HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI
HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI
Menene matsayin daura Laya da shan Tofi da shan Rubutu a addinin Musulunci?.
Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Ruq'yah da Harhada magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Abinda ya zo na Hadisan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
game da yadda wasu mutane suke amfani da wasu abubuwa da sunan kare kansu daga wani sharri ko kuma janyowa kansu wani amfani. Inda mutane su kanyi amfani da Laya ko Qaho ko Wuri ko Zare ko Dutse, wasu kuma sukan yi Tofe-tofe ajikin wasu abubuwa ko a jikin mutum da sunan magani, yayinda kuma wasu suke rubuta wadansu abubuwa su wanke, su sha. Ko na Alqur'ani ko wanda ba na Alqur'ani ba. Da kuma matsayin yin wanka da ruwan Alqur'ani ko shafe jiki da shi.
Da fari dai, ga fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratuz Zumar:-
بسم الله الله الرحمن الرحيم
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۚ قُلْ أَفَرَأَيْتُم مَّا تَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ إِنْ أَرَادَنِيَ اللَّهُ بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَاشِفَاتُ ضُرِّهِ أَوْ أَرَادَنِي بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ مُمْسِكَاتُ رَحْمَتِهِ ۚ قُلْ حَسْبِيَ اللَّهُ ۖ عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ الْمُتَوَكِّلُونَ
(سورة الزمر)
Ma'ana:-
"Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara.". (Suratuz Zumar, ayah ta 38).
Abinda za mu fahimta daga wannan ayah.
Duk wanda kake rokonsa don neman biyan bukata to ba zai iya yaye maka wata cuta ba sannan ba zai iya amfana maka komai ba, saidai idan Allah kawai ka kira, domin ga Allah ne masu tawakkali na gaskiya suke dogara.
Ga wasu Hadisai.
عن عمران بن حصين "أن النبي ﷺ رأى رجلا في يده حلقة من صفر فقال: ما هذه؟ قال من الواهنة. فقال: انزعها، فإنها لا تزيدك إلا وهنا؛ فإنك لو مت وهي عليك ما أفلحت أبدا رواه أحمد بسند لا بأس به.
Ma'ana:-
An kar6o daga Imrana bin Husain, cewa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ga wani mutum da wani zobe na tagulla a hannunsa, sai ya ce masa menene wannan?. Sai ya ce 'Rigakafin ciwon hannu ne'. Sai ya ce masa 'Cire ta, domin ba za ta kara maka komai ba sai wahala. Domin da ka mutu tana tare da kai, to har abada ba za ka rabauta ba".
Ahmad ne ya ruwaito Hadisin da sanadin da ba laifi acikinsa.
Karin bayani.
Daga wannan Hadisi za mu fahimci cewa.
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya hana Sahabinsa saka wani zobe, wanda yake qudurce cewa zai iya hana shi kamuwa da wata cuta. Ya umarce shi ya cire shi nan take. Sannan ya sanar da shi cewa 'Da a ce ya mutu da wannan zoben a hannunsa to da har abada ba zai rabauta ba. Ma'ana kenan zai gamu da azabar Allah. Sannan tun a duniya ma zoben ba zai kara masa komai ba sai wahala, kamar yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya fada.
Wannan yana nuna cewa qudurce cewa wani zobe yana hana kamuwa da wata cuta, kamar yadda wasu mutanen suke ratayawa yara tagulla don maganin baki ko kuma masu saka zoben Azurfa don maganin Aljanu ko maganin farin jini, duka wannan shirka ne. Saidai idan mutum ya saka ne don ado, ba don wata manufa ba, to ba laifi bane.
Wannan Hadisi, bayan Imam Ahmad Ibn Hibban ma ya fitar da shi da Ibn Majah da Hakim, kuma Hakim ya inganta shi sannan Zahabi ya bi shi akan ingancinsa
A wani Hadisin kuma.
وله عن عقبة بن عامر مرفوعا: من تعلق تميمة فلا أتم الله له، ومن تعلق ودعة فلا ودع الله له وفي رواية: من تعلق تميمة فقد أشرك.
Ma'ana:-
Daga gare shi dai, an kar6o daga Uqbata bin Amir daga maganar Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
"Duk wanda ya rataya Laya to kada Allah ya cika masa burinsa, kuma duk wanda ya rataya Wuri to kada Allah Ya warkar da shi".
A wata ruwayar kuma "Duk wanda ya rataya Laya to ya yi shirka".
Karin bayani:-
Wuri shi ne wani abu mai kama da hakori ko qashi, wanda ake hakoshi daga kasa, ana ratayawa yara shi a wuyansu da sunan magani sannan `yan-duba ma suna amfani da shi.
Daga cikin Hadisin za mu fahimci cewa Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
ya yi mummunar addu'a ga wanda ya rataya laya, inda ya ce "Kada Allah ya biya masa bukatarsa", sannan ya yi mummunar addu'a ga wanda ya rataya wuri inda ya ce "Kada Allah Ya warkar da shi". Haka dai ruwaya ta biyu ta nuna cewa "Duk wanda ya rataya laya to ya yi shirka".
A wannan Hadisin kuma
ولابن أبي حاتم عن حذيفة: أنه رأى رجلا في يده خيط من الحمى، فقطعه وتلا قوله: وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللَّهِ إِلاَّ وَهُمْ مُشْرِكُونَ [يوسف: 106].
Daga Ibn Abi Hatim daga Hazaifah cewa: ya ga wani mutum a hannunsa akwai wani Zare na Rigakafin Zazza6i, sai ya yanke masa shi kuma ya karanta fadin Allah Madaukakin Sarki
وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللَّهِ إِلاَّ وَهُمْ مُشْرِكُونَ [يوسف: 106].
Ma'ana
"Kuma yawancinsu ba sa yin imani da Allah face suna yin shirka". (Suratu Yusuf, ayah ta 106).
A nan za mu fahimci cewa:-
Daura wani Zare ko Rumi (Rumi wani nau'in zare ne da ake hada zarurruka da yawa a tufka su waje daya) don ya tsare shi daga kamuwa da wata cuta to ya yi shirka. Kamar yadda wasu suke daurawa yara bakin zare a wuyansu ko a hannunsu, da sunan tsari, wasu kuma sukan daurawa yara Rumi a `kugunsu, shi ma dai don neman tsari.
Ba mutane kawai ba, har dabbobi ma Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
ya hana daura musu laya.
في الصحيح عن أبي بشير الأنصاري "أنه كان مع رسول الله ﷺ في بعض أسفاره؛ فأرسل رسولا أن لا يبقين في رقبة بعير قلادة من وتر، أو قلادة إلا قطعت".
Ma'ana:-
A cikin Sahihin Hadisi, daga Abiy Bashir Al-Ansariy, cewa "Wata rana ya kasance tare da Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
acikin wata tafiya, sai (Manzon Allah ﷺ ) ya aika dan aike akan 'Kada a bar wani Rataye na Tsirkiya a wuyan wani Raqumi, ko kuma kowane irin rataye face an yanke ta".
Bukhari ne ya ruwaito shi.
Karin bayani. Tsirkiya wani zare ne mai kama da roba, har yanzu wasu suna amfani da shi wajen daura abun wuya ko damarar mata.
Daga wannan Hadisi za mu fahimci cewa:-
Manzon Allah ﷺ ya ba da umarni cewa duk Rakumin da aka daura masa Tsirkiya ko Sarka ko ma wane irin abu aka daura masa, da sunan neman sa'a ko kare shi daga wani bala'i to a yanke shi.
Don haka ashe ba daidai bane a daurawa abin hawa wata laya ko wani abu da sunan kare shi daga fadawa matsala ko yin hadari.
Laya tana da matsala in ka karanta wannan Hadisin.
وعن عبد الله بن عكيم مرفوعا: من تعلق شيئا وُكل إليه رواه أحمد والترمذي
Ma'ana:-
An kar6o daga Abdullahi bin Ukayyim daga maganar Manzon Allah ﷺ cewa "Wanda ya rataya wani abu, to sai a jingina shi zuwa gare shi".
Ahmad da Tirmiziy ne su ka ruwaito wannan Hadisi
Wato wannan Hadisi yana nuna mana cewa, idan mutum ya rataya wani abu da sunan ya taimake shi, to sai Allah ya kyale shi da wannan abun, ya taimake shi din, in zai iya. Kenan duk wanda ya rataya Laya ko Dutse ko Wuri ko Qaho da dai sauransu, da sunan neman agajinsa, to sai Allah ya janye tallafin da yake ba shi, ya kyale shi da layar ta sa.
Bayan Laya ba ta da amfani, kalli irin yadda take janyowa musulmi asara.
وروى أحمد عن رويفع قال: قال لي رسول الله ﷺ: يا رويفع، لعل الحياة ستطول، بك فأخبر الناس أن من عقد لحيته، أو تقلد وترا، أو استنجى برجيع دابة أو عظم، فإن محمداً بريء منه.
Ma'ana:-
Ahmad ya ruwaito daga Ruwaifi'u ya ce "Manzon Allah ﷺ ya ce da ni
"Ya Ruwaifi'u, mai yiwuwa rayuwarka za ta yi tsawo, to ka gayawa mutane cewa, duk wanda ya yiwa gemunsa kitso, ko ya rataya Laya ko ya yi tsarki da kashin dabba ko qashin dabba, to ba shi ba Annabi Muhammad ﷺ.
Wannan Hadisi ko ba a yi masa sharhi ba, ka san kai tsaye Manzon Allah ﷺ ya ce "Duk wanda ya rataya laya to ba shi ba Annabi Muhammad ﷺ.
Allah Ya kiyaye mu.
Hasali ma, in ka ga mutum da laya ka cire masa ita, lada za ka samu.
وعن سعيد بن جبير قال: "من قطع تميمة من إنسان كان كعدل رقبة" رواه وكيع
Ma'ana:-
An kar6o daga Sa'id bin Jubair ya ce "Wanda ya yankewa wani mutum layarsa, to yana da ladan `yanta Baiwa".
Wakiy'u ne ya ruwaito shi.
Wannan Hadisi yana nuna mana cewa, idan ka ga mutum da laya, in har kana da iko da shi to ka cire masa, domin lada Allah Zai ba ka, saboda ka tsamo mutumin daga shirka, kamar dai yadda AbdUllahi bin Mas'ud
رضي الله عنه
ya ga matarsa da laya, ya kar6a, ya tsitstsinka ta, za mu kawo Hadisin nan gaba, insha Allahu.
Matsayin Sahabbai akan Laya.
وله عن إبراهيم قال: "كانوا يكرهون التمائم كلها، من القرآن وغير القرآن".
Daga wajensa dai, daga Ibrahim ya ce "(Sahabbai) sun kasance suna kyamar laya, ta Alqur'ani da wacce ba ta Alqur'ani ba".
Wannan Hadisin ma ma'anarsa a fili ta ke, cewa Sahabban Manzon Allah ﷺ ba su yarda a daura Laya ba, ko Alqur'ani aka rubuta a cikinta ko ba Alqur'ani aka rubuta ba.
Matakin da Sahabbai suke dauka idan iyalinsu sun daura laya.
وعن زينب امرأة عبد الله بن مسعود - رضي الله عنه - أن عبد الله رأى في عنقي خيطا ، فقال : ما هذا ؟ فقلت : خيط رقي لي فيه قالت : فأخذه فقطعه ، ثم قال : أنتم آل عبد الله لأغنياء عن الشرك ، سمعت رسول الله - صلى الله عليه وسلم - يقول : " إن الرقى والتمائم والتولة شرك " فقلت : لم تقول هكذا ؟ لقد كانت عيني تقذف ، وكنت أختلف إلى فلان اليهودي ، فإذا رقاها سكنت ، فقال عبد الله : إنما ذلك عمل الشيطان ، كان ينخسها بيده ، فإذا رقي كف عنها ، إنما كان يكفيك أن تقولي كما كان رسول الله - صلى الله عليه وسلم - يقول : " اذهب البأس ، رب الناس واشف أنت الشافي ، لا شفاء إلا شفاؤك ، شفاء لا يغادر سقما " . رواه أبو داود .
Ma'ana:-
Kuma an kar6o daga Zainab, matar AbdUllahi bin Mas'ud Allah Ya kara yarda a gare shi, ta ce "Hakika AbdUllahi ya ga wani Zare (ko a ce Rumi da Hausa) a wuyana, sai ya ce 'menene wannan? ', sai na ce Zare ne akai min tofi a jikinsa. Sai ya kar6a, ya tsitstsinka shi sannan ya ce 'Ku iyalin gidan AbdUllahi, wAllahi kun fi karfin shirka. Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa 'Hakika Tofe-tofe da Layoyi da Asirin Mallaka shirka ne".
Ta ce 'Sai na ce masa don me kake fadar haka?, hakika na kasance idona yana yi min ciwo, kuma na kasance ina zuwa wajen wani Bayahude, idan yay min tofi sai idon nawa ya warke. Sai AbdUllahi (bin Mas'ud) ya ce 'To ai wannan aikin Shaidan ne, shi ne yake tsokane idon da hannunsa, idan yay tofin sai ya dena. Kawai abinda zai wadatar miki shi ne, ki fadi abinda Manzon Allah ﷺ ya ke fada
'Iz'habil ba'asi, Rabban naas, washfi, Antash shafiy, laa shifaa'a illaa shifaa'uka, shifaa'an laa yughaadiru saqaman'
( Ma'ana)
'Ka tafiyar da cuta, Ya Ubangijin mutane, kuma Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, ba wata warkarwa sai warkarwarka, warkarwar da ba ta barin ragowar ciwo".
Abu Dawuda ne ya ruwaito shi.
Daga wannan Hadisi za mu fahimci.
Fahimtar Sahabbai game da matsayin laya da kuma matakin da suke dauka akanta. Sannan tofe-tofe ajinkin wani kulli da sunan magani shirka ne amma tofi irin wanda ba musulmai ne suke yinsa ba, kamar yadda matarsa ta ce ta je wajen Bayahude. Saidai idan tofin na ayoyin Alqur'ani ne da ingantattun addu'o'i to ba laifi, kamar yadda bayani zai zo nan gaba. Sannan mas'ala ta hudu acikin Hadisin tana nuna yadda ake hada baki tsakanin Sahidan da Boka, in Shaidani ya saka cutar shi kima Bokan sai ya bada magani, alhali duk bakinsu daya.
ABUBUWAN DA ZA MU IYA FAHIMTA DAGA WADANNAN HADISAI BA KI DAYA SU NE.
1- Hana daura laya da makamanta, kamar su Guru da Kambu da dai sauransu.
2- Duk wanda ya mutu da laya a jikinsa to ba zai rabauta ba ranar Alqiyama.
3- Duk wanda ya daura laya to ba za ta kara masa komai ba sai wahala.
4- Duk wanda ya rataya wani abu don ya taimake shi, to Allah Zai kyale shi da wannan abun.
5- Kai tsaye, duk wanda ya daura laya to ya yi shirka.
6- Rataya wani Zare ko Rumi, ko Zobe ko Sarka da kudurce cewa zai taimake ka, shi ma matsayinsu daya da laya.
7- Rataya Wuri ko Qaho ko sassan wata dabba, shi ma yana cikin haka.
8- Mummunar addu'a da za ta tabbata akan wanda yake rataya irin wadannan abubuwa, kamar yadda ya zo a Hadisi.
9- Tofi, wanda ba na ayoyin Alqur'ani ko addu'a sahihiya, ba shirka ne.
10- Yi wa mutum asirin mallaka shirka ne.
11- Yin Ruqiyyah ko tofi da Ayoyin Alqur'ani ko addu'ar Manzon Allah ﷺ ba laifi bane ba, kamar yadda Ibn Mas'ud ya koyawa matarsa.
12- Ladan da wanda ya cirewa wani laya zai samu.
Maganganun Malamai akan wannan mas'ala suna da yawa, amma zan takaita in kawo iya manufar ta su.
*Malamai sun yi sa6ani akan layar da aka rubuta ta da Alqur'ani ko Addu'ar Manzon Allah ﷺ, wasu Malaman sun ce za a iya daura ta ba laifi, amma idan aka hada ta da wani abu to shirka ne, saidai magana mafi inganci ita ce, Sahabbai suna kyamar daura laya, ko ta Alqur'ani ko wacce ba ta Alqur'ani ba, kamar yadda ya zo a Hadisin da ya gabata. Don haka magana mafi inganci ita ce gaskiya laya haramunce ko kuma shirka.
*Yin Ruqiyyah ko yin Tofi ko Shan Rubutu, wanda ya kasance da Ayoyin Alqur'ani ne ko Hadisan Manzon Allah ﷺ su ma Malamai sun yi sa6ani akan halarcinsu, inda wasu su ka ce ba su halatta ba. Amma dai maganar mafi inganci shi ne sun halatta, saboda yadda Manzon Allah ﷺ ya aikata haka, Nana A'isha Allah Ya kara yarda a gareta itama ta aikata haka, haka nan sauran Sahabbai kamarsu Ibn Mas'ud, kuma an aikata Ruqiyyah Manzon Allah ﷺ ya tabbatar da yin hakan, da dai hujjoji da dama.
In kana bukatar karin bayanin akan halarcin rukiyyah, za aka iya duba shafina, domin na yi rubutu mai tsawo a kai da dalilai. Za ka iya shiga nan domin dubawa fb.me/tarbiyyahislamiyyah3
domin duab rubutuna mai taken 'Matsayin Ruqiyyah a addinin Musulunci'.
GAME DA HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA YIN TOFI KUWA
Za mu dauki fatawar Shaikh Bin Baaz, ko da ba mu kawo dalilai daya bayan daya ba, kasancewarsa dalilannda ya kafa hujja da su sanannnu ne a addinin Musulunci.
Ya zo a cikin littafin Majmuw'ul fataawaa
مجموع الفتاوى
An tambayi Mallam game da hukuncin rubuta Alqur'ani, a wanke, a sha don magani, sai ya ce:-
"Ba mu san wani abu da ya haramta haka ba. Saidai abinda ya fi inganci shi ne, a karanta ajikin mara lafiyar, a dinga tofa masa, ko kuma dan uwansa ya karanta masa a hannunsa ko a kafarsa ko kuma a wajen da yake masa ciwon, kamar dai yadda Annabi ﷺ ya kasance yana aikatawa".
Mallam ya cigaba da cewa "Haka nan idan mutum ya karanta acikin ruwa ya sha, ko ya shafe jikinsa, ko ya rubuta ayoyi da addu'o'i acikin kwarya, acikin Za'afaran, ko ajikin takarda kuma ya wanke, ya sha to babu laifi. Da yawa daga Magabata na kwarai sun aikata haka, haka nan Ibn Qaiyim da sauran manyan Malamai sun ambaci hakan da cewar ba laifi bane. Amma dai abinda ya ke mafi fifiko da cancanta da kuma amfani, shi ne abinda Manzon Allah ﷺ ya aikata, shi da kasance, ya kasance yanaiwa mara lafiya karatu kuma yana yiwa mara lafiya tofi, kuma ya kasance yana yiwa kansa karatu sannan yana yin tofi ajikinsa idan ya samu wata damuwa ﷺ. Haka nan idan zai yi bacci yana yin tofi a hannunsa sannan ya shafe jikinsa. Lokacin da yay rashin lafiya kuma ﷺ, rashin lafiyarsa ta karshe, sai A'isha Allah Ya kara yarda a gareta, ta kasance tana yi masa tofi a hannunsa, sannan ta shafe inda hannun zai iya kaiwa ajikinsa (da hannunsa ﷺ ta ke shafawa, ba da hannunta ba) don koyi da abinda yake aikatawa lokacin yana da lafiya ﷺ. Kuma ya tabbata cewa Manzon Allah ﷺ ya yi wa Sabit Bin Qais karatu (na tofi) sannan ya zuba masa ajikinsa ﷺ".
Wannan shi ne karshen fatawar Bin Baaz.
Haka abin ya ke kuma Manzon Allah ﷺ ya yiwa Sayyidna Aliy
رضي الله عنه
tofi a idonsa, lokacin da ya ke ciwon ido.
Sai Bashir Halilu ya ce:-
Daga fatawar Mallam, za mu fahimci cewa:-
1- Ba laifi bane a rubutawa mutum Alqur'ani ko addu'a ya sha.
2- Yin tofi na Alqur'ani ko addu'a, shi ma ba laifi bane.
3- Yin tofi ya fi shan rubutu falala da amfani.
4- Ana iya yin tofi a jikin mutum ko a cikin ruwa ko acikin magani sannan a ba shi ya sha, kamar yadda Mallam ya ambaci Za'afaran.
5- Ya halatta mutum ya rubuta Alqur'ani ko yay tofi a ruwa, ya shafe jikinsa da shi.
6- Ba sai lokacin rashin lafiya ba, haka kawai ma mutum zai iya yiwa kansa tofi, kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya keyiwa kansa, saida rashin lafiya ta same shi sannan matarsa ta ke yi masa.
7- Ba laifi bane don wani ya yiwa wani tofi ya sha, ko rubutu, ba dole sai mutum ya yi da kansa ba.
To amma fa duka wannan Mallam yana magana ne akan Rubutu ko tofi na zallan Alqur'ani ko addu'a sahihiya, shi ne ya halatta. Amma matukar aka hada Alqur'anin da sunayen Aljanu ko Rauhanay ko wasu `Dalasimai ko Saqandamai ko Hatimai da dai sauransu, to wannan shirka ne, kamar yadda hujjoji su ka gabata.
Allah Ya tsare mana imaninmu kuma Ya sa mu dace Amiyn.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruqiyyah da Harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Shiga shafukan Tarbiyyah Islamiyya don yin bincike akan abubuwa da dama, kamar:-
GURAREN ZAMAN AL-JANU ACIKIN GIDAJEN MUTANE
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/07/guraren-zaman-al-janu-acikin-gidajen.html)
TARKON AL-JAN. Yadda ake daure Aljani da kashe shi yayin Rukiyyah.
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/07/yadda-ake-daure-aljani-da-kashe-shi.html
HUKUNCIN YIWA ALJANU YANKA. YANKA DABBOBI BISA UMARNIN ALJANU.
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/05/hukuncin-yiwa-aljanu-yanka-yanka.html
BAYANI AKAN RAUHANAI Shin Rauhanay Aljanu ne ko Mala'iku? http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/bayani-akan-rauhanai-shin-rauhanay.html
DANNAU. AL-JANI MAI DANNE MUTUM LOKACIN DA YAKE BACCI.
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html
Da dai sauransu
Za ka iya downloading na application din Bashir Halilu Tarbiyya Islamiyyah a wayarka, ta yadda za ka dinga samun dukkan rubututtukan mu acikin sauki, a yanzu haka sama da mutum dari suna amfani da shi a wayoyinsu, kawai shiga wannan shudin rubutun
http://www.appsgeyser.com/7550770
sai ka danna download kay intalling a wayarka.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruqiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment