ASIRIN HADDASA ZUBAR DA CIKI GA MACE WATO SIHRU ISƘĀƊIL-JANĪN (سِحْرُ إِسْقَاطِ الْجَنِينِ) Daga shafin Bashir Halilu.Lambar waya 08134434846.
Asirin haddasa zubar da ciki, wato sihirin da ake yi domin cutar da mace mai ciki, ta yadda za ta rasa cikin da take ɗauke da shi kafin lokacin haihuwa.
Haka kuma ana kiran wannan sihiri da suna
سِحْرُ إِسْقَاطِ الْحَمْلِ
'sihru isqaɗil hamli' wato sihirin haddasa zubar da ciki. Ko kuma:
سِحْرُ إِهْلَاكِ الْجَنِينِ
'sihru isƙaɗil janiyn' wato sihirin halaka ɗan da ke cikin mahaifa.
Wannan yana cikin abubuwan da wasu malaman da suka yi rubuce-rubuce a kan sihiri suka tattauna, inda suka bayyana yiwuwar amfani da sihiri wajen cutar da mace a lokacin da take da ciki.
Saboda haka, malaman da suka yi magana a kan illolin sihiri sun bayyana cewa sihiri yana iya zama sanadin cutar da mutum a wasu fannoni na rayuwarsa, amma komai yana ƙarƙashin ƙaddarar Allah.
Sheikh Abul Baraa Usama bin Yasin Al-Ma'ani ya yi magana a kan yiwuwar amfani da sihiri wajen cutar da mace a lokacin da take ɗauke da ciki.
A cikin bayanansa game da wannan batu, ya ambaci wasu siffofi da ake zargin masu sihiri za su iya amfani da su, ciki har da lalata ƙwayar halittar da ta samu bayan haɗuwar maniyyin namiji da ƙwan mace.
Haka kuma ya ambaci haddasa zubar da cikin mace bayan watanni uku na ciki.
Duba: bayanan الشيخ أبو البراء أسامة بن ياسين المعاني a kan ruƙiyyar shari'a da nau'o'in sihiri.
NAU'O'IN SIHIRIN HADDASA ZUBAR DA CIKI
1. سِحْرُ إِسْقَاطِ الْجَنِينِ
Sihru Isƙāɗil-Janīn.
Wato sihirin da ake yi domin haddasa zubar da cikin da mace take ɗauke da shi.
2. سِحْرُ مَنْعِ اكْتِمَالِ الْحَمْلِ
Sihru Man'i Iktimālil-Haml.
Wato sihirin da ake yi domin hana cikin mace kaiwa lokacin haihuwa.
3. سِحْرُ تَكْرَارِ إِسْقَاطِ الْجَنِينِ
Sihru Takrāri Isƙāɗil-Janīn.
Wato sihirin da ake zargin ana yi domin mace ta riƙa rasa cikin da take ɗauka a lokuta daban-daban.
ALAMOMIN SIHIRIN ZUBAR DA CIKI
1. نُزُولُ الدَّمِ
Mace mai ciki ta fara zubar da jini ba bisa ƙa'ida ba.
2. آلامُ أَسْفَلِ الْبَطْنِ
Jin raɗaɗi ko matsanancin ciwo a ƙasan ciki wanda aka kasa gano sababinsa.
3. تَكَرُّرُ فَقْدِ الْحَمْلِ
Mace ta kasance tana yawan ɓarin cikin da take ɗauka.
4. نُزُولُ أَنْسِجَةٍ مِنَ الرَّحِمِ
Fitowar wasu ƙwayoyin nama daga mahaifa tare da jini.
5. ضَعْفُ الْحَمْلِ
Rashin daidaituwar ci gaban cikin da ke mahaifa.
6- رُؤْيَةُ اسْتِخْرَاجِ شَيْءٍ مِنَ الْجَسَدِ فِي الْمَنَامِ
Mafarkin ganin wani ko wasu mutane suna cire wani abu daga cikin jikinki.
7- أَعْرَاضُ الْحَمْلِ دُونَ وُجُودِ حَمْلٍ
Mace tana ganin alamomin ciki a jikinta, amma idan ta je asibiti, sai a tabbatar mata cewa babu ciki, kuma an kasa gano ainihin matsalar.
MUHIMMIN BAYANI TA FUSKAR LAFIYA
Zubewar ciki yana iya faruwa saboda dalilai daban-daban na lafiya, kamar matsalolin halittar jariri, cututtuka, matsalolin mahaifa, da sauran matsalolin da suka shafi lafiyar mace. Saboda haka, mace mai ciki da ta fara zubar da jini ko jin matsanancin ciwon ciki ya kamata ta garzaya asibiti domin a bincika ta.
Kada a jingina duk zubewar ciki ga sihiri, domin hakan na iya jinkirta samun maganin da ya dace.
HANYOYIN KARIYA DA MAGANI
Idan ana zargin akwai sihiri, ana iya yin ruƙiyya ta Alƙur'ani da Sunnah, tare da yawaita addu'a da kuma neman magani.
Allah Ya kare mana imaninmu, Ya kiyaye matanmu da 'ya'yanmu, Ya kuma azurta duk masu neman haihuwa da zuriya saliha.
Daga shafin Bashir Halilu, mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments
Post a Comment