LITTAFIN CUTUTTUKAN MATA DA MAGUNGUNANSU. WALLAFAR BASHIR HALILU. LAMBAR WAYA 08162600700, 08134434846.

CUTUTTUKAN MATA DA MAGUNGUNANSU
ABUBUWAN DA KE CIKI
1- CIWON NONO GA MATA
    i) Yadda ake kamuwa da ciwon nono.
   ii) Alamomin ciwon nono. 
  iii) Rikagafin ciwon nono. 
   iv) Yadda ake magance ciwon nono. 
   v) Gyaran nono. 

2- GOYON CIKI. 
   i) Alamomin samun ciki. 
   ii) Abubuwan da ya kamata a yi idan an samu ciki. 
   iii)  Abubuwan da ke kawo zubewar ciki. 
   iv) Rikagafin 6ari ko zubewar ciki. 
   v) Abubuwan da ke taimakawa wajen samun ciki. 
   vi) Abubuwan da ke hana samun ciki. 
   vii) Matsalolin da ke faruwa bayan zubar da ciki ko 6arin ciki.
   viii) Abubuwan da ke sa matsala ta biyo bayan zubewar ciki. 
   ix) Yadda ake magance wannan matsala. 
   x) Shawarwari. 

3- BAYANI AKAN JININ AL'ADA (JININ HAILA)
   i) Asalin jinin haila. 
   ii) Yadda ake bambance jinin haila da jinin cuta. 
   iii) Abubuwan da ke sa jini ya zo ga mace ba bisa ka'ida ba. 
   iv) Yadda mace za ta gane ta samu tsarki daga jinin haila ko nifasi. 
   v) Karin bayani. 
   vi) Abin lura. 
   vii) Rigakafin matsalolin haila. 
   viii) Abubuwan da ke taimakawa jini ya zo ga wacce ba ta yi. 
   ix) Abubuwan da ke sa wa jini ya dauke ga wacce ya zo ba bisa ka'ida ba. 
   x) Yadda ake magance matsalolin zuwan jinin haila. 

4- RASHIN SHA'AWA
   i) Abubuwan da ke kawowa mata rashin sha'awa. 
   ii) Rigakafin rashin sha'awa ga mata. 
   iii) Illolin rashin sha'awa ga mace. 
   iv) Maganin rashin sha'awa. 

5- CIWON SANYI
   i) Abubuwan da ke kawowa mata ciwon sanyi. 
   ii) Yadda mace za ta gane ta kamu da ciwon sanyi. 
   iii) Rigakafin ciwon sanyi ga mace. 
   iv) Yadda ake magance ciwon sanyi. 

6) ILLOLIN MASTURBATION
   i)  Wasu daga illolin masturbation. 
   ii) Hanyoyin rabuwa da masturbation. 
   iii) Magance matsalar masturbation. 
   iv)  Magunguna ga mai aure. 

7- MAGUNGUNAN ASIBITI GA MATA. 
   i)  Tasirin magungunan asibiti ga mata. 
   ii) Amfanin magungunan asibiti ga mata. 
   iii)  Illolin magungunan asibiti ga mata. 

8- MAGUNGUNAN GARGAJIYA GA MATA. 
   i) Tasirin magungunan gargajiya ga mata. 
   ii)  Amfanin magungunan gargajiya ga mata. 
   iii)  Illolin magungunan gargajiya ga mata. 

CIWON NONO GA MATA.
 Wato Sanqaran Mama ko kuma Kansar mama. 
MA'ANAR:- ciwon nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wandanda ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya.
YADDA AKE DAUKAR CIWON 
Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono. 
1- Shekaru ko tsufa. 
    Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono. 
2- Sinadarin 'iyistirogen', idan yay yawa ajikin mace.
3- Fara jinin al'ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya. 
4- Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al'ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono.
5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su iya kamuwa da ciwon nono.
6- Jinkirin haihuwa. 
Idan mace ta dauki shekaru da yawa da aure ba ta samu haihuwa ba za ta iya kamuwa da ciwon nono.
7- Girman jiki.
   A binciken likitoci, mace mai tsawo da mace mai kiba, sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon nono, musamman masu tarin kitse a jikinsu ko a kugunsu.
8- Gado. 
  Idan iyayen mace suna fama da ciwon nono, to itama zai iya yiwuwa ta yi gado.
9- Idan nonon mace guda daya ya ta6a yin ciwo, to zai iya yiwuwa dayanma ya kama ciwo daga baya.
10- Matar da aka ta6a cire mata tsiro a mamanta, yana da kyau ta dinga zuwa asibiti  tana samun shawarwari don gudun kamuwa da ciwon nono daga baya.
ALAMOMIN CIWON  NONO
1) Canjin yanayin girman nono.
 Haka kawai ki ga nononki yana kara girma ko ya yamutse, ba tare da wani dalili ba.
2) Jin kullutu acikin nono.
   Za ki ji kamar wasu abubuwa suna tsirowa daga nononki, har suna kara girma.
3) Canjin kalar fatar nono. Za ki ga fatar nonon tana komawa kamar yalo-yalo ko jaja-jaja ko wata kala daban.
4) Canjin kalar fatar kewayen nono (nipple), ki ga fatar wajen ta yi jajawur.
5) Kan nonon mace (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai kuma yana ciwo.
6) Fitar wani ruwa kamar ruwan ciwo haka kawai daga nonon mace. Ba sai lallai matar aure ba, ko da budurwa ce.
7) Radadi da ciwo mai zafi akan nonon da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.
8.) Kumburin hammata tsakanin allon kafada zuwa sashin nonon.
9- Jin ciwo mai tsanani idan kika matsa nonon.
RIGAKAFI YA FI MAGANI.
Yadda za ki gane kina dauke da cuta a mamanki, tun kafin ya fara ciwo.
1- Za ki ga wani dan tsiro akan nononki amma ba ya ciwo kuma ba ya zafi, wasu matan ma suna dauka kamar wani abin ado ne.
2- Yana iya farawa da jin ciwo kadan a maman.
3- Ya kan iya farawa da ciwo ko kaikayi a fatar da ta zagaye kan nonon.
4- A wasu matan kuma, kan nonon ne yake fara shigewa ciki, za ki ga kan nono daya ya shige ciki, dayan kuma ba haka yake ba. Likitoci suna ganin idan har kan nonon ya lo6a ciki, to cutar ta fara ha6aka kenan.
5- Wasu ya kan fara da fitar wani ciwo a karkashin maman, wanda zai dinga kara yawa, yana kewaye kasan maman kuma ba lallai ne ya zama yana yin zafi ba.
Karin bayani.
★ Idan akayi sake ba a dauki mataki da wuri ba, zai iya yiwuwa ciwon yayta  ci daga ciki, har ya taso fatar maman, ya zama gyambo wanda yake fitar da jini da ruwa mai wari.
★ Zai iya yiwuwa ciwon nono ya fara ta saman fatar, yana kuma iya farawa daga can cikin nonon, don haka da an ji canji to a gaggauta tuntu6ar masana.

YADDA AKE MAGANCE CIWON NONO TA HANYAR MAGANIN GARGAJIYA. 
1- Sakiya. Idan nonon mace ya kumbura har ya ja ruwa, ana iya yin sakiya, wato a yi amfani da kayan aiki wajen huda ruwan ya tsiyaye. Kwararrun masu magunguna ne kadai suke yi. 
2- Idan nonon mace yana kaikayi ne, sai a hada Man Zaitun da Man Hulba, ta dinga shafawa. 
3- Wacce nonon yake mata ciwo da radadi kuma sai ta samu Garin Ararra6i, ta dinga jika cokali daya, tana sha, kullum, har zuwa kimanin sati daya zuwa biyu. 
3- Idan kari ne acikin ciwon, sai a samu Garin Sabara cokali daya, garin Bakin Kajiji rabin cokali, a jika a ruwa, ta sha. Tsallaken kwana daidai, ta sha kamar sau biyar. 
Amma dai mafi kyau shi ne aje asibiti ko wajen kwararren mai hada magungunan gargajiya.
GYARAN NONO. 
Kara girmansu, cikowarsu, mikewarsu, kara musu sheki da kuma hana su zubewa. 
Sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi.
1) Wacce nononta ya zube a sakamakon shayarwa, ko kuma su ka zube sakamakon rashin samun abinci mai dauke da sinadaran da ke gina nono,  sai ta yi wannan hadi. 
1- Habbatussauda
2- Hulba
3- Alkama
4- Gyada
5- Ridi ko Kantu
6- Danyar shinkafa
7- Busasshen karas. 
     A hada su waje daya, a markada ko a nika. Sai a dinga diban cokali biyu a sha da madara, kullum, safe da yamma. 
2) Masu karamin nono kuma
Wacce kuma ta ke asali nononta dan karami ne amma tana so ya kara cikowa, ya taso sosai, to sai ta yi wannan hadi. 
1- Albasa madaidaiciya
2-  Zuma
3- Garin gero
4- Madara
Yadda za a hada. 
Ki samu albasa madaidaiciya, ki yanyanka, sai ki
saka a tukunya da ruwanki ta tafasa shi sosai
har sai ruwan ya koma baki, sai ki juye ruwan ki
sami zumar ki mai kyau, garin gero ludayi daya,
madara ta gwangwani daya na ruwa sai ki juye
su kan ruwan tafasasshe albasa nan ki sha .
Amma fa karki bari ya kwana baki shanye ba.
Wannan hadine da zai gyara miki nono
3) Wacce ta ke so nononta yay kyau da laushi da sheki. 
Idan Ana so nono yayi kyau yayi laushi da santsi
da girma sai ayi wannan hadin.
1- Aya
2- Gyada
3- Ayaba (plantain)
4-Alkama
5- Madara
Yadda za a hada. 
Zaki wanke ayarki, sai ki hada da gyadarki ki
markada su, ki tace, dama kin yanyanka ayabarki, kin busar, kinyi gari da ita, kin tankade sai ki rikka diban garin plantain din kina hadawa da ruwan
ayaba gyadarki kina sa madara ta ruwa kina sha. 
Zai gyara miki nono domin wannan hadi ne wanda sai kin sha mamaki. 
4) Mai shirin shiga daki. 
   Idan za ay bikinki amma kina so nononki ya cicciko, ya tsaya, kara kyau, sai kiyi wannan. 
A samu garin Hulba, sai ki tankade, yay laushi sosai. Sai ki dama ta da ruwan dimi, ki shafe nonon, ki saka rigar mama wacce ta matse ki. Da safe sai kiy wanka da ruwan dimi, ki shafe su da man hulba. Kiyi haka kamar sau uku zuwa biyar ko bakwai. Ki kuma dinga dama hulba kina sha cokali biyu kullum da madara ko zuma. 
Nonuwa za su cicciko tare da yi kyau kuma jikinki zai kara kyau da kumari. 
Daga Dr.  Bashir Halilu. 
Mai Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
  Sakataren Hadaddiyar Kungiyar masu magunguna na Musulunci da na Gargajiya ta Nigeria, mai suna ITMCA. 
Lambar waya 08162600700.

SAMUN CIKI DA RAINON CIKI. 
Wato yadda mace ta ke samun jariri ko dan-tayi a cikin mararta har ya girma zuwa haihuwa. 
Mafi yawa mata suna haihuwa ne bayan wata tara da samun ciki, wasu kuma suna haihuwa a wata bakwai. Amma dai haihuwa na iya farawa daga wata shida zuwa sama, wani lokacin ma ta kan tsallake wata tara. Mata su kan ji sauye-sauye ajikinsu idan ciki ya shige su musamman idan ya kai wani dan lokaci.
YADDA MACE ZA TA GANE TA SAMU CIKI. 
1- Batan wata. Wato mace ta ga al'adarta ba ta zo ba kamar yadda ta saba. 
2- Tashin zuciya, musamman da sassafe. 
3- Amai, a wasu lokutan. 
4-Saurin gajiya idan an yi wani dan aiki. 
5- Yawan kasala. 
6- Yin jiri idan an zo mikewa. 
7- Wasu matan suna yawan yin tusa ta gaba ko ta baya.
Idan ciki ya kai kamar wata uku kuma sai a fara ganin alamu kamar haka
7- Girman ciki.
8- Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari. 
9- Ciwon baya ga wansu matan. 
10- Ciwon kirji, wato zafin kahon zuciya. 
11-  Kwarnafi saboda ‘acid’ din ciki na tasowa kirji. 
12- Sai kuma a fara samun duhun fuska ga wadansu matan
13- Fitowar zane a fatar ciki wato Nankarwa. 
14-Budewar hanci a wasu matan. 
15- Nauyi ko ciwon mama. 
16- Wasu matan jikinsu yana kara kyau mai ban kaye. 
Ba dole ba ne kowace mace ta samu dukkan wadannan alamu, amma kusan rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamun. 
ABUBUWAN DA YA KAMATA A YI IDAN AN SAMU CIKI
Idan ya tabbata kina da ciki, sai ki dinga kula da wadannan shawarwari masu zuwa a kasa. 
1- Zuwa kar6ar magani, irin na masu ciki da kuma duba lafiyarki da ta jaririnki. 
2- Duk wani magani da za ki sha, idan kina da wata lalura, to ki gayawa mai maganin cewa kina da ciki, kafin ki fara shan maganin. 
3- Ki yi rikagafin cututtukan da ke wahalar da masu ciki, tun kafin cikinki ya fara tsufa, kamar su typhoid, malaria, mura da dai sauransu. 
4- Idan ta kama za ayi miki aiki akan wata lalura daban, kamar hakori misali, to ki tabbatar kin sanar da mai maganin cewa kina da ciki. 
5- Ki tabbatar kina kar6ar magunguna masu dauke da sinadaran gina jiki, irin wadanda ake baiwa masu ciki, domin cin abinci mai gina jiki kadai ba ya wadatar da masu ciki. 
6- A dinga samun isasshen bacci, in da hali ya zama ana iya baccin awa 7 zuwa 9, a rana. 
7- Motsa jiki da sauran ayyuka. Idan cikinki yana kasa da wata hudu ana so ki guji daukar abu mai nauyi da aiki mai wahala kamar jan ruwa a rijiya, yin daka ko surfe da dai sauransu. Amma idan cikinki ya kai watannin haihuwa, kamar wata bakwai zuwa sama, ana so ki dinga motsa jiki, kamar yin tafiya a kasa, wanki da wanke-wanke da dai sauransu. 
8- Saduwa da iyali. 
Saduwa tana da matukar amfani ga mai ciki, idan cikin ya dan fara girma, kamar wata hudu misali, domin yana taimakawa wajen kara samun lafiyar mai ciki da jaririnta da kuma yin haihuwa cikin sauki. Amma dai a tabbatar mace ba ta da matsalar rashin kwarin mahaifa ko wata lalura wacce za ta sa yawan saduwar ya kawo matsala. 
9- Gina jiki. 
   Ana so mai ciki ta dinga cin abubuwan da za su gina mata jiki, kamar dafaffen kwai, kifi da dai sauransu amma a kula, narka uwar kiba yana baiwa mai ciki matsala, domin danta zai yi kato sosai, hakan kuma zai iya kawo matsala wajen fitowarsa lokacin haihuwa, ita kuma zai kawo mata kasala da nauyin jiki. 
10- Ba a so mai ciki ta dinga shan taba ko shisha ko giya da sauran kayan maye. Masu cikin da suke shaye-shaye suna iya haifar yaran da nauyinsu bai kai ba ko kuma yara dakikai, marasa iya gane karatu idan sun girma. 
11- A guji shan magungunan wankin mara lokacin da ake dauke da ciki da kuma magungunan da suke tunzura nakuda, sai dai bisa wata ka'ida. 
12- Kwanciya rigingine ga mai ciki kan iya janyo mutuwar jaririnta a ciki. 
13- Ki guji duk abinda zai iya sa miki damuwa ko 6acin rai yayin goyon ciki.
14- Ana so mai ciki ta dinga ci da kuma shan abubuwa masu kara jini a jikin mutum. 

ABUBUWAN DA KAN IYA KAWO ZUBEWAR CIKI. 
1. Aikin karfi wanda ya wuce kima, musamman lokacin da ciki bai yi kwari sosai ba. 
2- Saka matsatstsun kaya da wasu masu cikin suke yi. Hakan kan na iya sawa ruwan da jaririn yake ciki ya ragu, ta sanadin hakan kuma cikin na iya zubewa. 
3- Shan magunguna ba bisa ka'ida ba da kuma shan kayan maye 
4- Tsufa ko yawan haihuwa na kawo wannan matsala ta yin 6ari, domin a duk lokacin da aka haihu mahaifa na kara rauni, haka sassan jikin da ke taimakonta.
4.  Rashin samun wadataccen abinci ga mai ciki, ko kuma abinci mai gina jiki. 
5- Rashin kwarin mahaifa. 
6- Illar mummuna wacce ciwon sanyi yake haifarwa.
7- Gur6ataccen muhalli. Yawan zama ko aiki a wajen da yake akwai kara mai yawa ko tashin wari da abubuwa masu guba. 
8- Ciwon suga wanda aka kasa shawo kan sa. 
9- Wasu matsalolin kamar na iska ko sihiri.
RIGAKAFIN BARI KO ZUBEWAR CIKI
Abubuwan da ya kamata masu ciki su dinga ci. 
1) Magungunan Gargajiya da ke kara jini ajikin mutum, kamar Ganyen Auduga, Ganyen So6arodo, ko a ce Yakuwa, Ganyen Zamarke, ana kuma kiransa Kalambu, Saiwar Gwandar_daji, tana kara yawan jini kuma tana rage hawan jini, Giginya, wato tsokar Giginya din, Saiwar Kargo, Ganyen Geza, 'Ya'yan Kanya, Sassaken `Baure, Saiwar Goruba, Qamsuwa. Baki dayanta ake amfani da ita, Goga_masu. Shi ma baki dayansa ake amfani da shi,  don kara jini. 
2) Magungunan da ke rage radadin ciwo, kamar 
Ganyen idon Zakara, ganyen Turaren turawa, ganyen gwanda, sassaken Ararra6i, Dan Tamburawa, Raidore. 
3) Abubuwan da ke gina jiki, kamar Dafaffen kwai, kifi, naman kaza, wake, tafasa, tsidau, da dai sauransu. 
4) Abubuwan da ke kara karfin garkuwar jiki, kamar Zogale, Mirammiya, Si'itir, Zuma, Habbatus saudaa. 
5) Abubuwan da ke saukaka haihuwa, idan watan haihuwa ya kama, kamar Kuka, karkashi, ku6ewa, Hulba, Sana-makiy, Na'ana'a, Shajaratu Maryam, da dai sauransu. 
    Amma dai yana da kyau a nemi shawarar masani lokacin da za ayi amfani da wadannan abubuwa ko kuma a kar6a daga wajen kwararren mai hada magani.
ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA WAJEN SAMUN CIKI
1- Mace ta sa wani abu mai kamshi (kamar farin almiski) a jikin yanki ko auduga ta yi kunzugu da shi.
2- Saduwa lokacin da mace ba ta dade da
gama jini ba, don lokacin mahaifar ta ta na da dumi.
3- Idan mace ta sha nonon taguwa sannan mijinta ya sadu da ita.
4- A cakuda habbatussaudaa da man shanu mace ta dinga lasa lokacin da za ta kwanta, kwana uku.
5- Yin Istigfari yayin jima‘i.
6- A dinga karanta wannan addu'a "Rabbi habliy min ladunKa waliyya" 
Ko kuma wannan
"Rabbi habliy min ladunka zurriyyatan tayyibatan, innaKa Sami'ud du'a'i"
 ABUBUWAN DA KE HANA SAMUN CIKI
1- ‘Kan‘kantar gaban namiji ko kuma zurfin farjin mace, na iya kawo jinkirin samun cikin wani lokacin. 
2- ‘Karancin ruwan namiji, wato ya zamto kwayoyin haihuwarsa ba su da yawan da ake bukata. 
3- Fitar jinin haila mai yawan gaske.
4- In mace tana rub-da-ciki bayan gama
saduwa.
5- Damuwa mai tsanani ko rashin kwanciyar
hankali gamace.
6- Sihirin hana haihuwa da akan iya yiwa mace ko kuma matsalar jinnul Ashiq.
MATSALOLIN DA SUKE FARUWA BAYAN ZUBAR DA CIKI KO BARIN CIKI. 
Idan aka samu matsalar zubewar ciki, to ba cikin kawai ake rasawa ba, akwai matsaloli da zai iya yiwuwa su biyo baya idan ba a dauki mataki ba. 
Sannan wani lokacin idan anyi amfani da wasu abubuwa ne wajen zubarda cikin, su ma suna iya haifarda kwayoyin cuta ga mahaifa. 
To idan mace tay 6ari ko ta zubar da ciki, za ta iya fuskanta wadannan alamomi
1) Zafin jikinta zai karu (zuwa kamar 38oc). 
2) Yawan bugun zuciya, kamar ta buga sau dari cikin minti daya. 
3) Kumburin ciki.
4) ciwon ciki
5) taurin ciki. 
6) Fitar ruwa mai wari ta gabanta. 
7) Jin rashin lafiya ko gajiya sosai. 
8) Zubarda jini fiyeda kima, shima wannan wani damuwa ce ko matsala da take faruwa bayan mace tasamu barin ciki. 
9- Kumburin ciki. Wata cikinta zai kumbura, kamar mai ciki wata hudu. Wata kuma kumburin zai dinga tafiya yana dawowa. 
ABUWAN DA KE SA WA MATSALA TA BIYO BAYAN ZUBEWAR CIKI
1- Zai iya yiwuwa da akwai wata tsoka ta jikin jaririn acikin mahaifa wacce ba ta fado ba, don haka za ta iya ru6ewa a ciki ta haifar da matsaloli.
2- Idan zubar da cikin aka yi ta hanyar shan maganin zubar da ciki, to su magungunan za su iya haifar da illoli ga mahaifa. 
3- Idan an yi amfani da wani abu ne aka ciro jaririn, kamar almakashi misali, to zai iya yuwuwa an yi wa mace rauni ajikinta. 
4- Zai iya zama bakin mahaifa ya kamu da infection, wanda watakila ma shi ne sanadin zubewar cikin. 
YADDA AKE MAGANCE WANNAN MATSALA
1- Idan ya kasance akwai wata tsoka ko wani 6angare na jikin jariri acikin uwa,  to dole sai an fitar da shi sannan jinin da ya tsinke ma ta zai tsaya, haka ma ko da infection ne ba zai warke ba,  sai an cire. 
2- Indai ba wata tsokace ta rage aciki ba to wasu matan jikinsu yana komawa dede a hankali. 
SHAWARA
Ya akamata a  ziyarci masanin harkar lafiya bayan an yi 6arin ciki ko zubarda ciki sannan a dinga cin kayan gina jiki wadanda mu ka ambata.
Daga Dr. Bashir Halilu
Shugaban Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci. 
Sakataren Kungiyar masu Magunguna na Musulunci da na Gargajiya  ta Nigeria, ITMCA. 
Lambar waya 08162600700.

BAYANI AKAN JININ AL'ADA WATO HAILA DA MAGUNGUNAN DA SUKE DA ALAKA DA SHI
Ma'anar jinin haila. 
Shi jinin Haila wani kwan haihuwa ne da mace take dasawa, idan ya hadu da kwan haihuwa na namiji sai su hadu, su zama da. Idan kuma bai samu kwan namiji sun samar da abin halitta ba sai ya lalace ya ru6e, daga nan sai a wanko shi ya fito waje. Galibi mata suna yin jinin haila ne a duk bayan wata guda, wasu matan kuma suna yi fiye da haka ko kasa da haka. 
Bugu da kari shi jinin haila yana wanke duk wani datti da ke mahaifar mace ya kuma fitar mata da shi yayin zubar jinin. 
       Mace tana fara haila ne lokacinda ta balaga. Mata kan iya fara haila daga shekara tara ko sama ko kasa da haka, ya danganta ne da irin abincin da take ci da kuma yanayin wajen da ta ke rayuwa. 
Wasu suna daina haila da wuri idan sun fara tsufa, wasu kuma suna dadewa ba su daina ba. Saidai daukewar haila alamar tsayawar haihuwa ce ga wadda ta tsufa ko kuma alamar shigar ciki ga mai haihuwa. Akan samu lalura kuma tasa haila ta dauke ko tayi jinkiri zuwa wani lokaci. Haka ma Haila na iya daukewa sakamakon amfani da magunguna da za su iya tsayar da ita.
YADDA JININ HAILA YAKE
Wani lokacin jini ya kan zo wa mace kuma ta kasa gane cewa ko jinin Haila ne ko kuma jinin cuta wato istihadha. Wannan ya kan rikita musu lissafi wajen gudanar da ibada da kuma sanin matsayin lafiyarsu.
GA YADDA AKE BAMBANCE JININ HAILA DA JININ CUTA. 
1- Jinin Haila ruwan kasa ne, ba ja ne sosai ba shi kuma jinin cuta za ki gan shi ja ne sosai kamar jinin ciwo. 
2- Jinin Haila yana dan yin wari, za ki ji yana dan wani wari mara dadi amma jinin cuta ba ya wari.
3- Jinin Haila yana fitowa ne da karfi, ma'ana za ki ji kamar ana turo shi ne amma shi jinin cuta a slow yake fita, ba da karfi ba.
4- Jinin Haila ya kan zo da  lalura kamar ciwon mara, ciwon kafa da dai sauransu, shi kuma jinin cuta bai fiye zuwa da lalura ba, saidai wani lokaci ya kan zo da ciwon mara.
5- Jinin Haila yana da kauri sosai, shi kuma jinin cuta ba shi da kauri.
6- Jinin Haila ba ya bushewa, idan ya diga a kasa za ki ga ya ki bushewa amma shi jinin cuta nan da nan yake bushewa.
7- Za ki ga jinin Haila yana kyalli, yana sheki, shi kuma jinin cuta ba shi da kyalli.
8-  Idan mace ta kasa bambance jinin da ya zo mata ta wadannan alamomi, to sai ta samu babbar roba ko bahon wanka, ta zuba ruwa a ciki, ta shiga ciki ta zauna. Idan ta ga yalo ya taso sama to jinin cuta ne amma idan ba ta ga yalo ba to jinin Haila ne.
ABUBUWAN DA KE SAWA JINI YA ZOWA MACE BA BISA KA'IDA BA. 
Ina nufin barkewar jinin cuta ga mace, wanda ba jinin al'ada ba. 
1- Samuwar tsiro ko wani ciwo acikin mahaifa ko a gaban mace, wanda yake zubar da jini. 
2- Shan magunguna ba bisa ka'ida ba. 
3- Jin rauni a cikin gaba ta sanadiyyar faduwa ko bigewa ko kuma fyade ko saka wani abu kamar karfe acikin gaba. 
4- Katsewa ko kuma samun rauni a wata jijiyar jini da ke a cikin gaba. 
YADDA MACE ZA TA GANE TA SAMU TSARKI DAGA JININ HAILA KO NIFASI 
(Nifasi na nufin jinin da yake zuwar wa mace daga lokacin da ta haihu zuwa sanda ya dauke). 
Wasu matan sukan kasa gane cewa sun samu tsarki ko kuma ba su samu tsarki daga jinin haila ba musamman ma idan jinin yana zuwa ne yana dauke musu. 
   To abu mai sauki dai hanyoyin da ake gane jini ya dauke guda biyu ne. 
 1- Tsanewa. Wato idan mace ta ciro auduga ko kuma abinda ta toshe gabanta da shi, sai ta ganshi a bushe ba jini a jiki. To jininta ya dauke kenan.
2- Idan mace ta ga wani ruwa yana fito mata mai garai-garai ko kuma mai kamar an wanke danyen nama, to alamace ta jininta ya dauke, wannan ruwan dauraya ne yake zuwar mata.
KARIN BAYANI
★Koda jini ya zarce kwana goma sha biyar yana zuba, indai ya cika alamomin jinin haila wadanda aka ambata to hukuncin mai haila ne akanta.
★Jinin cuta ba ya hana mace ibada, saidai ana so ta dinga tsaftace jikinta kuma kowace sallah za tay mata alwalarta kamar yadda malamai su kay bayani. 
★Jinin Nifasi ko Jinin biqi da matan da suka haihu suke yi, hukuncinsu daya da jinin haila a wajen ibada.

ABIN LURA
★Matan da samsam ba sa yin Jinin Haila to akwai alamar samun matsala game da haiuwa. 
★ Matan da suke ciwon mara mai tsanani lokacin al'ada yana da kyau su nemi magani.
★ Idan jinin mace yana zuwar mata bakikkirin, ma'ana kalarsa ta zama baki maimakon ruwan makuba, to itama tana da matsala.
★ Haka wadda take yin Haila mai doyi ko kuma wari sosai, to itama ta nemi magani.
★ Idan jini yana zuwa ya daukewa mace, kamar yau ya zo, ya dauke, gobe ya dawo. To lallai ita ma ta nemi magani.
★ Idan wani ruwa mai wari yana zubarwa mace mai kamar koko, to itama ta nemi maganin sanyi.
   Wasu daga cikin wadannan cututtuka matsalar Sanyi ce take kawosu wato Infection, wasu kuma matsalace ta jinnu.
RIGA-KAFIN MATSALOLIN HAILA
Wacce take gudun faruwar matsala game da yanayin zuwan jinin al'adarta, sai ta dinga lura da wadannan shawarwari
1- A dena shan miyar yauki lokacin da ake cikin jin haila, kamar Ku6ewa, Karkashi, Kuka da dai sauransu. 
2- A guji zama a gaban fanka ko A.C.
3-  A kaucewa saduwa ko saka wani abu acikin gaba ko cusa magunguna lokacin zuwan jini. 
4- A dinga canja auduga ko tsumma akan lokaci, kada a bari har jiki ya fara bugawa. 
5- Ana so mace ta dinga amfani da ruwan dimi da kuma turare mai dadi, kamar farin miski da dai sauransu. 
6- Shan ruwan dimi na taimakawa jini fita cikin sauki lokacin al'ada. 
7- A guji shan kayan sanyi ko yawan amfani da kaya masu sanyi lokacin zubar jini. 
ABUBUWAN DA KE TAIMAKAWA JINI YA ZO GA WACCE BA TA YI
1- Mace ta karya da Mur, kafin ta ci komai.
2- Shan ruwan zafi ko mai dumi.
3- Yin ‘kunzugu da Ayaba.
4- Hadiyar Habbul kharu', kwaya daya 
ABUBUWAN DA KE SA JINI YA DAUKE IDAN YA ZO BA BISA KA'IDA BA
1- A jika Kwan makera, sai mace ta sha. 
MAGANCE MATSALOLIN ZUWAN HAILA
1- Wacce take tsananin ciwon mara lokacin zuwan jini, sai ta samu Tuffah-khal, ta dinga zuba rabin murfi a ruwa rabin kofi, ta sha da safe, da yamma ma haka. Saidai tuffa khal yana da tsami. 
2- Wacce Jininta yake mata wasa, wato yana daukewa, yana dawowa, sai ta samu garin Hulba, ta tafasa rabin cokali, ta sa zuma, ta sha. Ta yi haka sau daya ko biyu ko uku, a duk wata daya. Hulba tana da gafi, kamar dandanon waken suya take. 
3- Wacce sam-sam ba ta yin jinin al'ada, sai a samu Kwan-makera, ta jika a ruwa, ta sha. Kwan makera ba shi da dandano. 
4- Wacce ta ke al'ada bakikkirin mai wari, ita ma ta dinga shan Hulba rabin cokali.
   Saidai zai fi kyau aje asibiti ko a ziyarci kwararren mai maganin gargajiya, don ya hada abindabya fi dacewa da yanayin mara lafiyar. 
Daga Dr. Bashir Halilu mai Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. 
Sakataren Kungiyar masu magunguna na gargajiya dana Musulunci ta Nigeria, wato ITMCA. 
Lambar waya 08162600700.

RASHIN SHA'AWA GA MATA DA ABUBUWAN DA KE KAWO SHI DA ILLOLINSA DA RIGAKAFINSA DA KUMA YADDA AKE MAGANCE SHI. 
In aka ce rashin sha'awa ga mace, ana nufin samuwar wani ciwo ko wani yanayi da yake hana mace jin dadin kwanciyar aure ko kuma rashin son kwanciyar gaba daya. A wasu lokutan ma ya kan haifarwa da mace jin ciwo ko fitar wasu abubuwa marasa dadi daga jikinta bayan kwanciyar aure. 
ABUBUWAN DA KE KAWOWA MACE RASHIN SHA'AWA. 
1- MATSALOLIN MARA DA MAHAIFA
 Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura, na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.
Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje acikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen acikin al'aura ba,  saidai su ce su na jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda gugar da ake musu yayin saduwa, sai wurin ya zama rauni.
2- BUDEWA
Budadden gaba ga mace na sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu samu gamsuwa ba da kyau, sannan macen baza ta iya jin 'kololuwar dadi ba shi ma namijin haka saboda rashin haduwar fata da fata yadda ya kamata. 
3- KACIYAR MATA
 Idan aka samu matsala wajen yiwa mace kaciya, ya zamanto an yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma.  Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i, domin kuwa beli shi ne matattarar jin dadin jima'in mace. 
4- MAGUNGUNA 
Yin amfani da magunguna ba bisa ka'ida ba. Yawaita shan magunguna barkatai kan iya ragewa mace sha'awa ko kuma ya sa ta dauke baki daya. Wani lokacin kuma ko da bisa ka'ida aka sha maganin to zai iya yiwuwa daga cikin side effect dinsa shi ne yana dauke sha'awa zuwa wani lokaci. 
6- RASHIN ABINCI MAI GINA JIKI. 
Abinci mai gina jiki na nufin abincin da ke dauke da sinadaran da jikin mutum ke bukatarsu, to shi ne mai gina jiki a wajensa. Idan mace ba ta samun ingantaccen abinci to za ta iya samun matsalar rashin sha'awa sosai. 
7- RASHIN FAHIMTAR YANAYIN MACE
Wata matar ba wai sha'awar ce ba ta da ita ba, a'a. Ita kanta ba ta fahimci abinda zai sa mata sha'awar ba ne, shi ma mijinta bai fahimce ta ba, sai a tafi a haka, a matsayin ba ta sha'awa. 
8- WASA DA GABA
  Idan mace na wasa da farjinta (istimna'i) da yatsa ko wani abu da take sakawa, to zai dauke mata sha'awa kuma zai lalata ma ta gabanta da mahaifarta. 
9- MATSALAR AL-JANU
    Wata matar ana iya samun shaidanin Aljani ya shafeta, saboda ya ga yana sha'awarta. Sai ya dinga kishi da mijinta, don haka sai ya saka mata rashin sha'awa, saidai in shi ya zo yana saduwa da ita a mafarki ta dinga jin dadi. 

RIKAFIN RASHIN SHA'AWA GA MATA
Matar da ke gudun ta kamu daa fadawa matsalar rashin sha'awa, sai ta dinga lura da wadannan shawarwari masu zuwa a kasa.
1- CIN ABINCI MAI KYAU
    In da hali, yana da kyai mace ta dinga cin abubuwa masu gina jiki kamar Yoghourt, Hanta, Kwai, Zuma, Dabino, Aya, Gyada, Kankana, Ayaba da sauran abinci mai gina jiki. Duk matar da ke cin irin wadannan abubuwa to kullum cikin nishadi da sha'awa ta ke. 
2- FAHIMTAR YANAYIN JIKI. 
Kowace mace tana da sha'awa amma kowacce da akwai wajenda anan ne shawarta ta fi karfi. Wata sha'awarta a tafin hannunta take, wata a kirjinta, wata a mazaunanta, wata a cinyoyinta, wata a le6enta, wata a wuyanta, da dai sauran sassan jiki. Ya kamata mace ta yi kokari ta gane babban wajenda in mijinta ya ta6a ma ta take jin dadi, to sai tay masa bayani. 
3- AIKA DAN AIKE
   Yin wasanni kafin kwanciyar aure. 
ILLOLIN RASHIN SHA'WA GA MACE
1-Yana iya kawo rashin jituwa tsakaninta da mininta. 
2- Ba lallai ta samu cikakkiyar lafiya ta murmure irin yadda matan aure suke yi ba, matukar ba ta samun kwanciya saboda rashin sha'awa.
MAGANIN RASHIN SHA'AWA. 
A samu Garin Marke da Garin Ararra6i, kowanne cokali biyu, sai ki zuba ruwa kamar kofi uku, ki dora a wuta, ki sa wutar kadan-kadan. Idan ya tafasa sai ki sauke, ki tace, ki sa zuma. Ki sha maganin tsawon kwana biyu, kullum safe da yamma.
Za ki sha mamaki, insha Allahu. 
Amma dai yana da kyau a ziyarci asibiti ko wajen kwararren mai hada maganin gargajiya don ya hada miki wanda zai dace da yanayinki. 
Daga Dr. Bashir Halilu. 
Shugaban Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci. 
Sakataren Kungiyar masu magungunan gargajiya da na Musulunci ta Nigeria, ITMCA             Lambar waya 08162600700

CIWON SANYI
Ciwon Sanyi na mara, ga mace, shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta ko kuma jin rauni a matse-matsin mace ko cikin gabanta ko kuma mahaifarta da sauran abubuwanda suka ji6inci wadannan gurare, tare da haifar mata da rashin lafiya ko sauyawar yanayin jikinta.
Ciwon sanyi na iya kasancewa da kuraje ko gyambo ko kuma fitowar wasu bakin abubuwa daga gaban mace. 

ABUBUWAN DA KE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION. 
1)Rashin sanya pant. Indai mace za ta dinga yawo babu wando ajikinta, to `kura da sauran kwayoyin cuta za su samu saukin shiga gabanta. 
2)Barin pant yay dauda sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke. 
3)Saka pant ko wando a jiqe da ruwa.
4)Yawan tsarki da ruwan sanyi, wanda ba a tafasa ba, domin za a iya samun kwayoyin cuta acikin ruwan kuma za su iya wucewa har marar mace. 
5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yay yawa, shi kuma yana kashe wasu kwayoyin halitta masu amfani a gaba. 
6)Rashin aske gashin mara akai-kai, domin gashi yana tara kwayoyin cuta a jikinsa. 
7)Wasa da gaba. Idan mace tana saka dan yatsanta ko wani abu acikin gabanta, to za tay wa gabanta rauni kuma za ta kamu da ciwon sanyi. 
8) Yawan cin `Danyar Albasa.
9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci ko kuma ba bisa ka'ida ba, musamman wadanda ake cusawa acikin gaba. 
10)Dadewa akan Masai ko toilet, saboda kwayoyin cuta wadanda suke tasowa daga cikin masai suna shiga gaban mace. 
11) Rashin shan iska, idan mace ba ta samun lokaci tana dan bude jikinta a waje mai tsafta don ya sha iska. 
12)Musanyar tufafi musamman under wears,  saboda ciwon sanyi ciwo ne wanda ake iya dauka. 
13)Saduwa da mai cutar, ana iya daukar ciwon sanyi ta hanyar jima'i. 
12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.
13- Yawan shan kankara ko ruwa mai sanyi. 
14- Yawan zama akan Siminti ko tayal ba tare da shimfida ba. 
15- Yin aika-aikacen gida ba takalmi, kamar wanki da wanke-wanke misali. 
16- Kaciyar mata. Wani loakcin rashin yin kaciyar yana kawo matsalar sanyi, haka ma idan aka samu matsala wajen yin kaciyar, shi ma yana kawowa. 
17- Zubar da ciki ko 6arin ciki. Idan mace ta ta6a yin 6ari, to za ta iya kamuwa da ciwon sanyi, haka nan shan magungunan zubar da ciki shi ma yana kawo sanyi. 

YADDA MACE ZA TA GANE TA KAMU DA CIWON SANYI. 
Illolin da sanyi ko infectoin yake yiwa mata. 

1)Yana sa Rashin Sha'awa, ya zamto kwata-kwata mace sha'awarta da dauke, ba ta sha'awar da namiji. 
2)Yana sa ciwon mara mai tsanani, musamman lokacin zuwan jinini al'ada da ma sanda ba lokacin ba 
3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.
4)Yana sa mace ta dinga jinin al'ada bakikkirin mai wari.
5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata ko ta dinga ganin wani datti mai kamar gasara yana fito mata. 
6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.
8)Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.
10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11)In yay karfi yana hana mace haihuwa. 
12) Ya kan iya kaiwa gaban mace ya ru6e ko ya dinga fitar da tsutsotsi. 
13) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

RIGAKAFIN CIWON SANYI GA MACE. 
Idan ba kya so ki kamu da ciwon sanyi, to ki dinga lura da wadannan shawarwari masu zuwa a kasa. 
1- Ki dinga sanya pant ko wando, wanda datti ba zai shiga gabanki ba. 
2- Yawan tsaftace under wears. 
3- Tsarki da ruwa mai dimi. 
4- Aske gashin gaba akan lokaci. 
5- Ki guji saka hannu ko wani abu acikin gabanki. 
6- Duk magungunan mata da za kiy amfani da su, ki tabbatar da tsaftarsu kuma ya zama kwararren mai magani ne ya hada. 
7- Ki guji aron kaya ko sanya kayan mai cutar. 
8- Idan kina da yara mata, to ki kula da tsaftarsu, domin su ma yana iya sa musu warin gaba da kaikayi da kuraje har ma da tsutsa. 

YADDA AKE MAGANCE CIWON SANYI. 
Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewar ni'ima ko budewa da kwailewa da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi. Za a dace da yaddar Allah.
1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.
2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. Amma hadin wannan magani yana da zafi da kuma daci. 
3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection sannan idan infection ne wanda Aljanu su ka saka shi ma zai magance, insha Allahu. 
4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba. Amma kada a yi sau biyu a jere, ya kamata a dinga samun ratar kamar sati daya. 
5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.
6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.
7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.
8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Ganyen idon Zakara, sai ta dake su tay Yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni'ima da magance duk
matasalolin sanyi.
9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma'ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari sannan yana sa sha'awa. 
10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni'ima.
11) A samu Garin Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa kuma yana magance dattin sikari. 
Daga Dr. Bashir Halilu
Shugaban cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci. 
Sakataren Kungiyar masu magunguna na Musulunci da na Gargajiya ta Nigeria mai suna ITMCA. 
Lambar waya 08162600700.

ILLOLIN MASTURBATION WATO ISTIMNA'I
Masturbation ko kuma Istimna'i, shi ne wasa da tsiraici don biyawa kai bukatar jima'i.
   Masturbation ko kuma Istimna'i a larabce, wata hanya ce da mutum kan bi don biyawa kansa bukatar sha'awa irinta aure.
   Wasu sukan yi amfani da hannunsu ko wasu sassa na jikinsu, wasu kuma sukan yi amfani da injina ko sauran abubuwa da aka kera musamman don ay wannan lalata da su.
   Masturbation ya zama ruwandare game duniya a tsakanin musamman matasa, wanda shi ne babban bala'in da ya ke lalata rayuwar matasa a wannan lokaci, ya 6ata rayuwar matasa da yawa maza da mata.
   Anan muna so ne muy bayanin illolin Masturbation da kuma hukuncin Mai yinsa a addinin musulunci, duk da dai wasu Malaman sun ce duk Mai Yin Istimna'i za a tashe shi ranar Alqiyama ya yi wa hannunsa ciki.
   Kafin in kawo illolin Masturbation, bari in yi bayanin wasu daga cikin abubuwan da ke jefa matasa har da ma wasu masu auren cikin wannan bala'i.

WASU DAGA ILLOLIN MASTURBATION
Yana janyo:-
   1- Yawan mantuwa. Duk mai yawan istimna'i zai gamu da yawan mantuwa da shiririta.
   2-Yana rage hazaqar kwakwalwa. Duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya dena fahimta.
   3- Kankancewar gaba da
maraina ya koma kamar na yaro karami ko ya tattare ya dinga komawa ciki.
   4-Saurin kawowa yayin jima'i. Wani ko minti daya ba ya iya yi, yayin tarawa da iyalinsa sai ya ji ya kawo kuma ba zai iya komawa ba.
   5-Ramewa. Mutum zai ta ramewa, komai cin abincinsa da shan magunguna kara kiba.
   6-Rashin karfin mazakuta har ta kai in yay aure ba ya iya gamsar da iyalinsa.
   7- Mazakutar namiji tana iya karyewa, ya zama kwata-kwata ya dena tashi, sedai ya dinga dan motsawa kadan.
   8- 'Karancin sha'awa bayan aure.
   9-Karancin maniyy. Wanda hakan yake da illoli da yawa, kamar haifar da rashin gamsar da iyali, rashin iya haihuwa da dai sauransu.
   10-Raunin jiki, duk mai yin masturbation yanay wa jikinsa asarar wasu sinadarai masu kara kuzari. Don haka zai zama mai raunin jiki.
   11-bushewar fatar kan zakari ya dinga wani abu kamar 6awo ko `kanzo.
   12- Tsargiya, fitsarin jini. Yin masturbation kan sa mutum ya ga yana fitsarin jini, ko in yay masturbation din ya ga ya taho har da jini.
   13- Watery sperm. Yana sa maniyyin mutum ya tsinke ya zama kamar ruwa kuma mara kauri, wanda hakan ke nuna dakyar in mutum zai iya haihuwa.
   14- Yana sa mutum haka kawai ya ji yauqi yana fito masa koda bai yi masturbation din ba.
   15- Idan masturbation ya ratsa mutum, to in bai yi ba ba zai iya bacci ba.
   16- In ya sarqi mutum to in ya kwana biyu bai yi ba sai ya yi ciwon ciki kamar zai mutu.
   17-Mace mai yin masturbation yana jawo mata doyin farji. Wato jin wari yana fitowa ta gabanta.
   18- Ganin wani farin ruwa yana fito mata 
   19- Kaikayi da kurajen gaba.
   20- Yana kawarwa da mace budurcinta.
   21- Yana kawo zubewar nono ga mace.
   22- Yana sa mace ta dena sha'awar namiji samsam.
   23-Koda mutum yay aure in ya tara da iyalinsa to se ya kara da masturbation sannan yake samun cikakkiyar gamsuwa. Idan mace ce ma haka.
   24- Yana iya sa wa idan mutum ya girma ya kasa rike fitsari.
   25- Masturbation hanya ce ta afkawa cikin zina da madigo da makamantansu.
   26- Yana rage lafiyar idanu.
   27- Yana sa mace ta zama wawakekiya mai fadi. 
   28- Da wahala namiji ya iya gamsar da matar da take istimna'i. 
   29- Tun tana yi tana jin dadi, in aka dau shekaru kuma in ta yi sai ta dinga jin jiri da ciwon kai da 6acin rai. 
   30- Mace mai yin istim'nai daga daga baya zai zama abinda take amfani da shi ba ya gamsar da ita. 
   31- Yana kawo mataalar Aljanu da yawan mafarkin haihuwa ko saduwa. 

HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION
   1. Nisantar duk wani hoto ko video mai nuna tsaraici.
   2. Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
   3. Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.
   4. Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.

MAGANIN MATSALAR ISTIMNA'I
Idan ba ka da aure kuma sha'awa na damunka ko damunki sai ka:-
   1- Dinga cin abinci wanda aka sarrafa da waken suya, yana rage sha'awa.
    2- Na'ana'a na da amfani ga lafiya sosai, toh
amma itama 'dan'danon 'mint' da take
dashi yana dakushe sha'awa.

WANDA YAKE DA AURE KUMA
   1- Ka dinga markada Gurji wato Cocomba kana yin lemo da shi, wannan yana kara yawan sperm.
   2- Ka dinga cin Muruci, yana karawa maza karfin jima'i.
   ★Yana da kyau ka ziyarci likita in har in wannan matsala ta ci karfinka ko wajen masu maganin gargajiya. 
Daga Dr. Bashir Halilu
Shugaban Cibiyar Sunnah Medicine, Masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. 
Sakataren Kungiyar masu magungunan Gargajiya da na Musulunci ta Nigeria, ITMCA.

TASIRIN MAGUNGUNAN GARGAJIYA DA AMFANINSU DA KUMA ILLOLINSU GA MATA. 

Maganin gargajiya na nufin bin tsohuwar hanya wacce aka gada iyaye da kakanni don magance wata cuta ko kuma domin inganta lafiya. 
   Maganin Gargajiya yana da tasiri sosai ga rayuwar mata da 'ya'yansu da kuma mazajensu, domin kuwa shi ne maganin da ake amfani da shi iyaye da kakanni, tun farkon duniya. Hausawa da sauran mutanen duniya suna amfani da 'ya'yan itatuwa da sake-saki, da saiwoyi da ganyayyaki da itatuwa da tsirrai da hakukuwa da kauci da fure da huda da kwallaye da 'karo da mai da ruwa da sauran sassan jikin bishiyoyi da ciyayi ko 'kayoyi don magance cututtuka da kuma gyaran lafiyarsu ko kyautata ta. Haka kuma a gargajiyance, ana amfani da wasu sassan jikin dabbobi wajen hada magunguna, kamar man jikin wasu dabbobin ko naman jikinsu ko nono ko kaho ko fitsari ko kashinsu ko farce da dai sauransu. Haka nan ana iya amfani da wadansu abubuwa da Allah madaukakin Sarki ya tanadar da su a ban kasa wadanda ba a jikin dabbobi ko tsirrai suke ba wajen hada magunguna, kamar alumun da kanwa da gishiri da farar wuta da kalba da dai sauransu. A dai gargajiyancen, ana amfani da wasu abubuwa daban wadanda mutane su ka fahimci suna da amfani, da wanda aka samesu sakamakon hada wani abu daban, kamar kwan makera da dai sauransu. 
   Hanyoyin maganin gargajiya a wajen Bahaushe sun hada da yin kaho, yin sakiya, yin tawaida, yin dauri, yin dori yin kaciya ga maza da wata da kuma cire 'yar wuya. 
Kasancewar mata su ne iyayen al'uma, magungunan gargajiya suna da tasiri sosai a wajensu, domin kowace mace da akwai nau'o'in magunguna na gargajiya da ta sani ana amfani da shi agidansu wajen warkar da cututtuka ko kuma samun saukin irin cututtukan da suke gama-gari kamar amai, ciwon ciki, zazza6i, ciwon kai, magungunan masu juna biyu, magungunan saukaka nakuda da dai sauransu. Wannan ya sa maganin gargajiya ya yi tasiri sosai ga mata kuma har ta kai wasu sun ma fi so suyi amfani da maganin gargajiya sama da maganin asibiti, wasu kuma suna raba kafa ne, inda suke amfani da duka biyun. Amma dai da wahala a samu matar da sam-sam ba ta amfani da maganin gargajiya, ko kuma amfani da hanyoyin gargajiya don samun waraka. 

AMFANIN MAGUNGUNAN GARGAJIYA GA RAYUWAR MATA. 
1- Maganin Gargajiya yana warkar da cuta ne gaba daya tare da kashe kwayoyin cutar, matukar an hada shi kuma an yi amfani da shi yadda ya kamata. Fahimtar haka ya sa mata su ka aminta da yin amfani da su a matsayin hanya ta farko don samun waraka. 
   2- Maganin Gargajiya ba ya haifar da illa a wani 6angaren daban (side effect). Misali, idan mace ta sha maganin saukaka nakuda na gargajiya, to ba zai haifar ma ta da illa a jikinta ko ga jaririnta ba. Saboda magungunan da ake amfani da su dama abinci ne mara illa, kamar miyar ku6ewa, kuka, karkashi da dai sauransu.  Haka nan magungunan sauran cututtuka da na gyaran jiki. 
   3- Maganin gargajiya yana da saukin samu da kuma saukin hadawa, domin mafi yawan abubuwan da ake amfani da su bishiyoyi ne da ake shukawa acikin gida da kuma abubuwan da ake amfani da su yau da gobe. Wannan ya sa a koda yaushe ba a rasa mata da tanadin wasu magungunan gargajiya don shirin ko ta kwana. Kamar kanwa, Tazargade, man kadanya, Madaci,  Sabara, Rawaya, sabulun salo, kanumfari da dai sauransu. 
   4- Maganin gargajiya bai fiye kawo matsala ba, domin ana iya gane amfaninsa ko illarsa tun kafin a sha, ta hanyar dandanonsa ko warinsa ko kuma zafinsa. Mata su kan guji amfani da shi,  domin duk wacce ta dandana magni ta ji yana da yaji misali, to ba za ta baiwa karamin danta ba. Haka nan in mutum ya dandana magani ya ji tsami, to ba zai sha ba in ya san yana da lalurar da ba a shan abu mai tsami. 
   5- Ana iya saurin gane maganin gargajiya wanda ya lalace tun kafin a sha, ta hanyar kumburarsa ko bugawarsa ko kuma yin tsutsa idan na ruwa ne. Haka idan na gari ne akan ga ya yi kwari ko ya canja launi. In kuma sassake ne ko ganye, ya kan yi funfuna ko yana ko kwari. Don haka abu ne mai wahala mutum yay kuskuren shan maganin gargajiya wanda ya lalace. Haka nan maganin gargajiya musamman wanda aka kyautata ajjiyarsa, yana daukar lokaci mai ysawo bai lalace ba, wani ya kan dauki shekara biyar, bakwai, har sama da haka bai lalace ba. Shi ya sa mata suke tanadarsu su ajjiye, don shirin ko ta kwana. 
   6- Maganin gargajiya guda daya yana iya warkar da cututtuka da yawa. Misali, yawancin maganin sanyi na gargajiya to yana maganin basir. Ko kuma za ka samu dan itaciya guda daya amma yana magance cututtuka da yawa, misali Habbatus sauda da dai sauransu. 

   7- Maganin gargajiya galibi ainihin binciken tasirinsa da amfaninsa an gan shi ne a aikace ajikin mutane bayan sun yi amfani da shi. Don haka ba a kokwanto akan aikinsa ko kuma fargabar wani abu na cutarwa zai biyo baya idan mutum ya yi amfani da shi. Shi yasa mata ba su fiye tsorata ba idan za su yi amfani da maganin gargajiya, saidai bisa wani dalili na musamman. 
   8- Yawancin magungunan gargajiya wadanda ake baiwa mutane, sun dace ne da yanayin al'adarsu da kuma yanayin muhallinsu. Sa6anin wasu magungunan da ake hadawa daga wata kasa daban, wanda ba yanayinku daya da su ba. Shi yasa da wahala mutum ya sha maganin gargajiya bai masa aiki ba, saidai in ba a hada bisa ka'ida ba ko kuma ba sha bisa ka'ida ba. 
   9- Yawanci masu magungunan gargajiya su suke hada maganin da kansu, su ji matsalolin mara lafiya ko su duba shi da kansu, su ba shi maganin kuma suyi masa jinya. Don haka sun san yadda ake hada maganin da yadda ake bayar da shi da yadda yake tasiri da kuma illarsa in yana da ita da kuma nau'in wadanda ya kamata suyi amfani da shi da wadanda bai kamata ba. Shi yasa mata su ka fi so su je wajen masu maganin gargajiya domin mutum daya yana aikin malaman asibiti akalla guda uku, shi kadai. 
   10- Yawancin masu magunguna gargajiya suna ba da magungunan da suka danganci gangar jiki da kuma ruhi. Yadda za a fi ganewa shi ne, masu magungunan gargajiya suna ba da magungunan matsalolin Aljanu da na cututtukan ga6o6in jiki da kuma cututtukan da aka kasa gane kansu. Wasu ma suna da'awar suna iya baiwa mutum sa'a ko su kawar ma sa da kaddara mara kyau ko kuma su janyo masa wani amfani. Wannan ya sa mata su ka fi so su je wajen masu magungunan gargajiya, domin ko menene matsalarta to akwai abinda mai maganin zai ba ta. 

ILLOLIN MAGUNGUNAN GARGAJIYA GA MATA. 
   1- Rashin tsafta. Magungunan gargajiya, musamman wadanda ake siyarwa a kasuwa, wasu akan samu rashin tsafta wajen ajjiye maganin ko kuma wajen busar da shi. Don haka musamman magani da ba a dafawa kafin a sha, za a iya daukar cuta ajikinsa idan ba a kyautata dibansa ko kuma ajjiyarsa ba. 
   2- Karancin ilimi ko kuma wayewa daga wasu masu ba da magungan gargajiya. Akwai wadanda ba su yi karatun addini ko na zamani ba amma sun gaji bayar da magunguna daga iyaye da kakanninsu, don haka iya wannan su ka sani. Ba sa so su bayyana iliminsu ballantana in da kuskure ai musu gyara sannan kuma ba sa dora magungunansu da marasa lafiyarsu bisa ma'aunin addini da zamani. 
   3- Rashin kayan gwaje-gwaje. Yawanci masu magungunan gargajiya ba su da kayan gwaje-gwaje na zamani wadanda ake amfani da su don gano lalurar da ke damun mutum,  sai 'yan kadan, wadanda su ka zamanantar da sana'arsu.
   4- Maganin gargajiya wanda mutane suke hadawa a gida da kansu, ana iya samun matsala saboda amfani da shi ba bisa ka'ida ba. Shi yasa magungunan gargajiya suke da illa ga mata, musamman magungunan karin ni'ima da sauran matsaloli da su ka danganci aure. 

      Daga Dr. Bashir Halilu
Shugaban Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. 
   Sakataren Kungiyar masu magungunan Gargajiya da na Musulunci ta Nigeria, (ITMCA). 
Lambar waya 08162600700.

TASIRIN MAGUNGUNAN ASIBITI DA AMFANINSU DA KUMA ILLOLINSU GA MATA
   Magungunan asibiti da na gargajiya asalinsu daya ne, domin dukkansu an samar da su imma daga jikin tsirrai ko jikin wasu dabbobi ko kuma wasu abubuwa na musammn da Allah Ya halitta a ban kasa. Saidai su magungunan asibiti an kara musu karfi, an dada kyautata su kuma an inganta su sannan an ware wata cuta guda daya wacce kowane magani zai aiki akanta. Magungunan asibiti acikin asibiti kadai ake sayar da su da kyamis ko kuma wani waje na musamman da hukuma ta amince. Wasu daga cikin magungunan asibiti doka ne a siyarwa da mutum ko kuma mutum yay amfani da shi, saidai idan likita ne ya ba shi umarni kuma sai mutum ya nuna kwakkwarar sheda sannan za a sayar masa. Maganin asibiti ana sayarwa da mutum iya wanda zai yi amfani da shi ne ko kuma iya wanda likita ya ba da umarni a ba shi. 

 TASIRIN MAGUNGUNAN ASIBITI GA MATA. 

Maganin asibiti yana da tasiri sosai a wajen mata, kasancewar shi ne maganin da ya samu kar6uwa a wajen gwamnati sama da na gargajiya  sannan ana yin bincike da gwaje-gwajen lafiya kafin a baiwa mutum. Maganin asibiti ya kara samun tasiri a wajen mata ne saboda kusan kowane asibiti ana iya ajjiye mara lafiya yayi jinya kuma idan wani likitan bai fahimci matsalar mutum ba zai tura shi wajen wani. Haka nan asibiti kowane 6angaren lalurar akwai mai lura da shi, na musamman. Mata sun fi so su haihu a asibiti ne saboda akwai tanadin gurin haihuwa na musamman da kayan kar6ar haihuwa da magunguna a kusa. Saidai wasu na so su haihu a gida don kar a ce lalura ta kaisu asibiti. 
AMFANIN MAGUNGUNAN ASIBITI GA MATA
   1- Maganin asibiti sai an ga mara lafiya sannan ake ba shi, sannan ajiki an rubuta yadda za a yi amfani da shi kuma iya adadin wanda zai yi amfani da shi za a ba shi. Don haka da wahala mutum yay kuskuren shan maganin ya wuce kima ko ba bisa 'ka'ida ba. 
   2- Maganin asibiti yana saurin saukar da ciwo ko rage radadinsa ga mara lafiya. Kamar mata masu goyon ciki da masu matsolin al'ada da masu jarirai, sun fi so su sha ko su baiwa yayansu maganin asibiti saboda yawanci cikin kankanin lokaci yake saukar da zazza6i ko radadin ciwo. 
   3- Maganin asibiti ya fi tsafta, kyawun mazubi da kuma kyawun gurin ajjiya. Don haka da wahala wata kwayar cuta ta makale ajikin maganin asibiti, har ta cutar da wanda yay amfani da shi. 
   4- Maganin asibiti an fi hada shi ta hanyar kwarewa da bincike da ilimi da kuma tabbatarwa bisa aikinsa. 
   5- Maganin asibiti a rubuce ake baiwa mutum. Da sunan magani da karfinsa da kuma adadin yadda mutum zai amfani da shi da kuma lalurar da ta sa aka baiwa mutum. Don haka idan ya haifarwa da mutum matsala ko ya sha ba bisa ka'ida ba, to abu ne mai sauki a gano inda matsalar ta ke da kuma wani maganin da za a ba shi ta hanyar duba katin da aka ba shi a asibiti. 
   6- Masu magungunan asibiti sun fi samun ingantaccen horo kuma kar6a66e wajen sanin yadda ake samo magani da hada shi da ajjiye shi da bayar da shi ga mara lafiya da kuma sanin yadda yake aiki ajikin mutum sannan sun fi yin aikinsu karkashin sa ido da kulawar jami'ai ko hukumomi. 
   7- Ma'aikatan asibiti suna da hanyoyin baiwa mutum taimakon gaggawa sama da na gargajiya, kamar durawa mutum ruwa ta jijiya ko karin abinci ko karin jini ko taimakon numfashi ko kuma saurin gano 6angaren da ke da matsala ajikin mara lafiya da kuma yanayin matsalar. 

ILLOLIN MAGUNGUNAN ASIBITI GA MATA
   1- Yawanci magungunan asibiti ba sa warkar da cuta gaba daya, sai dai mutum ya dan ji sauki na wani lokaci sannan ciwon ya sake tashi. 
   2- Yawancin magungunan asibiti suna da illa, suna cutar da wasu 6angaro na jikin mutum saboda sinadaran da ake kwa6a magungunan da su da wadanda ake zubawa don hanasu lalacewa sannan suna kara zama illa ne saboda yawanci kashe radadi suke yi ba kashe cuta ba, don haka mutum zai ta sha ne ana canja masa wasu. Don haka yawan shan yana taimakawa wajen karuwar yawan illar. 
 Wasu daga cikin illolin sun hada da matsalar kwakwalwa, matsalar zuciya, matsalolin jini, matsalolin haihuwa da dai saransu.
   3- An fi saurin cewa za a yanka jikin mutum a asibiti don a cire masa cuta ko a yanke ma wata ga6ar ta jikinsa wanda yawancin mutane ba sa son haka. Wasu su kan gwammace su koma yin amfani da maganin gargajiya akan ayi musu aiki a asibiti. 
   4- A asibiti ne ake dora mutum akan magani bisa wata cuta ta musamman kuma gaya masa cewa ba zai warke ba. 

Daga Dr. Bashir Halilu
Shugaban cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci 
Sakataren kungiyar masu magungunan gargajiya da na Musulunci ta Nigeria (ITMCA) .
Lambar waya 08162600700.

Comments

Popular Posts