TSAYUWAR DARE TARE DA LIMAN A WATAN RAMADAN.
TSAYUWAR DARE TARE DA LIMAN A WATAN RAMADAN.
An karɓo daga Abiy Zarrin (RA) ya ce "Mun yi Azumi tare da Manzon Allah (SAW) a watan Ramadhana, bai tsaya da mu wani abu ba a wannan watan (don yin sallolin nafila), har sai da ya rage saura kwana bakwai, sai ya tsaya da mu, har sai da ɗaya bisa ukun dare ya shuɗe.
Da ya zama saura kwana shida bai tsaya da mu ba, da ya rage saura kwana biyar sai ya tsaya da mu har sai da rabin dare ya ahuɗe.
Sai na ce "Ya Rasulallahi da ka yi mana nafilar tsayuwar wannan daren gaba ɗaya", sai ya ce "Ai haƙiƙa idan mutum yay sallah tare da liman har ya idar to za a lissafa masa (lada) na tsayuwar wannan daren".
Da ya rage kwana huɗu bai tsaya da mu ba. Da ya rage saura kwana uku sai ya tara ahalinsa da matansa da sauran jama'a, ya tsaya da mu har sai da mu ka ji tsoron lokacin sahur zai ƙuɓuce mana. Daga nan kuma bai kuma tsayawa ragowar kwanakin watan ba".
- Abu Zarrinil Giffariy.
Daga cikin Abubuwan da hadisin ya ke karantarwa:
1- Manzon Allah (SAW) yana jagorantar iyalan gidansa da matansa da sauran jama'a sallolin Nafila a watan Ramadan, ana yinta a jam'i.
2- Wani sa'in yana jan sallar har a kai ɗaya bisan ukun dare, wani lokacin har rabin dare, wani lokacin kuma har lokacin sahur ya kusa ƙurewa ana sallar.
3- Ba lallai ne sai mutum ya yi tsayuwar dukkan watan ba, yana iya zaɓar kwanakin da ya ga dama, kamar yaddda Manzon Allah (SAW) ya yi.
4- Falalar wanda ya tsaya nafilar dare tare da Liman har aka idar, za a rubuta masa ladan wanda ya sallaci daren gaba ɗayansa.
5- Mata da sauran jama'a suna halartar sallar, ciki har da matan Manzon Allah (SAW).
Da dai sauran darussa.
Wannan hadisi:
* Abu Dawuda ya ruwaito shi (1375)
* Tirmizi (806).
* Nasa'iy (1364), kuma lafazin Nasa'in ɗin mi ka kawo.
* Ibn Majah (1327)
* Ahmad (2141)
* Kuma Albaniy ya inganta shi acikin 'silsilatul ahadisus sahihah'.
- عن أبي ذرٍّ قالَ : صُمنا معَ رسولِ اللَّهِ صلَّى اللَّه عليه وسلم رمضانَ فلم يقُم بنا شيئًا منَ الشَّهرِ حتَّى بقِيَ سبعٌ فقامَ بنا حتَّى ذَهبَ ثلثُ اللَّيلِ فلمَّا كانتِ السَّادسةُ لَم يقم بنا فلمَّا كانتِ الخامسةُ قامَ بنا حتَّى ذَهبَ شطرُ اللَّيلِ فقلتُ: يا رسولَ اللَّهِ لو نفَّلتَنا قيامَ هذِهِ اللَّيلة. قالَ فقالَ: إنَّ الرَّجلَ إذا صلَّى معَ الإمامِ حتَّى ينصرِفَ حُسِبَ لَهُ قيامُ ليلةٍ. قالَ: فلمَّا كانتِ الرَّابعةُ لم يقُم فلمَّا كانتِ الثَّالثةُ جمعَ أَهلَهُ ونساءَهُ والنَّاسَ فقامَ بنا حتَّى خشِينا أن يفوتَنا الفلاحُ. قالَ قلتُ وما الفلاحُ قالَ السُّحورُ ثمَّ لم يقم بقيَّةَ الشَّهرِ.
-
الراوي : أبو ذر الغفاري | المحدث : الألباني | المصدر : صحيح النسائي
الصفحة أو الرقم: 1363 | خلاصة حكم المحدث : صحيح
التخريج : أخرجه أبو داود (1375)، والترمذي (806)، والنسائي (1364) واللفظ له، وابن ماجه (1327)، وأحمد (21419)
Comments
Post a Comment