SALLAR IDI DA SAURAN ABUBUWAN DA KE DA ALAƘA DA ITA. DAGA SHAFIN BASHIR HALILU. LAMBAR WAYA 08162600700, 08134434846.
Musulmi muna da idi guda uku, biyu daga ciki suna maimaituwa duk shekara.....
1. Idin babbar sallah wanda yake maimaituwa duk ranar goma ga watan Zulhijjah.
2. Idin karamar sallah wanda yake maimaituwa duk ranar daya ga watan Shawwal.
3. Idin Jumma'a wanda yake maimaituwa duk sati.
Babu wani idi a musulunci bayan waɗannan.
KALMAR IDI.
Abinda kalmar idi take nufi shine duk abinda yake maimaituwa, yake dawowa, yake komowa da farin ciki a wani lokaci sananne.
Anas Ɗan Malik RA ya ruwaito cewa lokacin da Manzon Allah saw ya shigo Madina suna da wasu ranaku da suke yin idi a ciki wanda suke tunano abubuwa da suka faru a zamanin Jahiliyya, sai yace Allah ta'ala ya musanya muku da wasu ranaku da idin Fiɗir (karamar sallah ranar ɗaya ga watan Shawwal) da kuma idin adhha (ranar goma da watan hajji).
Imam Ahmad da Abu Dauda da Nasaiy duba Sahihu Abi Daawud. Ibn Hazmin ya ruwaito ijma'in Malamai akan Haka.
HIKMAR SALLAR IDI.
Allah ta'ala cikin hikmar sa ya warewa musulmi wata rana bayan sun ƙare ibadar azumi zasu shiga cikin watan hajji, su yi salla suyi farin ciki su girmama Allah bisa hore musu dama har suka ga ƙarshen azumi lafiya, kuma kwanakin hajji suka fara.
Abubuwa da ake ranar sallah
1. Yin sallar idi
2. Fitar da zakkar kono kafin sallah
3. Sada zumunta
4. Girmama Alalh da yi masa godiya
5. Shagulgulan sallah ga mata da yara waɗanda basu katare iyaka ba.
6. Bayyana farin ciki da yafiya da kyautatawa al'umma da makota.
HUKUNCIN SALLAR IDI.
1. Alkur'ani mai girma.
2. Sunnar Annabi saw.
3. Haɗuwar kan malamai.
An sami maganganu guda uku daga Malaman musulunci gamai da Hukuncin sallar idi, gwargwadon kowa daga cikin su dalilan da suke hannun sa:
1. Wajibi ne zuwa sallar idi, abinda ake kira wajibi shine, duk abinda shari'a ta nemi a yi shi dole, idan an yi shi yadda tace za a sami lada, idan ba a yi shi ba an aikata laifi, wanda azaba taya iya sauka akan haka,
2. Mustahabbi ne zuwa sallar idi, abinda ake kira mustahabbi shine, idan an yi za a sami lada, idan ba a yi ba babu alhakki.
Fardu kifaya ne zuwa sallar idi, abinda ake kira Fardu kifaya shine abinda ake nema wasu daga cikin al'umma su yi domin su daukewa ragowar, amma idan babu wanda ya yi to duk al'umma ta yi laifi.
Sallar idi ta banbanta da sauran salloli ta fuskoki da dama:
1. Ba a yi mata kiran salla ko iƙamah.
2. Ba a yin nafila kafin ta ko bayan ta.
3. Ba a yin huɗuba sai bayan an gama sallah.
4. Ana yi mata karin kabbarori guda bakwai a raka'ar farko har da kabbarar harama, da kabbarori guda biyar a raka'a ta biyu.
5. Ana canga hanya wajan tafiya da wajan dawowa.
6. Duk musulmi maza da mata yara da manya, har da masu jinin al'ada da jinin biƙi da amare da marasa hajabi, duk duk sai su aro daga makota domin su zo sallar idi saboda mahimmancin ta.
7. Waɗanda suke da larura ta rashin yin salla sai su koma gefe suna Kabbara, domin su dace da addu'ar wannan rana da albarkacin ta.
8. Za a tafi ana kabarbari cikin nutsuwa
9. Yin wanka da ado kwalliya da shafa turarai a ranar salla domin zuwa sallar idi.
10. Yin asuwaki da gyaran jiki, da tsafta da kaucewa maganganu na batsa da rashin kan gado.
11. An so a tafi a ƙafa a dawo a ƙafa. idan ba tafiyar akwai wahala ba.
12. Ana so aci dan dabino kafin a fita zuwa idi na karamar salla.
13. Ana so ayi sammako zuwa sallar idi,. musamman na babbar salla. domin a dawo da wuri a yanka abin layya.
14. Idan kuwa sallar idi ne na karamar sallah an so ayi jinkiri domin a sami lokacin fitar da zakkar fidda kai.
YADDA AKE SALLAR IDI.
13. Raka'a biyu ce.
14. Karatun ta a fili ake yi.
15. Za ayi Kabbara bakwai ban da kabbarar harama a raka'ar farko.
16. Za a Kabbara biyar banda kabbarar dagowa a raka'a ta biyu.
17. Ana karanta suratul A'ala a raka'ar farko bayan Fatiha. Ko suratu Ƙaaf,
18. Ana karanta sa suratul Gashiyati a raka'a ta biyu bayan Fatiha, ko suratu ƙamari,
19. Bayan an gama salla sai a gabatar da huɗuba guda ɗaya, ba biyu ba domin Hadisin da ya kawo ƙudubah biyu bashi da inganci, don haka masu fassara huɗuba sai su hade su a tsayuwa guda.
20. Ba a hawa minbari lokacin yin khutbar sallar idi a ƙasa ake yi,
21. Kada ayi doguwar khuɗuba, domin abawa mutane dama su koma gida da wuri.
22. A wajan Kabbarorin za a iya daga hannu, idan idan ba a ɗaga ba babu laifi.
23. Sahabbai suna yiwa juna fatan alkhairi da addu'a ta gari ranar idi,
Allah ya karɓa mana ya maimaita mana da alheri.
Daga shafin Bashir Halilu.


Comments
Post a Comment