SON ZUCIYAR ƳAN BID'A
SON ZUCIYA KENAN
* Har da masu kwanan Dala'ilu da masu kwanan Mauludi ake cewa bai kamata ayi Tahajjud da loud speaker ba, wai ana hana mutane bacci.
* Malaman da ke ɗiban ƴan mata su ta fi da su maƙabarta suna tafiya suna kaɗe-kaɗe da rawa da waƙe-waƙe, su ne ke cewa haramun ne mace ta fita sallar Tahajjud, wai mata kamata yay su zauna a gida. Alhali acikinsu har da masu ɗiban mata su fita tattaki, suna kwana a kan hanyoyi da cikin firamare.
*Masu cewa haramun ne mace ta fito tana tafsirin Alqur'ani sai dai ta yi wata mata kawai, wai saboda muryar mace tsaraici ce, su ne dai suke shirya mauludi da sauran bukukuwan addini, su kira mata suna yi musu wake-waken maulidi da kiɗa da rawa da kirari da sunan bege, kuma cikin mawaƙan na su har da matan aure.
Wannan son zuciya kenan. Ya Allah Ka raba mu da son zuciya.
Comments
Post a Comment