.
12-Wani yaron sam ba ya magana, wani kuma ba
ta fita sosai.
.
13- Ya kan sa yaro ya dinga dalalar da yawu daga
bakinsa.
.
14- Ya kan shanyewa yaro hannu ko ya dinga jan
kafa.
.
15-Wani lokaci ya kan bar tabo a jikin yaro, a ga
wani abu ya fito ma sa a ka ko a ciki ko a gadon-baya.
.
16-Yakan rikewa yaro kafa ya hana shi tafiya.
.
17- Ya kan sa kan yaro ya `ki tsayawa.
.
18-Yana sa gashin kan yara ya dinga ciccizgewa,
ko kuma su dinga tsigewa da hannunsu.
.
19-Yana sa yaro ya zama dolo a cikin yara.
.
20-Yana sa yaro ya dinga dauke-dauken kayan
mutane ko kudi.
.
.
Da dai alamomi masu yawa.
.
.
Indai Yaro ya girma da wannan Aljani a jikinsa ba
a cire shi tun yana karami ba to da wahala su rabu
da shi.
.
Don kuwa ko Rukiyya akai ba sa magana, wani
lokaci kuma su kan yi dakyar. Kuma ba su fiye
rabuwa da shi kwata-kwata ba, saidai suy sauki.
.
.
Idan wannan Aljani ya girma tare da yaro ya kan
zamar ma sa JINNUL QARIYN ﺟﻦ ﺍﻟﻘﺮﻳﻦ wanda za
muy bayani a kansa nan gaba insha Allahu.
.
. ABUBUWAN DA UMMUL ATFAL KE YIWA YARA 1- Suna daukar jarirain mutane su tafi yawo da su. Wani lokaci ma uwar yaron tana kallo za a dau yaron ai waje da shi. 2- Suna baiwa yara ruwa ko kuma guba su sha. 3- Suna daukar jarirain mutane su ba su nono. 4- Suna zuwa tun lokacin saduwa su yi kokarin hada tsatsonsu dana uban yaron, don a haifo musu da. Dadai sauransu. YADDA AKE TSARE YARA DAGA SHARRIN UMMUL ATFAL
da yaddar Allah.
.
.
*A dinga sanyawa yara tufafi in za suy bacci,
ma'ana kada a kwantar da su tsirara. Hakama
lokacin da suke harkokinsu da rana.
.
*A dinga baiwa Jinjiri ruwan zamzam koda lokaci
zuwa lokaci ne.
.
*A hada man Zaitun da Man Habbatussaudaa a
dinga shafewa Yaro jikinsa koda sau daya ne a
sati.
.
*A dinga tofa Ayatal Kursiyyu da Falaqi da Nasi a
ruwa ana baiwa yaro yana sha.
.
.
YARON DA YA RIGA YA KAMU gaskiya sai an kai
shi wajen Malamai masana harkar Aljanu da magunguna.
.
. ZUWA GA MAI RUKIYYA Yadda za ka mu'amalanci Aljanin yara wajen fitar da shi. 1- Idan aka ce Aljanin yara ana nufin yaro dan shekara goma sha biyu zuwa kasa. 2- Yaro jikinsa yana da rauni, don haka ba kodayaushe Aljani yake zaune a jikinsa ba. 3- Ingantacciyar hanyar cirewa yaro Aljani shi ne a dora hannu akan qirjinsa ay masa karatu a kumnensa na hagu. 4- A tabbatar an shafewa yaron jikinsa da ManZaitun wanda a ka tofa ayoyin Ruq'yah a ciki kafin a faray masa Ruq'yar kuma nisanci ido da shi domin ManZaitun yana kona ido. 5-Kada a dau dogon lokaci ana magana da Aljani a jikin yaro, kawai ay saurin fitar da shi ta hanya me sauqi. 6-Lokacin da za ay wa yaro Ruq'yah se ay amfani da sauti madaidaici yadda yaron ba ze firgita ba. 7-Kada a sanar da yaro karami cewa Aljanu ne suke damunsa. A dai nuna masa kawai wata lalura ce ta daban . 8-Idan Ruq'yah ba aikinka bace, kada ka ce za kay wa wani yaro ko babba. Zai fi kyai a kay mutum wajen masu aikin.
9-Idan aka yi wa Yaro karami dan kasa da shekara hudu Rukiyya zai iya
mutuwa.
.
.
Ya Allah ka tsare mana lafiyar mu da ta 'ya'yanmu,
wadanda suka kamu kuma Allah ka ba su lafiya.
Daga shafin Bashir Halilu mai Rukiyyah da harhada magungunan musulunci.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment