CIGABA DA AYYUKAN ALKHAIRI BAYAN RAMADAN.
Bayan Watan Ramadhana akwai sauran ayyukan alkhairi.
Wasu Malaman suna ganin cigaba da ayyukan alkhairi bayan shigewar Ramadhana tamkar wata alama ce da ke nuna cewa Azuminka da sauran ayyukan alkhairi da ka gabatar acikin watan sun karɓu.
Ga wasu ayyukan alkhairi da za mu lura da su domin cigaba d samun fa'ida daga ayyukan alkhairi da mu ka koya a watan Ramadana.
1- Yin Azumin sitta shauwal.
Wanda yai Azumin watan Ramadana sannan yai Azumin kwana shida acikin watan da ke bin Ramadana to za a ba shi lada kamar ya yi Azumin shekara guda ne. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya faɗa.
"من صام رمضان ثم أتبعه سة من شوال كان كصيام الدهر".
2 - Yin Azumin kwana uku acikin kowane wata. Ya zamto kowane wata in ya kama za ka zaɓi kwana uku ka yi Azumi acikinsa. An fi so ya zama ranekun 13 da 14 da 15 na kowane wata.
أيام البيض (الثالث عشر والرابع عشر والخامس عشر من الشهر العربي) هي الأفضل.
3- Ƙiyamul laili.
Ka daure ka cigaba da sallolin nafila acikin dare kamar yadda ka saba yi a watan Ramadana. Kamar Yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce
(وَمِنْ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَكَ عَسَى أَنْ يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَاماً مَحْمُوداً).
4- Karatun Alƙur'ani.
Cigaba da yawaita karatun Alƙur'ani mai girma kamar yadda ka saba a Ramadhan. Domin Manzon Allah (SAW) ya ce "Ku karanta Alƙur'ani, domin zai zo ranar Alƙiyama yana ceton masu karanta shi".
( اقرءوا القرآن فإنه يأتي يوم القيامة شفيعا لأصحابه ) خرجه مسلم في صحيحه.
5- Yawan tuba da yawaita Istigfari. Domin Allah Yana ƙarawa mutane arziƙi da ƙarfi kuma yafe musu zunubansu idan suna yawaita tuba da istigfari.
6- Yin ayyuka na gari waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki Ya ke so kamar sadaka da taimakon addini da kuma nisantar aikata saɓo.
Allah Ya sa mun yi Azumi karɓaɓɓe kuma Allah Ya taimake mu wajen cigaba da ayyukan alkhairi har bayan Ramadan.
Daga shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment