YADDA ZA KA GANE KANA DA ALJANI KO KUMA AN YI MA KA ASIRI
YADDA ZA KA GANE KANA DA ALJANU KO
KUMA AN YI MA KA SIHIRI
Ana gane mai Aljanu ne ko wanda aka yiwa
sihiri ta hanyoyi guda uku:
1) Alamomin boye.
2) Alamomin sirri.
3) Alamomin zahiri.
.
.
*Alamomin boye sune alamomin da shi mara
lafiyar
ne kawai ya ke iya ji ko ganin su a tare da
shi.
Kamar
*Yawan mafarki mai abin tsoro.
*Yawan ciwon kai dab da magriba.
*Jin abu nai ma yawo a jiki kamar kiyashi.
*Haka kawai gaban mutum ya dinga faduwa.
*yawan mafarkin saduwa.
*Rashin son yin aure.
*Bacin rai mara dalili.
*Yawan tunane_tunane marasa amfani.
*Gane-ganen abubuwan tsoro kamar karnuka,
macizai, kuraye da dai sauran su.
*Jin kasala lokacin da za ka yi sallah.
*Jin ciwon kai lokacin da ake karanta Alqur‘ani.
*Rashin fahimtar karatu ko kuma saurin zubewar sa, musamman ma na addini.
*yawan jin an kira sunan ka kuma ka waiwaya ba ka ga kowa ba.
*yawan jin kamar an caka ma ka kibiya ko allura a jiki.
*za ka kwanta barci da wuri amma ya ki daukar ka sai dab da asuba.
*Yawan batan kudi ko kayan amfani.
*Yawan fada ko gaba da mutane.
Da dai sauran alamomi.
Ya a ke gane mai Aljanu?
ko wanda aka jefe
shi da Sihiri(kashi na biyu)
Ana gane mai Aljanu ne ta hanyoyi guda uku
kamar
yadda mu ka fada tun a farko
1) Alamomin 6oye
2) Alamomin sirri
3) Alamomin zahiri
Mun yi bayanin alamomin 6oye, yanzu ga alamomin sirri.
Alamomin sirri alamomi ne wadanda se wanda ke
tare da mara lafiyar ko da yaushe shi ne zai dinga ganin su ko fuskantar su.
* Mutum ya dinga magana a lokacin da ya ke
bacci.
* Nauyin Bacci mara misali.
* Dadewa a bandaki alhali ba abin da mutum ya ke yi.
* saurin fushi.
*Son zama a duhu.
*Son zama a waje mai kazanta.
*Zama da kazanta da rashin son yin wanka.
*Surutu barkatai.
*Rashin dariya ko murmushi sanda a ke abin dariya.
*Rashin son yin sallah.
*Yawan harare-harare.
*Kura wa mutane ido.
*Yawan dariya ko murmushi ba dalili.
*Taurin kai.
*Rashin samari ga Budrwa.
Da dai alamomi da yawa.
Daga shafin Sunnah Islamic Medicine.
Don karin bayani Shiga wannan shudin rubutun, ka danna like
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Shin ko yawan wasi wasi da Kuma baka da wani tunani saina mutuwa shima alamace tame aljanu
ReplyDelete