GURAREN ZAMAN ALJANU
GURAREN ZAMAN ALJANU
=======================
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruqiyyah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Abu ne mai muhimmanci mutum ya san guraren zaman Aljanu saboda aqalla zai zama ka kiyaye shiga irin wadannan gurare ko kuma ya zama ka yi addu'a idan za ka shige su.
Sannan yana da kyau mai Ruqiyyah ko mai bada magani ya san muhallai da kuma guraren zaman Aljanu.
Hakan zai taimaka maka sosai ta yadda zaka gane nau'in Aljanin da yake jikin mutum da kuma irin yadda zaka mu'amalanci Aljanin da yadda za kay maganinsa cikin sauqi insha Allahu.
.
.
Za ka samu cewa mafi yawa ko kuma dukkan guraren zaman Aljanu, dama Addini ya yi umarnin mu nisance su in ba da wata lalura ba kuma sunnah ta koyar da addu'o'i yayin mu'amala da wadannan muhallai.
.
.
Mazaunin Aljanu ya danganta da irin addininsu da al'adarsu da kuma ra'ayinsu ko yanayin halittarsu.
Musulman Aljanu suna zama a wajen da ya dace da rayuwar musulmi, Kafuran cikinsu ma suna zama a inda ya dace da addininsu.
A cikinsu akwai qazamai, akwai masu tsafta akwai 'yan gayu akwai talakawa akwai masu wadata.
Haka nan Aljanu suna da qabilu da bambancin launin fata da bambancin yanayin abinci da sauran bambance-bambance da ake samu a tsakanin mutane.
Don haka kowa yana rayuwa daidai yadda ya samu kan sa da yadda yaga ya dace da shi.
.
.
GURAREN ZAMAN ALJANU
=======================
1) QANQARAR SAHARA
Akwai Aljanu masu rayuwa a cikin SAHARAR QANQARA.
Kamar JINNUL KATFA, su kuma suna yin haka ne saboda munanan akidunsu da mugwayen dabi'o'insu da kuma yadda basa son kowa ya ra6esu kuma su ma basa ra6ar kowa, koda kuwa 'yan uwan su Aljanu.
Suna da mugunta sosai kuma suna haifarwa da mutane ciwon farfadiya ko yawan faduwa idan suna tafiya.
Wadannan Aljanu wato Jinnul Katfa na kawo bayaninsu tuntuni. Mai bukata zai iya dubawa shafina.
2- BAQIN DUHU
Akwai Aljanu masu rayuwa a cikin duhu.
Kamar Jinnuz Zulam.
Wadannan Aljanu in suka shiga jikin mutum zai zama baya son zama a cikin mutane, ba ya son magana kuma ba ya son zama a cikin haske.
Tunani ya kan yi wa mutum yawa har ma ya zamto ba ya riqe karatu kuma zai dinga jin kamar duk mutanen duniya sun tsane shi.
Tuntuni na yi cikakken bayani akan wannan nau'in Aljanu.
3) BAN DAKI
Akawi Aljanu masu rayuwa a BANDAKI KO BAYI kamar KHADIMUL HAMMAM.
Wato Aljanu Qazamai.
In suka shiga jikin mutum suna sa wa ya dinga jin jikinsa yana warin kashi ko mutane su dinga jin sa yana wari.
Mutum zai zama ba ya son yin wanka ko tsafta sannan in ya shiga bandaki sai ya zauna ya dade kamar ba zai fito ba.
Su kan sa wa mata doyin farji ko warin ja6a.
Suma mun yi cikakken bayanin akansu.
4) MAQABARTA
Akwai Aljanu masu rayuwa a MAQABARTA kamar SAKINUL MAQBIR.
Idan suka shafi mutum zai dinga yawan mafarkin maqabarta ko matattu ko qaburbura ko kuma ya dinga mafarkin shi kan sa ya mutu.
(Tuni mun kawo bayani akansu).
5) CIKIN KOGI
Akwai Aljanu masu rayuwa a cikin KOGI KO TEKU. Kamar Jinnul Gauwas da Tabriyqul jinn.
Saidai su Jinnul Gauwas sun fi zama a cikin kogi mai cike da ruwa.
Sukan sa mutum fitsarin kwance da yawan mafarkin kogi da kuma ciwon ga6o6i.
Suma dai mun yi bayani akansu a can baya.
Su kuma Tabriyqul Jinni sun fi zama a cikin kogi wanda ba ruwa sosai ko wanda ya qafe.
Za mu kawo bayani akansu insha Allahu.
6-KAN BISHIYA
Akwai Aljanu masu rayuwa a kan BISHIYOYI, Kamar JINNUT TAYYAR. Wato Aljanu masu siffar tsuntsaye.
Sukan yi shawagi a sararin samaniya sannan su sauka akan bishiya kamar yadda tsuntsaye suke yi.
Suna sa mutum ya zama mai yawon tsiya. Koda mace ce ko yaro, su kan zama masu yawo da rashin son zama waje daya.
(Su ma mun dade muna bayani akansu).
7- CIKIN RAMUKA DA KWAZAZZABAI
Akwai masu rayuwa a cikin RAMUKA, kamar JINNUL HAYYAT. Wato Aljanu masu siffar Macizai.
Suna shiga jikin mutum idan yana fitsari a cikin rami ko masu haqe ramuka don su kama 6eraye da dai sauransu.
Sukan sa mutum ciwon haqori, kunne da zafin farcen kafa dana hannu.
Wani lokacin sukan rufe bakin mutum ya kasa yin magana.
suma mun kawo cikakken bayani akansu.
8- JIKIN MUTANE
Akwai masu rayuwa a cikin JIKIN MUTANE, kamar JINNUL QARIYN.
Wato Aljanu masu yawo a cikin jinin mutane, masu kwana acikin hancin mutane masu yiwa mutane fitsari a kansu. Su ne kuma suke cin abinci tare da mutane.
Sukan sa mutum rashin son ibada da kasala da yawan sha'awar aikata sa6o.
(mun kawo muku bayani a kansa cikakke tuntini).
Sannan akwai JINNUL BAKAM su ma suna rayuwa ajikin mutane amma su rashin lafiyar ga66ai suke sakawa, kamar rikewar kafa da shanyewar jiki da dai sauransu.
(Nan gaba za mu kawo bayani akansu insha Allahu.
9- GONAKI.
Akwai Aljanu masu rayuwa a cikin gonaki. Kamar Jinnul Shu'un, wadanda mukay muku bayanin cewa dukkaninsu sana'a suke babu mai zaman banza a cikinsu.
Idan suka shiga jikin mutum zai dinga yawan mafarkin daji da fili mai fadi da gonaki da ciyayi.
Mutum zai dinga jin ba ya son raini don haka ma gara ya ware can inda ba kowa yay rayuwarsa shi kadai.
Shi yasa wanda suka shafa zai zama mai yawo mara amfani kuma shi kadai. Ba ya son tafiya da kowa.
Su ma dai mun yi bayani akansu tuntuni.
10- MASALLATAI.
Akwai Aljanu masu zama a Masallaci suna ibada. Akwai ma wadanda suka tare a Ka'aba suna i'itikafi.
Dukkanninsu Musulmai ne amma ba dukkansu ne mutanen kirki sosai ba.
Akwai masu zuwa cikin gari suy harkokinsu sannan su koma. Akwai kuma masu zuwa su aikata 6arna sannan su koma masallatai suy ibada.
Wannan dai dabi'a ce ta duk wani mukallafi. Indai ba ma'asumi bane to an san watarana zai iya aikata sa6o.
Mun sha samun Aljanu da laifin shiga jikin mutane amma idan mun neme su sai ace suna Ka'aba suna ibada. Har sai sun dawo sannan mu kama su.
11- CIKIN DAJI.
Akwai Aljanu wadanda sam ba sa shigowa cikin mutane kuma basa ra6ar Dan'Adam ballantana su shiga jikinsa.
Irin wadannan Aljanu sun fi zama a qungurmin daji kuma idan sun ga mutane sun fara ra6arsu sai su canja waje.
Duk da dai wani lokaci idan aka cika takura musu to 'ya'yansu suna fantsama cikin gari su dinga shiga jikin al'umma da niyyar daukar fansa.
12-TSOHUWAR RIJIYA.
Wasu daga cikin Jinnul Hayyat suna zama a cikin tsohuwar Rijiya wadda ba ruwa a cikinta.
Idan suka shiga jikin mutum suna sa masa yawan jiri da saurin gajiya da mutuwar jiki.
Suna sa Bokaye su dinga jefa musu layoyi da sauran kayan tsibbu a cikin tsohuwar rijiya.
13- KAN BOLA.
Jinnul Mazabil da wasu nau'in Khadimul Hammam suna zama akan bola da sauran guraren qazanta
Suna shafar yara masu kai shara da tsakar rana ko masu wasa akan bola.
Suna sa yaro ya zama mai giggiwa sosai da firgita cikin dare da kuma rashin tsafta.
14- MAYANKA.
Wato inda ake yanka dabbobi.
Nau'in Aljanu mashaya jini kamar Tabriyqul Jinni, suna zama a guraren da ake ta'ammali da jini kamar mayankar dabbobi.
Idan suka shiga jikin mutum zai dinga yawan mafarkin an yanka dabbobi ko ya ganshi a kogin jini.
Suna shafar mata masu yin jinin haila da nifasi da jinin istihadha, hatta lokacin da mace zata haihu suna kokari su zo wajen don su shafeta ita da yaron.
Suna sa mace ta ji gefen cikinta ya nay mata qara ko yana motsi sannan kwanakin hailarta duk wata sai sun qaru ko kuma jini ya dinga kin dauke mata kwata-kwata.
Nan gaba za mu kawo cikakken bayani akan wadannan Aljanu mashaya jini insha Allahu.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment