BAYANI AKAN RAUHANAI Shin Rauhanay Aljanu ne ko Mala'iku?
MENENE RAUHANIY?
Su waye Rauhanay?
.
.
_Wasu mutane suna ikirarin cewa suna aiki da Rauhanay, inda suke taimaka musu wajen bada magani ko wasu ayyukansu na rayuwa. To su waye rauhanay kuma aiki da su ya halarta?_
```Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin ruqiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya +2348162600700, +2348134434846.```
.
.
بسم الله الرحمن الرحيم.
Da farko dai kalmar *Rauhan* tana nufin wani 6oyayyen ilimi wanda Allah Ya ke6anci wasu daga cikin bayinsa da shi, in ba su ba ba wanda ya sanshi, Allah ne yake za6ar wasu daga cikin bayinsa Ya sanar da su.
Kenan kalmar _Rauhaniy_ tana nufin _wanda yake da ilimin da kowa bai sani ba sai shi_.
To amma su waye Rauhanan da wasu Malamai ko Shehunai da sauran wasu mutane suke ikirarin suna aiki da su?
Malaman da suka kawo maganar Rauhaniy a littattafan _dibbu طب_
sun yi sa6ani akan asalin Rauhaniy da kuma menene shi. Maganganu mafiya shahara dai su ne guda uku.
*Magana ta farko*:- ita ce Su Rauhanay Mala'iku ne. Allah Ya halicce su ne kamar sauran Mala'iku, saidai su suna mu'amala da mutane. Tsarkin zuciyar mutum da kuma kula da ibada shi yake sawa wadannan Mala'iku su kusance shi har su dinga mu'amala da shi.
Kowane mutum yana da Aljani kuma yana da Mala'ika a tare da shi. Idan aikin sa6onka yay yawa to Aljaninka zai tasiri akanka idan kuma aikin ibadarka ya rinjaya to Mala'ikanka zai zama shi ne jagoranka. Wannan Mala'ikan mai maka jagora shi ne Rauhaninka.
Ya danganta da yadda ya yaba da hankalinka da nutsuwarka, sai ya bayyana maka kansa a fili kuma ya dinga zuwa kuna mu'amala, yana taimaka maka akan wasu ayyukanka na rayuwa da ibada.
Kowane mutum yana da wannan Mala'ika Rauhaniyyi a tare da shi, kuma sunanka yana kama da sunan Rauhaninka. Misali idan sunanka _Bashir_, to sunan Rauhaninka _Bashiru'iylu_. Idan sunanka _Musa_, to sunan Rauhaninka _Musa'iylu_. Ma'ana kalmar _iylu_ ake karawa a gaban sunan mutum shikenan sunan Rauhaninsa ya fita.
Wannan ita ce magana ta farko.
*Magana ta biyu kuma ita ce*
Su Rauhanay, an halicce su ne da haske kuma jikinsu na haske ne amma *_ba Mala'iku bane kuma ba Aljanu ba_*, su dai wata halittace ta daban.
Acikinsu akwai wanda yake yiwa wata surar Alqur'ani hidima ko kuma yana hidimtawa wani daga cikin sunayen Allah, da dai sauransu.
( _Abinda ake nufi, wato acikinsu akwai wanda idan ka karanta wata sura ta Alqur'ani, to zai zo wajenka ya tambayeka abinda kake so yay maka ko kuma idan ka ja wani daga cikin sunayen Allah to Rauhanin zai zo ya tambayeka duk irin hidimar da kake so yay maka._ )
Ba sa aikata sa6o ko sharri kuma ko mutum ya sasu su cutar da wani basa yi.
Ba sa ra6ar mutum ko su dinga mu'amala da shi sai yana bin Allah kuma yana zama da tsarki sannan su kan dorawa mutum wani lazimi na musamman da zai dinga karantawa a wani sanannen lokaci ko wasu salloli da azumi dai sauransu, indai yana so su cigaba da zama da shi.
Kowane mutum zai iya mallakar Rauhaniy idan ya bi hanyoyin da ake bi a mallake su kuma za suy masa hidima matukar ya iya tafiyar da su.
*Da akwai hanyoyi da yawa na mallakar Rauhanay*.
_Misali_:- Da akwai hanyar da mutum zai ke6ance kansa a wani waje da aka gaya masa, ya sanya wasu nau'in tufafi da akay masa umarni, ya dauki azumi na adadin wasu kwanaki sannan ya dukufa yana karanta wasu surorin Alqur'ani da aka ke6ance masa, tare da wasu sunayen Allah yana kuma amfani da wasu turaruka na ruwa ko na hayaki sannan ya dinga kiran sunayen Rauhanan da yake da bukata su bayyana agareshi yanay musu kirari da iyayensu tare da karanta wasu rubutattun haruffa wadanda bai san ma'anarsu ba. Daga nan sai su bayyana agareshi, su gaya masa ka'idodi da dokokin zama da su da kuma iya ayyukan da za su iya yi masa. Shikenan ya zama mai rauhanay.
Saidai hanyar tana da hadari, domin idan mutum yay kuskure yana iya haukacewa.
*Magana ta uku da Malaman* _dibbu طب_
*Sukay akan asalin rauhanay itace*
Su Rauhanay Aljanu ne. Asalin halittarsu da ta Aljanu daya ne. Dukkansu `ya`ya da jikokin Iblis ne. Saidai kamar yadda mu ka sani, acikin Aljanu akwai musulmai, akwai kafurai. Akwai masu bin Allah, akwai masu sa6o, kamar dai yadda Allah Madaukakin Sarki Yay bayani acikin suaratul jinn da sauran gurare acikin Alqur'ani mai girma.
To dukkan Aljani musulmi wanda ba ya cutar da mutane kuma yana kula da ibada sannan yana mu'amala da mutane masu tsarki, sunansa Rauhaniy.
Don haka Rauhaniy a fahimtar wadannan malaman _dibbu طب_
ita ce Rauhanay su ne Salihan bayin Allah ko kuma Waliyyay daga jinsin Aljanu.
*A dunqule*
Dukkan Malaman _'Dibbur Rauhaniy طب الروحاني_
Sun hadu akan cewa Rauhanay musulmai ne masu karfin imani, ba sa cutarwa, ba sa zama da mutum sai mai tsarki sannan suna taimakon mutane. Sun yarda cewa Rauhanay sun fi Aljanu karfi da kwarjini da kyawun halitta. Dukkan Rauhanay a Makkah da Madina da Quds suke yin sallah, sannan Rauhanay suna iya fadar abinda ya wuce da abinda zai faru nan gaba kuma suna iya bada sa'a akan wani al'amari ko su juya sharri ya zama alkhairi.
*Sai Bashir Halilu yace*
Dukkan wadannan maganganu basu da asali daga Alqur'ani ko hadisin Mazon Allah صلى الله عليه وسلم
don haka ba sai mun 6ata lokaci muna kawo sunayen littattafai ba amma dai muna da su a hannunmu.
*Magana ta farko* cewa Rauhanay Mala'iku ne, karya ce kawai. Domin Mala'iku ba sa mu'amala da wani mutum har su dinga kawo masa labarai kuma yana ganinsu ido da ido yana sa su ayyuka, saidai in Annabin Allah ne shi. Don haka duk wanda ya kudurce cewa yana da wani Mala'ika da yake aiki da shi to tamkar ya yi da'awar Annabta ne.
*Magana ta biyu kuma* cewa Rauhanay ba mutane bane, ba Aljanu bane kuma ba Mala'iku bane itama shirme ne da kame-kame.
Saboda Allah Madaukakin Sarki bai ambaci wadansu halittu masu ilimi da hankali kuma mukallafai a Alqur ni ba sai mutum da Aljan da Mala'ika kuma sunnar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
bata zo da su ba.
Ba'a ambaci Rauhaniy a Alqur'ani ko a Hadisi ba, Malaman Fiq'hu dana Tauhidi ba suy maganarsu ba, don haka wannan ba shi da tushe balle makama.
*Magana ta uku* cewa Rauhanay wani jinsi ne na Aljanu, wannan ta fi kusa da daidai kuma na fi yarda da ita. Saboda mu'amalarsu da yadda suke shiga jikin mutane da kuma yanayin halittarsu duk daya suke da Aljanu.
*Saidai* gaskiya ba dukkan Aljanu masu kiran kansu da suna Rauhanay ne mutanen kirki ba.
Wasu daga cikinsu Ma6arnata ne, wasu fasiqai ne wasu ma arna ne gabadaya.
Abinda mutane suke ruduwa da shi shi ne, Rauhanan suna bayyanar musu acikin fararen kaya da kyakkyawar siffa sannan dukkansu larabawa ne.
Amma abin akwai rainin wayo da rainin ilimi aciki. Saboda tun daga hanyar da ake Mallakar Rauhanin zaka samu cewa akan yi sa6o da shirka ta wasu hanyoyin, haka ma wajen aikin da su akan yiwa Allah shishshigi.
Misali. Akan rubuta sunayen Allah ajikin takarda ko allo, sai kuma a rubuta _Ajib ya Tabtaya'iylu, ajib ya Rauqaya'iylu, ajib ya Kasfaya'iylu, ajib ya Ahum, Ajib ya Saqkun, ajib ya hal'un, ajub ya Yasun,_ da dai sauransu.
Ma'ana za ay wata addu'a ko a akawo ayar Alqur'ani amma a karshe sai adinga kiran sunayen Rauhanay cewa su biya bukatar abinda aka roka. Na ta6a ganin wata takarda ta maganin tsari, acikin abinda aka rubuta harda _Ajib ya Mallam Alhaji_ wai ana kiran sunan wani Aljani mai suna Mallam Alhaji shi ma ya amsa bukatar.
Mu'amalantar Aljanu yau da gobe da kuma karance-karance akansu, ta sa ni Bashir na kara fahimtar cewa lallai acikin Aljanu akwai makaryata sosai kuma dole ai taka tsantsan da su.
Na ta6a ganin wani mutum mai aiki da Rauhaniy. Sunan Rauhanin nasa Mallam Ahmad kuma shi ne shugaban Rauhanay mazauna Madina da kewaye kamar yadda ya gabatar da kansa amma dana kure Aljanin sai ga shi bai iya larabci ba, akarshe dai ya bayyana min cewa gaskiya shi arnene sunansa Kingkong. Alhali ya dade yana mu'amala da mutumin amatsayin Rauhaniy, har yana sa shi yana yanka dabbobi da yin sadaka da wadansu abubuwa da kuma yin wadansu ibadu.
An ta6a kawo min wata yarinya mai rauhanay wacce idan an samu mara lafiya Rauhanan suke shiga jikinta su je su bayar da magani. Har ma suka bada shawara a kawota wajena don ta kara ilimi amma lokacin dana kure Rauhanin nata sai ya tabbatar min cewa gaskiya shi arnene kuma shi ya hanata aure.
Misalan suna da yawa, domin har recordings na sha tura muku kala-kala na yadda mukay da Rauhanan karya da kuma masu zuwa su cewa mata su ne Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.
Ni kaina wata Aljana ta ta6a zuwa wajena tace min ita Rauhaniy ce, sunanta Mallam Umar amma dana shaqeta sai ta gaya min gaskiya ita mace ce, sunanta Rukayya kuma makauniya ce bata gani, wai na ta6a konata ajikin wata yarinya ne, shi ne take neman hanyar da zata cutar da ni.
Don haka dai gaskiya masu aiki da Rauhanay sai ayi taka-tsan-tasan kuma a nemi ilimin addini domin gudun fadawa cikin halaka.
Mai son karin bayani akan yadda Aljanu suke shiga jikin masu rukiyyah da masu bada magani, sai ya duba rubutuna mai take *Jinnul jalab wattahdeer* zaka ga ta yadda Aljanu suke biyowa masu magani ta salo daban-daban na yaudara har su 6atar da su. Mai son karanta yadda Aljanu suke 6ullowa sauran mutane su yaudaresu da sunan su Rauhanay ne ko wasu matattun waliyyai, sai ka duba rubutuna mai taken *Jinnul filosafiy*.
Insha Allahu a fitowa ta gaba zan yi bayanin *SHIN AIKI DA MUSULMAN ALJANU YA HALATTA? da kuma wani 6angare na kissar Annabi Sulaiman Alahis salam da yadda Aljanu suke masa aiki.*
.
Muna neman dacewa a wajen Allah, Allah Ka tsare mana imaninmu da rayuwarmu. Wassalamu alaykum wa rahmatUllah.
http://bashirhalilu.xtgem.com/__xt_blog/__xtblog_entry/11326488-mene-rauhani-shin-rauhanay-aljanu-ne-ko-mala-iku-ko-kuma-wata-halitta-ce-ta-daban-.-tabiyyah-islamiyyah-blog.#xt_blog
.
.
Bashir Halilu Idris
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin rukiyyah da harhada magungunan musulunci.
Lambar waya+2348162600700, +2348134434846.
Comments
Post a Comment