ASIRIN HANA HAIHAUWA
ASIRIN HANA HAIHUWA
Abu ne sananne cewa akan iya yiwa namiji ko mace sihiri, domin ahana mutum haihuwa, ko mace ta dinga yawan yin 6arin ciki, da dai sauransu.
A wannan lokaci za muyi bayani ne insha Allahu akan alamomin da mutum zai gane cewa matsalar haihuwarsa tana da alaqa ne da sihiri ko jinnu ko kuma ba ta da alaqa da su.
Kafin nan, ga wadansu dalilai na dabi'a, wadanda suke hana daukar ciki, koda kuwa babu asiri ko Aljani a tare da mutum.
ABUBUWAN DA KE HANA SAMUN CIKI
1- ‘Kan‘kantar gaban namiji, idan ya kasance ba ya iya kaiwa har bakin mahaifarta.
2- ‘Karancin ruwan namiji, ta yadda ba shi yawan da zai iya gangarawa har inda ake so ya je.
3- Fitar jinin haila mai yawan gaske, wanda kan iya wanko abinda ke cikin mahaifar.
4- In mace tana rub-da-ciki bayan gama saduwa, hakan zai sa dukkan abinda mijinta ya zuba mata ya dawo, ba zai shiga mahaifarta ba.
7- Damuwa mai tsanani ko rashin kwanciyar
hankali gamace.
8- Yin allurar 'planning' ko shan maganin gargajiya na hana haihuwa ba tare da qa'ida ba, yana iya janyo tsayawar haihuwa gaba daua.
9- Ciwon sanyi ko Sabara wanda aka fi sani da suna 'Infection', idan yay muni ya kan iya hana mace daukar ciki ko cikin ya dinga zuwa da matsaloli.
10- Matsalar Aljanin dare wato Jinnul Ashiq ko kuma Asirin hana haihuwa, wanda za mu kawo bayani akansa yanzu.
Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah. Masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
ALAMOMIN SIHIRIN HANA HAIHUWA.
Ta 6angaren namiji:-
1-Rashin sha‘awa sam-sam, ba tare da wata sananniyar matsala ba, kamar Sanyi ko Basir ko Hawan jini ko Ciwon-siga, da dai sauran sanannun cututtuka msu dake sha'awa.
2-‘Kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i, alhali haka kawai kuma yana mikewa. Ki kuma in ka juya sai ya mike, in ka dawo sai ya kwanta.
3-‘Kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum, ya hana shi inzali.
4-Saurin gajiya, yayin jima‘i da rikewar ga6o6i.
5-Jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in
haihuwa, kamar maraina da gaban mutum da duburarsa, yayin jima‘i ko ma haka kawai.
6-Rashin cimma bukatar jima'i, ya zamto mutum dai yana yi ne kawai amma ba abinda yake fahimta.
7- Duk sanda ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka ko ka manta ko kuma ka ji kawai ka fasa, ba tare da wani dalili ba.
8- Da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo
tun kafin ka fara.
9- Komawar gaba da maraina su shige ciki, su ki fitowa, a lokacin da shiga dakin uwargida, in ka fito kuma sai komai ya dawo daidai.
10- Yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar
gaba, a duk lokacinda ka tunkaro dakin matarka.
11- Haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka, kana jin haushinta ko kamar ka saketa, alhali bata aikata ma ka wani zunubi ba.
12- Jin matarka tanay maka wari ko doyi ko ka dinga ganinta a siffa mai abin tsoro.
13- Wani lokacin in mutum ya kwanta da matarsa sai ya ji kamar ba ita ba, kamar ta zama tsohuwa ko ya ji kamar ua fada kwata.
14- A duk lokacinda mutum ya kwanta da matarsa ya kan yi kwanaki yana ciwon kai da 6acin rai, har ta kai ma ba ya son kusantarta.
15. Wani in ya sadu da matarsa da safe, to kafin yamma gabansa ya kumbura ko ya tsatstsage ko ya dinga masa zugi.
16- Mutum zai dinga yawan mafarki yana saduwa da wata mata ko tana wasa da shi ko ya ga ta miko masa jariri.
17- In mutum ya tashi daga bacci sai ya ga gabansa amike, alhali idan zai yi jima'i ba ya mikewa. Alama ce ta cewa Aljana ta zo ta biya bukatarta da shi, yana bacci.
Da dai alamomi da yawa.
Ta 6angaren mace. Idan mace ce aka yiwa sihirin hana haihuwa ko kuma take tare da Aljanin dare, to ga alamomin da za ta dinga gani.
1- Mace za ta dinga yawan ciwon ciki mai tsanani da yin jiri kuma in ta je asibiti za a ce ba a gane abinda yake damunta ba.
2- A duk lokacin da su kay nufin saduwa da mijinta kawai sai ta ga jini ya zo ma ta, in su ka fasa kuma sai jinin ya dauke, za ta ga kullum acikin haka ake.
3- Zai kasance mace tana da sha'awa amma da an zo yin jima'i sai sha'awar ta dauke kuma in ana jima'in ma zafi kawai ta ke ji.
4- Suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba
ma ta ya dinga dawowa, domin Aljanin ba zai bari ya shiga mahaifarta ba.
5- Matsanancin ciwon baya ko kwankwaso, wanda ba ya jin magani kuma an kasa gano kansa.
6- Za ka samu mace tana gujewa mijinta lokacin kwanciyar aure kuma in an tambayeta dalili za ta ce ba komai.
7-Yawan mafarkin wani na saduwa da ita, da siffar mijinta ko kuma da wata siffa daban. Wani lokacin ma mace za ta gani tana mu'amalar aure da ita.
8- Yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da
taron suna.
9- Mace za ta dinga ganin wani a mafarki ya nutsa hannunsa a cikinta ya fizgo wani abu ko kuma ya saka mata wani abu acikinta ko a gabanta. Galibi kuma daga nan sai ta tashi da jini.
10- Yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen
dalili ba, musamman bayan yin mafarkin Qadangare ko namijin dare ko mafarkin danyen nama.
11- Yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.
12- Jin motsi a cikinki, wani lokaci ma har yana dada girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba.
13- Rashin son yin magana da kowa da jin haushin
mutane.
14- Tsanar mai gida haka kawai.
15- Jin wari mara dadi daga gaba da ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen gaba da yawan fitar ruwa mai doyi.
16- Yawan samun matsaloli da suka danganci ciki da qirji da kuma mara.
17- Mace ta dinga jin motsi a tafin qafarta da tafi hannunta kamar kiyashi nay mata yawo.
Da dai sauran su.
.
.
Idan mafi yawan wadannan alamu suka tabbata kuma ba 'a samu haihuwa ba to akwai alamun Aljani ko Sihirin Hana Haihuwa a jikin mutum.
Allah Ya shiga tsakanin na gari da Mugu.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah. Masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci.
Shiga shafinmu na facebook a wanna shudin rubutun, sa ka danna like
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment