MATSAYIN KAMBUN IDO A ADDININ MUSULUNCI.
MATSAYIN KAMBUN IDO A ADDININ MUSULUNCI.
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce "Daya bisa ukun mutanen da ke cikin kabari KAMBUN IDO ne ya kashe su".
Kuma ya ce "Yawancin wadanda suke mutuwa acikin al'umata, bayan hukuncin Allah da qaddararsa, to KAMBUN IDO ne yake kashe su".
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci.
Shi ga cikin wannan shudin rubutun kayi downloading Application dinmu, wanda za ka dinga samun rubututtukanmu cikin sauki
https://appsgeyser.io/7550770/Bashir%20Halilu%20Tarbiyyah%20Islamiyyah
Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin
rubutun, sai ka danna like
http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700.
MA'ANAR KAMBUN IDO.
Kambun ido wani dafi ne da Allah Yake halittarsa acikin idanun wasu mutane ko Aljanu, ta yadda idan suka kalli wani abu da idanunsu to wannan dafin zai iya fitowa ya harbi abinda su ka kalla, sai wannan abun ya samu wata nakasa ko ya kamu da cuta. Kambun ido yana iya yin tasiri ajikin mutum ko dabba ko bishiya ko abin hawa, da dai sauransu.
Kambun ido na iya sa wa mutum ya kamu da rashin lafiya ko ya fado daga abin hawansa ko kuma ya kashe mutum gaba daya.
Kamar yadda mu kay bayani tun a farko, Kambun ido halitta ce da Allah Ta'ala Ya ke yi a idanun wasu mutane, don haka ba koyarsa ake yi ba kuma ba siyensa ake ba. Wasu mutanen sun san suna da Kambun ido, wasu kuma ba su sani ba.
Da akwai Hadisai masu yawan gaske daga Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
da suke tabbatar da samuwar Kambun ido, da yadda ya kama wadansu da kuma yadda ake magance shi.
Ya zo acikin tafsirin suratu Yusufa عليه السلام
aya ta 67, inda Annabi Ya'aquba عليه السلام
ya ke cewa da `ya`yansa su goma sha daya, lokacin da za su tafi awon kayan abinci zuwa wani gari:-
"يا بَنِيَّ لا تَدخُلوا من باب واحد وادخلوا من أبواب متفرقة... "
Ma'ana "Ya ku `ya`yana, kada ku shiga (garin Misra) ta kofa guda daya, ku shiga ta kofofi mabambanta... "
Malamai su ka ce Annabi Ya'aquba عليه السلام
ya jiye musu tsoron Kambun idon mutane ne, domin dukkansu kyawawa ne kuma ga shi `ya`yan mutum daya, don haka mutane za suyi ta kallonsu suna tanka su, don haka ya ce kowa ya shiga garin ta kofarsa daban, inda a karshe Annabi Ya'aquba ya ce da su ya san dai hukunci na Allah ne, don haka ba dabararsa ce za ta kwace su ba.
Saboda haka Malamai su ka ce Kambun ido dadaddiyar cuta ce kuma har Annabawa suna neman tsari daga sharrinta, domin tana iya jefo mutum daga dutse ko ta jawo a saka rakuma tukunya, ma'ana ta yi sanadiyyar a yanka shi ko ya mutu.
WASU DAGA HADISAN MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم
DA SU KA YI MAGANA AKAN KAMBUN IDO.
1) Acikin littattafan Bukhari da Muslim, An kar6o daga Nana A'isha, Allah Ya kara yarda da ita, ta ce, "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya kasance yana umarta ta in yiwa kaina rukiyyah, (ko addu'a) daga sharrin Kambun ido".
في الصحيحين عن عائشة رضي الله عنها قالت : " كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يأمرني أن أسترقي من العين "
2) Haka nan an samu Hadisi daga Muslim da Ahmad da Tirmiziy kuma Tirmizy ya inganta shi, daga ibn Abbas Allah Ya kara yarda da su, daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce "Kambun ido gaskiya ne, da ace akwai wani abu da zai riga qaddara faruwa to da Kambun ido ne, don haka idan an nemi kuyi wanka to kuyi wankan".
Albaniy ma ya inganta Hadisin acikin littafinsa.
، وأخرج مسلم وأحمد والترمذي وصححه عن ابن عباس رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال : " العين حق ولو كان شيء سابق القدر لسبقته العين ، وإذا استغسلتم فاغسلوا " صححه الألباني في السلسلة الصحيحة ( 1251 ) .
3) Haka nan Imam Ahmad da Tirmiziy sun fitar da Hadisi daga Asma'u bint Umays, ta ce "Ya Manzon Allah, hakika `ya`yan gidan Ja'afar sun kamu da Kambun ido, shin ma iya yi musu ruqiyyah?".
Sai ya ce "Na'am, domin da da akwai abinda zai riga qaddara faruwa to da Kambun ido ne".
Shi ma Albaniy ya inganta shi acikin littafin Tirmiziy.
وأخرج الإمام أحمد والترمذي وصححه ، عن أسماء بنت عميس أنها قالت : يا رسول الله ، إن بني جعفر تصيبهم العين ، أفنسترقي لهم ؟ ، قال : نعم ، فلو كان شيء سابق القدر لسبقته العين . وصححه الألباني في صحيح الترمذي .
4) Abu Dawuda shi ma ya ruwaito daga Nana A'isha, Allah Ya kara yarda a gareta, ta ce "Ya kasance, ana umartar wanda yake da Kambun ido yayi alwala, sai wanda aka yi wa kambun idon ya yi wanka da ruwan".
Abu Dawuda ya ruwaito shi, Albaniy ya inganta shi.
وروى أبو داود عن عائشة رضي الله عنها قالت : كان يؤمر العائن فيتوضأ ثم يغسل منه المعين . وصححه الألباني في صحيح أبي داود .
5) Daga Abu Zarrin Algiffariy
رضي الله عنه
daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
yace : "Hakika Kambun ido ya kan shafi mutum da izinin Allah, har sai ya hau wani tudu mai tsawo sannan ya fado daga gare shi".
(Ahmad da Abu Ya'ala ne suka ruwaito shi).
6) An kar6o daga Nana Ummu Salamah رضي الله عنها
tace "
Watarana Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya kalli wata Kuyanga agidanta, sai ya ga wani baki-baki afuskarta, sai ya ce : "Lallai akwai kallo na Kambun ido a tare da ita, ku yi mata ruq'yah"
Bukhari ne ya ruwaito shi.
7) Haka nan an samu hadisi daga Jabir bin Abdillahil Ansariy رضي الله عنه
daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
yace : "Kambun ido ya kan shigar da mutum kabari, kuma ya kan shigar da rakumi murhu".
Abu Nu'aym.
SHARHI KADAN GAME DA ABUBUWANDA ZA MU IYA FAHIMTA DAGA WADANNAN HADISAI.
1-Kambun ido gaskiya ne, daga bakin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.
2- Har Annabawa suna gujewa Kambun ido kuma suan neman tsari daga gare shi.
3- Kambun ido tsohuwar cuta ce, da ta dade a duniya.
4- Kambun ido yana kashe mutum ko dabba.
5- Kambun ido yana iya sa wa mutum ya fado daga kan tudu ko bene ko abin hawa.
6- Kambun yana shafar mutane da dabbobi, don yana iya sawa yanzunnan rakumi ya shiga tukunyar girki.
7- Kambun ido yana da saurin tasiri, ta yadda yake kama wanda aka yiwa a take.
8- Ya hallarta ayiwa wanda aka yiwa kambun ido tofi ko rukiyyah.
9- Idan aka zargeka da cewa ka yi wa wani kambun ido, sai aka ce kayi wanka a ba shi ruwan, to kayi wankan, kada ka yi taurin kai, kamar yadda karin bayani zai zo nan gaba.
10- Saboda tasirin Kambun ido, da da akwai abinda zai riga abinda Allah Ya kaddara faruwa to da kambun ido ne, kamar yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya fada.
11- Kambun ido yana tasiri ne da iznin Allah.
BAMBANCIN KAMBUN IDO DA MAITA.
Wasu suna ganin kamar Kambun ido shi ne Maita amma gaskiya ba haka bane, Kambun ido daban, Maita daban. A dan takaice, ga bambancin da ke tsakaninsu
1-Kambun ido halitta ce, ba siya ake ko koya ba amma Maita ba halitta bace, koyarta ake yi ko a siya wajen masu ita.
2- Kambun ido ba tsafi bane amma Maita tsafi ce.
3- Mai Kambun ido ba da Aljanu yake aiki ba amma Mayu suna aiki ne da Aljanu.
4- Ba dukkan mai Kambun ido ne ya san yana da shi ba amma duk wani Maye ya san shi Maye ne.
5- Ingantattun Hadisai da Manyan Malamai sun yi magana akan Kambun ido amma ba su yi magana akan Maita ba, don haka ana shigar da ita ne acikin nau'o'in sihiri da bokanci.
6- Maye yana iya yin abubuwa da yawa da maitarsa, kamar ya ce yana ganin abinda yake cikinka ko ya ce ya ga wata cuta ajikinki ko kuma ya ce yana ba da magunguna amma shi mai Kambun ido tasiri daya kawai ya ke da shi, wato wata cutuwa ta samu abinda ya kalla da idonsa.
Bambanci yana da yawa amma wataran insha Allahu zan ware lokaci in yi bayani akan Maitar, ita kanta.
AL-JANU MA SUNA DA KAMBUN IDO.
Ba sai na yi dogon bayani anan ba amma dai Al-janu ana samun masu Kambun ido acikinsu kuma suna iya harbar Dan-Adam da shi, ya kamu da cuta ko ya gamu da wani mummunan hadari.
Yawanci za ka ga mutum ya kamu da cuta irinta Aljanu amma kuma in an masa ruq'yah sai a ga Aljani bai bayyana ba, to wata kila Kambun idon Aljanu ne a tare da shi.
SHIN KAMBUN IDO SHI NE KAMBUN BAKA?
Gaskiya dai da Hausa ne kawai ake cewa Kambun Baka.
Anan zan iya fadar abubuwa guda biyu, na farko dai ta iya yiwuwa shi Bahaushe yana nufin Kambun ido ne, shi ne yake cewa Kambun Baka. To indai haka ne, to wannan daidai ne kuma sananne a addinin Musulunci.
Na biyu kuma, indai Bahaushe yana nufin cewa Kambun Baka shi ma wani abu ne mai zaman kansa, kamar a ce idan mutum ya fadi wata magana a kanka mara kyau ko ya yabeka to wat cuta za ta iya kama ka, indai haka ne to Malamai sun ce Addinin Musulunci bai zo da maganar wani Kambun Baka ba.
YADDA AKE GANE KAMBUN IDO YA SAMU MUTUM
Yadda za ka gane Kambun ido ya sameka ko ya samu wani.
1- Akwai faduwa nan take a lokacin da mai abun ya kalle ka wani lokaci har da fitar dafara ko magagin mutuwa.
2- Fadowa daga Kan abin hawa ko wani tudu mai nisa, ba tare da wani sanannen dalili ba.
3- Ya kan zo da rashin lafiya mai tsanini tare da bayyana sunan wani mutum. Saidai abubuwa da yawa suna iya sawa mara lafiya ya dinga kiran sunan wani mutum. Daga ciki akwai shakuwa ko soyayya ko maita ko gaba ko kuma in ka je duba mara lafiya yana bacci, to in aka tashe shi ku ka gaisa, zai iya komawa yana kiran sunanka ko ya dinga ganin kana zuwar masa.
4- Ciwon kai wanda bayajin Magani idan kuma ka kwanta kayi ta ganin mutum a idonka.
5- Tauna hakora a lokacinda mutum ke cikin rashin lafiya.
6- Yawan rama ba tare da wani ciwo ba ga kuma cin abinci me yawa.
7- Karewar Jini ba tare da wani dalili ko wani ciwo ba.
8- Shiririta da rashin son yin abu mai amfani.
9- Kasala da komawar al'amura baya, kamar na karatu ko kasuwanci da dai sauransu.
10- Bayyanar wani tabo ko baqi-baqi akan fuskar mutum ko wani 6angare na jikinsa.
YADDA AKE NEMAN TSARI DAGA KAMBUN IDO.
Addu'o'i da aka ruwaito daga bakin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
1- An kar6o daga A'isha, matar Mazon Allah صلى الله عليه وسلم
ta ce "Manzon Allah
صلى الله عليه وسلم
ya kasance idan yay rashin lafiya sai Mala'ika Jibriylu yay masa ruq'yah, ya ce
َ بِاسْمِ اللَّهِ يُبْرِيكَ وَمِنْ كُلِّ دَاءٍ يَشْفِيكَ وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ وَشَرِّ كُلِّ ذِى عَيْنٍ. صحيح مسلم
"Bismillhi Yubriyka wa min kulli da'in yashfiyka, wa min sharri hasidin iza hasada, wa sharri ziy ainin"
Ma'ana: Da sunan Allah Ya warkar da kai, kuma Ya ba ka lafiya daga kowace irin cuta da sharrin mai hassada idan yay hassadar da kuma sharrin mai Kambun ido".
Sahih Muslim.
2- Daga Ubadata bin Samiti ya ce " Mala'ika Jibriylu ya zo wajen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
a lokacin yana zazza6i, sai ya ce
بِسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ ، مِنْ حَسَدِ حَاسِدٍ ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ ، اللَّهُ يَشْفِيكَ.
"Bismillahi arqiyka min kulli shay'in yu'uziyka, min sharri hasidin, wa min kulli ainin, Allahu Yashfiyka"
Ma'ana: "Inay maka ruq'yah da sunan Allah da kowane abu da yake cutar da kai, daga sharrin mai hassada, da kuma kowane irin Kambun ido, Allah Ya ba ka lafiya".
Acikin Sunan Ibn Majah kuma Albaniy ya ce hadisin Hasan ne.
3- An kar6o daga Abiy Sa'id cewa " Mala'ika Jibriylu ya zo wajen Annabi صلى الله عليه وسلم
sai ya ce da shi "Ya Muhammad, da alama ba ka da lafiya", sai ya ce "Na'am". Sai ya ce
َ بِاسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ مِنْ كُلِّ شَىْءٍ يُؤْذِيكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ اللَّهُ يَشْفِيكَ بِاسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ.
"Bismillahi arqiyka min kulli shay'in yu'uziyka, min sharri kulli nafsin au aini hasidin, Allahu Yashfiyka, bismillahi arqiyka".
Ma'ana: "Inay maka ruq'yah da sunan Allah daga kowane abu da yake cutar da kai, daga sharrin duk wani abu mai numfashi, ko sharrin Kambun idon mai hassada, Allah Ya ba ka lafiya, inay ma ka ruq'yah da sunan Allah".
Sahih Muslim.
4- An kar6o daga Aba Hurayrat, Allah Ya kara yarda a gare shi, ya ce "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya zo duba ni, sai ya ce da ni "Shin in yi maka ruq'yah da wata addu'a da Mala'ika Jibriylu ya zo min da ita? "
Sai na ce "Da uwata da ubana, na amince ya RasulAllahi". Sai ya ce
بِسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ وَاللَّهُ يَشْفِيكَ مِنْ كُلِّ دَاءٍ فِيكَ ( مِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ ) ثَلاثَ مَرَّاتٍ."
"Bismillahi arqiyka wAllahu Yashfiyka min kulli da'in fiyka (min sharrin naffasati fil uqadi, wa min sharri hasidin iza hasada) ". Sau uku..."
Har dai zuwa karshen hadisin amma Albaniy ya raunana shi, sedai tunda addu'a ce kuma ba wata cutarwa acikinta.
Ibn majah
5- An kar6o daga Nana A'isha, Allah Ya kara yarda a gareta, ta ce "Na kasance ina yiwa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ruq'yah daga Kambun ido, sai in dora hannuna akan kirjinsa, in ce
ُ امْسَحِ الْبَاسَ رَبَّ النَّاسِ بِيَدِكَ الشِّفَاءُ لا كَاشِفَ لَهُ ألا أَنْتَ .
"Imsahil ba'asa Rabban nas, bi yadiKash shifa'u, la kashifa lahu illa Anta".
Ma'ana: "Ka shafe cutar nan ya Ubangijin mutane, waraka tana hannunKa, babu mai yaye masa sai Kai".
Ahmad ne ya ruwaito.
Wadannan su ne wasu daga addu'o'i da ake yi domin neman tsari daga sharrin Kambun ido ko kuma warkewa idan an kamu.
Amma in ya kasance an samu wani mutum ya fadi yana shure-shure ko magagin mutuwa ko yana fitar da dafara daga bakinsa ko kuma ya fita daga hankalinsa, sai aka tabbatar cewa Kambun ido ne ya same shi, to sai a umarci wanda ake zaton shi ne yay masa kambun idon yayi alwala, kuma ya wanke ga6o6in jikinsa da madaurin wandonsa sai a kwararawa mara lafiyar ruwan ajikinsa, to zai mike nan take insha Allah, kamar yadda ya faru a zamanin Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.
Sannan idan aka zargeka cewa ka yi wa wani Kambun ido kuma aka nemi cewa kayi wanka a zuba masa ruwan, to kayi wankan kawai, kada ka tsaya da gardama, kamar dai yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ba da umarni acikin Hadisin da mu ka kawo.
Idan aka bi wannan hanya mutum bai mike ba ko kuma mara lafiyar bai warke ba ko kuma ba a gane wanda yay masa Kambun idonba, to zai fi kyau a kaishi wajen kwararren mai rukiyyah ko wajen wani Malami in kuma duka babu to sai a kaishi asibiti, watakila wata cutarce daban.
RIGAKAFI YA FI MAGANI.
Yiwa kanka da `ya`yanka Rigakafin kamuwa da cutar Kambun ido ta hanyar
1-Rage yada hotunanka dana `ya`yanka da sauran masoyanka a social media.
2-Ka san ko kisan irin kwalliyar da za ku dinga yi yayin shiga taron jama'ar da ba ku san irinsu ba.
3- A hana yara gantali a cikin gari lokacin da akay musu kwalliya ko kuma lokacin da babu cikakkiyar sutura ajikinsu.
4- Musamman mata, a dena saka sutura wacce za a iya ganin jikinki ko maza masu yin ball ba riga sai gajeren wando ko wanka a inda mutane suke ganinka.
5-Yawan neman tsari daga sharrin Kambun ido da kuma yin addu'a yayin fita daga gida ko hawa abin hawa da dai sauransu.
*Gaskiya bayani akan Kambun ido yana da yawan gaske, wanda na tabbatar ban kawo daya bisa biyar anan ba amma dai mai bukatar karin bayani zai iya komawa sauran littattafai.
Muna rokon Allah Ya tsare mu daga sharrin masu Kambun ido da sharrin Mahassada.
Insha Allahu nan gaba zan kawo bayani ne akan #HASSADA wacce itama wani lokaci take da tasiri mai kama da na Kambun ido.
Bashir Halilu.
Daga shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magungauna na Musulunci.
Yi download din Application dinmu wanda za ku dinga samun rubututtukanmu cikin sauki, acikin wannan shudin rubutun
https://appsgeyser.io/7550770/Bashir%20Halilu%20Tarbiyyah%20Islamiyyah.
Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin rubutun, sai ka danna like
http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment