MAGAGIN BACCI
MAGAGIN BACCI
Da abubuwan da suke kawoshi da kuma yadda ake maganinsa.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Ma'anar Magagin Bacci itace:-
Mutum ya dinga magana ko tafiya ko yin wani aiki da jikinsa, alokacin da yake cikin bacci, ba tare da ya farka ba.
Yawanci dai Magagi ba ya wuce mintuna biyar zuwa sha biyar yake sakin mutane.
Magagin bacci, kamar yadda binciken zamani ya nuna, yana da alaqa da matsalar Dannau (karanta cikakken bayani akan Dannau acikin wannan shudin rubutun
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html ) inda binciken ya nuna cewa, a yayinda mutum yake bacci, to kwakwalwarsa da gangar jikinsa dukkansu suna hutawa ne, idan ya tashi farkawa kuma sai su farka gaba daya.
To idan aka samu matsala, kwakwalwar mutum ta farka, gangar jikinsa kuma bata farka ba, sai mutum ya ji ya dawo cikin hankalinsa amma ya kasa tashi kuma ya ji kamar an daddaure shi. Wannan shi ake cewa Dannau a bincikensu amma dai cikakkan bayani yana cikin wannan shudin rubutun
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html .
To idan kuma ya kasance gangar jikince ta farka, kwakwalwar kuma bata farka ba, sai gangar jikin mutum ta tashi, ta dinga yawo ko ta dinga magana ko wani aiki, ba tare da kwakwalwa ta san abinda ake yi ba. Wannan kuma shi ake kira Magagin Bacci.
ALAMOMIN MAGAGIN BACCI SUN HADA DA
1- Tashi ayi tafiya. Wato mutum ya tashi, ya kama hanya, yana tafiya, ba tare da ya sani ba.
2- Mutum ya tashi, ya zauna, yana mummurza idanu, yana muzurai.
3. Za ka ga mutum ya bude idonsa amma kuma ba ya gane abinda yake gani.
4- Idan mutum yana Magagi, za ka ga idan ka nay masa magana ba ya gane abinda kake cewa ko kuma ba ya ba da amsa daidai.
5- Mai Magagin Bacci yana wahalar wattsakewa, ba kamar mai bacci ba.
6- Yin magana, lokacin da mutum yake bacci. Manya ma suna yi amma ya fi faruwa ga yara. Za ka ji suna ta hirar wasanni da kuma abubuwan da suke yi a makaranta.
7- Mai Magagin bacci ya kan ta shi, ya je yay fitsari, a wajen da ba a nan ake yi ba.
8- Wani kuma Magagin Baccinsa ya kan sanya shi buge-buge ne da jibgawa abokin kwanciyarsa kafa.
ABUBUWAN DA SUKE KAWO MAGAGIN BACCI.
1- Na farko akwai gado. Wato idan an samu acikin iyaye wani yana da shi, to zai iya yiwuwa acikin `ya`yansu wani ya gada.
2- Rashin Bacci. Idan ya kasance mutum ya dade sosai ba ya samun bacci to in ya samu baccin kuma zai iya tashi da Magagi.
3- Tashin mutum lokacin da bacci bai ishe shi ba. Idan ka tashi mai bacci kafin lokacin da ya saba tashi, to zai iya tashi da Magagi.
4- Rashin lafiya ko Zazza6i. Idan mutum ba shi da lafiya, to in ya samu bacci zai iya tashi da Magagi, musamman idan tashinsa aka yi.
5- Shan Magani. Idan mutum ya sha magani lokacin da zai kwanta bacci, musamman maganin asibiti, to zai iya tashi da Magagi.
6- Gajiya. Wanda yay Bacci bayan ya yi aikin gajiya sosai, shi ma zai iya tashi da magagi.
7- Idan mutum ya kwanta bacci, yana jin fitsari, to zai iya tashi da magagi kuma zai iya yin fitsarin a ko ina ne.
8- Yin bacci a waje mai hayaniya.
9- Canjin wajen kwanciya. Idan mutum ya kwanta a wajen da ba anan ya saba kwanciya bacci ba, to shi ma zai iya yin Magagi.
Saidai binciken Malamai ya tabbatar da cewa KASHI CASA'IN DA BIYAR NA MAGAGIN BACCI YANA DA ALAQA NE DA SHAFAR AL-JANU KO SIHIRI, kashi biyar bisa dari 5% ne kawai wadancan abubuwan da aka lissafa suke sabbabawa.
MA'ANAR MAGAGIN BACCI A WAJEN MALAMAN RUKIYYAH
Magagin bacci wani abu ne da yake faruwa, a lokacinda Aljani ya shiga jikin mutum, lokacin da yake bacci. Wani lokacin kuma Aljanu sukan zo suyi wasa da `ya`yan mutane, shi yasa yara suke magana, in suna bacci.
Wani lokacin, Aljanin ne da kansa ajikin mutum, yake magana. Wani lokacin kuma ya kan zowa mutum a mafarki ne, sai ka ji mutum yana magana, ko ihu ko wani aiki, a lokacin da yake bacci, amma in ka tambaye shi bayan ya farka, zai gaya maka cewa ya ga wani abu ne a mafarki. (Za mu kawo cikakken bayani akan mafarki, nan gaba kadan, insha Allahu).
ABUBUWAN DA SUKE KAWO MAGAGIN BACCI.
1- Rashin yin addu'a, yayin kwanciya bacci.
2- Kwanciya da janaba.
3-Fara kwanciya a 6arin hagu.
4- Kwanciya rigingine ko rub da ciki.
5- Matsalar Aljanu, indai mutum yana fama da matsalar Aljanu, zai iya dinga fama da magagi amma ba kowane Aljani ne ya ke sa magagi ba.
6- Matsalar Sihiri. Idan aka yi wa mutum asiri mai alaqa da kwakwalwa, kamar Asirin Mallaka
(karanta cikakken bayani akan Asirin Mallak acikin wannan shudin rubutun
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html ),
ko asirin Haukatarwa
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/asirin-hauka-asirin-da-aka-yiwa-mutum.html ,
ko asirin raba kauna
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/sihirin-raba-kauna-asirin-raba-soyayya.html
da dai sauransu, to zai iya dinga fama da magagi.
ME YASA AL-JANU SUKE SA MUTANE MAGAGI?
Mun yi bayani cewa ba kowane nau'in Aljani ko sihiri ne yake sa magagi ba amma ga abubuwan da suke sawa Aljanu suke sa mutane magagi:-
1- Aljani ya kan sa mutum magagi ne idan ya kasance ba ya iya shiga jikinsa sai lokacinda yake bacci.
2- Idan aka yi wa mutum asiri don ya so wa ni ko kuma don ya kyamaci wani, to Aljanin zai iya zuwa jikinsa, sai ya dinga kiran sunan wancan din.
3- Idan aka yiwa mace asiri don a koreta daga gidan mijinta, za ta iya tashi acikin magagi, ta bude kofa, ta fita waje, komai tsakar dare, saidai idan an lura a bi ta,a kamo ta. In gari ya waye kuma za ta ce ba ta san ayi ba, saboda Aljnin ne ajikinta yake yi.
4- Musamman wanda aka yi wa asiri don a haukata shi, ko a kore shi daga garinsu, zai dinga tashi a firgice, yana zurawa da gudu, ko ya dinga dukan mutane amma daga baya zai ce bai san ya yi ba.
5- Wani Aljanin idan yunwa ta ishe shi, sai ya shiga jikin mutum lokacin da yake bacci, ya zuba abinci, ya ci, amma in ka lura da mutum za ka ga yana cin abincin yana gyangyadi, kuma daga baya zai ce bai san ya ci ba.
6- Wani idan yay magagin bacci, to daga baya yana iya gane cewa ya aikata kaza amma kuma lokacin da ya aikata ba ya iya sarrafa kansa. To wannan da alamun Aljanu na so su shiga jikinsa kenan, ko kuma an yi masa sihiri.
7- Kamar dai yadda yake a matsalar Dannau, wani lokacin Aljani ya kan sadu da mace, ta yadda zata dinga yin wasu abubuwa, kamar magagi, alhali Aljani ne yake saduwa da ita ( karanta cikakken bayani akan Aljani mai saduwa da matan mutane acikin wannan shudin rubutun
https://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/jinnul-ashiq-aljani-mai-saduwa-da-matan.html )
ABUBUWAN DA MAI MAGAGIN BACCI YA KAMATA YA DINGA KIYAYEWA
Likitocin zamani da sukai bincike akan magagin bacci, sun bada shawarwari kamar haka:-
1- Yana da kyau kada ka dinga kwanciya a dakin da yake akwai abuwawa masu hatsari, kamar wuta ko abubuwa masu kaifi.
2- In zai yiwu, kamata yay ka dinga kwanciya a kasa, ba a kan gado ba.
3- Ka tabbatar ka kulle kofofi da makulli.
4- Yana da kyau ka saka kararrawa ajikin kofar dakin da kake kwanciya, yadda idan an ta6a ta za ta yi kara.
A ADDINANCE KUWA, YA KAMATA KA KIYAYE
1 - Kwanciya da Alwala.
2 - Yana da kyau mutum ya karkade shinfida kafin ya kwanta. Domin Aljanu su kan zo, su kwantar da yaransu ko su baza kayansu akan shinfidar mutane. In ka kwanta a kansu sai su shiga jikinka, kamar dai yadda mu ka kawo bayani acikin wannan shudin rubutun
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/aljanar-jarirai-ummul-atfal-aljana-mai.html
cikin bayanin mu mai taken AL-JANAR JARIRAI.
3 - Karanta Ayatal Kursiyyu kafin kwanciya bacci.
4 - Karanta Addu'ar Kwanciya Bacci.
5- An fi so mutum ya fara kwanciya a 6angaren dama, in ya gaji sai ya koma hagun.
ILLOLIN MAGAGIN BACCI
1- Yana iya sa wa mutum ya raunata kansa, kamar faduwa ko bugewa.
2- Yana sawa mutum ya fita cikin tsakar dare ya kama hanya yana tafiya, wanda har matan aure ana samun masu yin haka.
3- Idan magagin baccin mutum yana da alaqa da Aljanu, to suna iya shafar kwakwalwarsa.
4- In Magagin mutum yana da alaqa da sihiri, to wani yana iya yin kwana goma zuwa sati biyu, ko sama da haka, yana cikin magagin bacci.
5- Magagin bacci yana da alaqa da matsalar kwakwalwa ko kuma zai iya haddasa ta.
6- Mai yin dariya acikin magagi ya fi mai yin kuka matsala kuma ya fi wahalar dainawa ko magani.
YADDA ZA A MAGANCE MAGAGIN BACCI.
Maganin Magagi yana da alaqa da abinda ya kawo shi. Idan danka ko wani da kake tare da shi yana magagin bacci mai tsanani ko mai abin tsoro, to yana da kyau ka kaishi asibiti, don a samu shawarar likitoci. In abin bai bari ba ko kuma kana ganin matsalar jinnu ce ko sihiri, to yana da kyau a kai shi wajen mai rukiyyah.
2- Ana iya samun ganyen Na'ana'a da ganyen raihan sai a hada su waje daya, a tafasa da kanumfari da citta da girfa kadan. Sai a tace, a sa zuma. Mai matsalar ya dinga sha.
3- A samu bakin kajiji da jan kajiji da tafarnuwa da habbatus saudaa da habbatur rashad da farar wuta. Sai a hada su waje daya, a daka, a zuba man gelo da man zaitun aciki, a cakuda, sai mai lalurar ya dinga yin hayaki da shi sau biyu kullum.
4- A samu Jan miski da Man juda da misk al aswad da man habbatus saudaa, sai a hada waje daya, mai lalurar ya dinga shafawa a goshinsa, in zai kwanta bacci. In kuma yana yawan fama da ciwon kai to sai ya dinga shafawa sau biyu.
5- A samu ganyen tumfafiya da sassaken katsari da sassaken gawo da sassaken marke, sai a hada su waje daya, a tafasa, mutum yay wanka da ruwan. A yi haka kamar sau biyu ko sau uku.
6- A samu ruwan zamzam kofi daya, ma'ul wardi cokali daya, ma'ul khal cokali daya, ma'ul jinni cokali biyu, sai mutum ya dinga sha, kullum sau daya. In kuma mutum yana da olsa sai a cire ma'ul khal din.
7- A samu ruwa, a zuba acikin kwarya, sai a zuba ganyen magarya da ganyen za'afaran, a tofa ayoyin rukiyyah aciki. Mai lalurar ya dinga sha, yana shafe jikinsa.
A dinga kula, wajen hada magani yana da kyau adinga neman shawarar kwararru, kamar wajen hadawa yaro magani ko mace mai ciki ko kuma maganin da ba ka san adadin da ake shan sa ba.
Idan ka gwada hanyoyin da mukay bayani ba a dace ba, to ka je asibiti ko wajen masu rukiyyah.
Karanta cikakken bayani akan yadda ake hada magungunan da suke kona Aljani da kashe shi acikin wannan shudin rubutun http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/yadda-ake-hada-magungunan-aljanu.html .
Za ka iya sauke Application din mu, wanda za ka iya samun dukkan rubututtukanmu a wayarka, kawai shiga wannan shudin rubutun, sai ka danna download
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/yadda-ake-hada-magungunan-aljanu.html .
Ko ka biyo mu a facebook ta nan fb.me/tarbiyyahislamiyyah3
Allah Ya sa mu dace.
Daga shafin Bashir Halilu mai rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment