ZA MU FARA DARASI KYAUTA DOMIN FASSARA LITTAFIN ASSARIMUL BATTAR FITTASADDI LISSAHARATIL ASHRAR, TA BIDIYO DA KUMA RUBUTU.
Mutane da dama suna tambayata akan in buɗe musu aji na musamman akan 'Yadda ake haɗa magunguna da kuma wasu abubuwa da ke da alaƙa da Aljanu da warware sihiri.
Insha Allahu zan fara kawo muku karatun littafin 'Assarimul Battar', wanda littafi ne sananne da aka wallafashi akan Matsalolin Aljanu da warware sihiri, a bisa tsari mai kyau na Ahlus sunnah wal jama'a.
Zan dinga kawo muku karatun littafin Insha Allahu ta hanyar bidiyo a shafina na tiktok mai suna "Shafin Bashir Halilu" sai kuma in rubuta tarjamarsa a wannan shafin nawa na facebook mai suna "Bashir Halilu".
Ga kaɗan daga abubuwanda littafin ya ƙunsa.
١-تَصْحِيحُ الْعَقِيدَةِ فِيماَ يختَصُّ بِجَانِبِ السِّحْرِ وَالشَّيَاطِينِ .
1. Kyautata akidar Musulmi game da abinda ya ke da alaka da sihiri da aljannu:
٢-الاِ عْتِماَدُ عَلىَٰ الدَّلِيلِ فيِ مَسَائلِ عِلاجِ السِّحْرِ .
2- Dogaro da Alƙur'ani da Hadisi wajen warware mas'alolin sihiri.
٣-كَيْفَ يَقِي الْـمُسْلِمُ نَفْسَهُ وَأَوْلاَدَهُ مِنْ كَيْدِ السَّحَرَةِ ؟
3- Yadda Musulmi zai kare kansa da ƴaƴansa daga sharrin masihirta ko bokaye.
٤-تَعْرِيفُ الْـمُسْلِمِ بِطُرُقِ السَّحَرَةِ وَالْـمُشَعْوِذِينَ لِيَتَجَنَّبَهَا.
4. Yadda Musulmi zai san hanyoyin aikin sihiri da bokaye domin ya guje su.
٥-تَعْرِيفُ الْـمُسْلِمِ بِصِفَاتِ السَّاحِرِ لِيَحْذَرَهُ، وَلاَ يَذْهَبَ إِلَيْهِ .
5- Yadda Musulmi zai gane siffofin Bokaye (yadda ake gane boka) domin ya guje su, kada ya je wajensu.
٦-تَعْلِيمُ الْـمُسْلِمِ كَيْفَ يُعَالِجُ نَفْسَهُ وَأَهْلَهُ مِنَ السِّحْرِ بَعْدَ وُقُوعِهِ .
6- Ilmantar da Musulmi game da yadda zai wa kansa da da iyalansa maganin sihiri idan an yi musu.
٧-تَعْلِيمُ الْـمُسْلِمِ كَيْفَ يَقِي نَفْسَهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْعَينِْ وَالْـحَسَدِ .
7- Koyarda Musulmi yadda zai tsare kansa da iyalansa daga sharrin Kambun ido da hassada tun kafin ya same su.
.-تَعْلِيمُ الْـمُسْلِمِ كَيْفَ يُعَالِج نَفْسَهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْعَينِْ وَالْـحَسَدِ بَعْدَ وُقُوعِهِمَـا.
8- Koyarda Musulmi yadda zai warkar da kansa da iyalansa daga Kambun ido da hassada bayan sun faru.
٩-إِبْطَالُ سِحْرِ السَّاحِرِ أَثْنَاءَ الْقِيَامِ بهِ .
9- Ɓata sihirin mai sihiri a lokacin da ya ke tsakiyar aikata shi.
Da sauran dukkan darussa da ke cikin littafi.
A tura wannan saƙo ga jama'a domin masu bukatar samun ilimi a wannan fanni su amfana.
Lambar waya ta 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment