AMFANIN ZA'AFARAN GA LAFIYAR AL'UMA
AMFANIN ZA'AFARAN
==================
Ga lafiyar al'umma.
.
.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah. Masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
.
Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai dauke da launi mai abin sha'awa. Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama.
An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan akay Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma kasashenmu na Afrika.
.
.
Za'afaran yana maganin cututtuka kamar:
.
★Zubewar Gashi.
Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanqo. Hada Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana kara yawan gashi.
.
.
★Gyaran Fuska
Hada Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tay kyau da sheqi. Ana yin wannan hadin sau daya a sati.
.
.
★Matsalolin fata.
A jika ciyawar Za'afaran a ruwa tsawon awa biyu zuwa uku. Sai a shafe fatar jiki da shi. Yana bada fata mai laushi da taushi. Ana yin haka sau biyu zuwa uku a sati.
.
.
★Maganin kuraje.
A hada Za'afaran da Ray'han a kir6a a shafa akan fata sai a wanke bayan minti goma. Wannan hadin yana maganin kuraje, kyasbi, makero da tabo da kuma sauran cututtukan fata.
.
.
★Kwayoyin Cuta.
Zuba ko fesa Za'afaran a waje yana maganin kwayoyin cututtuka da ba'a iya ganinsu kuma yana kyautata lafiya.
.
.
★Kyautata Bugun Zuciya.
Za'afaran yana da sinadari potassium wanda ke kyautata bugawar zuciya da kuma bata damar yin aikinta yadda ya kamata.
.
.
★Zagayawar jini.
Za'afaran yana da sinadarai irinsu coper, potassaium, calcium, manganese, iron, magnesium, da zinc da kuma selenium. Wasu daga cikin wadannan sinadarai suna taimakawa wajen daidaita yanayin jini a jikin mutum.
.
.
★Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Za'afaran yana dauke da wasu kananan sinadarai kamar zea-xanthin da lycopene wadanda ke kare jikin mutum daga kamuwa da cutar Kansa wato Daji.
.
.
★Saukaka Narkewar Abinci.
Za'afaran yana da muhimmanci wajen saukake narkewar abinci a jikin mutum saboda sinadarin anti-cinvulsant da sauran sinadarai dake cikinsa.
.
.
★Ciwon Hakori.
Shafa Za'afaran hade da Zuma yana taimakawa wajen maganin cututtukan dasashi da hakori.
.
.
★Cututtukan Cikin Baki.
Idan aka hada Za'afaran da Zuma da Graceline ana shafawa a cikin baki yana maganin kuraje da sauran cututtukan da kan iya samuwa a cikin baki.
.
.
★Gyaran le6e.
Za'afaran yana cikin tsirrai kadan wadanda ke samar da sinadarin vitamin B2 mai yawa. Amfani da shi yana gyara la66a da kuma kyautata hadiyar abinci daga baki zuwa makogwaro.
.
.
★Maganin Sanyi da Tari.
Idan aka hada Za'afaran 1grm da ruwa 1ltr aka sha yana maganin Sanyi da kuma Tari.
.
.
★Jini lokacin Al'ada.
Za'afaran yana da kyau wajen daidaita zuwan jini yayin al'ada.
.
.
★Maganin Maza.
Amfani da Za'afaran yana taimakawa mazaje su dawo da karfinsu. Hatta tsofaffi yana ba su kuzari sosai.
.
.
☆ Amma a kula ☆
.
☆Yin amfani da Za'afaran ba bisa ka'ida ba yana sa
* Mura
*Ciwon Kai
da kuma
*Daukewar Miyau a baki.
.
.
Masana harkar lafiya ba suy bayanin illar Za'afaran ga mace mai ciki ba, sun ma dai ce yana taimaka mata.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah. Masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment