GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI.
* 1- Ya tabbata Annabi (SAW) yana kara kokari na ibada a cikin goman karshe na Ramadhan, kokarin da ba ya yin irinsa a wasu kwanakin.
عن عائشة رضي الله عنها قالت: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ يَجْتَهِدُ فِي رَمضانَ مَالا يَجْتَهِدُ في غَيْرِهِ، وَفِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ منْه مَالا يَجْتَهدُ في غَيْرِهِ" رواهُ مسلمٌ.
* 2- Asali Allah Ya kwaɗaitar a yi sallar Tahajjudi har ma ya ce ya kusanta Allah Ya tasheka a wani matsayi mai girma.
{وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَكَ } [الإسراء: 79]
Tahajjudi shi ne rashin bacci da raya dare da Sallah da Ibada.
* 3- Annabi (SAW ) ya kasance yana raya dare da Ibadau a goman karshe kamar yadda ya zo a Hadisin A’isha (SAW ) cikin Bukhari da Muslim.
وعَنْهَا رَضَيَ اللَّه عَنْهَا، قَالَتْ: كَانَ رسُول اللَّهِ ﷺ: إِذا دَخَلَ العَشْرُ الأَوَاخِرُ مِنْ رمَضَانَ، أَحْيا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَه، وجَدَّ وَشَدَّ المِئزرَ متفقٌ عَلَيهِ.
* An sunnanta mana yin Jam’i a Sallar dare a watan Ramadhana, saboda Sahabbai sun bi Annabi (SAW ) Sallah a daren 23, har zuwa 1/3 na dare, da kuma daren 25, har zuwa rabin dare, da kuma daren 27, har daf da Asubah. To sai ya dena fitowa, tsoron kar a farlanta Sallar, kuma daga baya al’umma su kasa.
عن أبي ذرٍّ قالَ : صُمنا معَ رسولِ اللَّهِ صلَّى اللَّه عليه وسلم رمضانَ فلم يقُم بنا شيئًا منَ الشَّهرِ حتَّى بقِيَ سبعٌ فقامَ بنا حتَّى ذَهبَ ثلثُ اللَّيلِ فلمَّا كانتِ السَّادسةُ لَم يقم بنا فلمَّا كانتِ الخامسةُ قامَ بنا حتَّى ذَهبَ شطرُ اللَّيلِ فقلتُ: يا رسولَ اللَّهِ لو نفَّلتَنا قيامَ هذِهِ اللَّيلة. قالَ فقالَ: إنَّ الرَّجلَ إذا صلَّى معَ الإمامِ حتَّى ينصرِفَ حُسِبَ لَهُ قيامُ ليلةٍ. قالَ: فلمَّا كانتِ الرَّابعةُ لم يقُم فلمَّا كانتِ الثَّالثةُ جمعَ أَهلَهُ ونساءَهُ والنَّاسَ فقامَ بنا حتَّى خشِينا أن يفوتَنا الفلاحُ. قالَ قلتُ وما الفلاحُ قالَ السُّحورُ ثمَّ لم يقم بقيَّةَ الشَّهرِ.
صحيح. رَواه النسائي
* 5- Tun daga nan sai aka dena yin Jam’in, har Annabi (SAW ) ya rasu, a zamanin Abubakar (RA) ma ba a yi ba, sai cikin Khalifancin Umar (RA), wata rana ya fito Masallaci cikin dare sai ya samu mutane suna Sallah daban-daban, sai ya hada su wuri daya, ya nada musu Ubayyi bn Ka’ab (ra) ya yi musu limanci. Sai Tamim Al-Dariy kuma ya yi limanci wa mata. Tun daga nan har yau al’ummar Musulmi suke yin Jam’in Sallar dare a Ramadhan.
- عن السائب بن يزيد أنه قال : ( أَنَّ عُمَرَ بنَ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنهُ جَمَعَ النَّاسَ فِي رَمَضَانَ عَلَى أُبَيِّ بنِ كَعبٍ وَعَلَى تَمِيمٍ الدَّارِيِّ عَلَى إِحدَى وَعِشرِينَ رَكعَةً ، يَقرَؤُونَ بِالمِئِينَ ، وَيَنصَرِفُونَ عِندَ فُرُوعِ الفَجرِ )
* Don haka mata ma ya halasta su fita Masallacin a yi Sallar daren da su.
* An ruwaito cewa tun daga zamanin Sayyidna Umar (RA) ana yin raka'a goma sha ɗaya ne. An ruwaito ashirin, an ruwaito ashirin da ɗaya kuma an ruwato ashirin da uku.
Wadannan bayanai duka suna cikin Muwaɗɗa Malik, Sahihul Bukhari da Muslim da “Sunanul Arba’a” da sauran littatafan Hadisi, cikin Hadisin A’isha (RA), Abu Zarr (RA), da kuma Nu’uman bn Basheer (RA) da wasunsu.
Allah Ka ba mu ikon raya waɗannan darare da ibada karɓaɓɓiya.
Comments
Post a Comment