TAKOBI MAI KAIFI DOMIN YAƘI DA MASIHIRTA DA BOKAYE. Fasarar Littafin Assarimul Battar.Daga shafin Bashir Halilu. (Darasi na 2).



BABI NA ƊAYA. 

1- Ma'anar Tsafi ko Sihiri. 

a) Tsafi a harshen Larabci. 

   * Mallam Al-Laith ya ce:
"Tsafi wani abu ne da ake yi domin neman kusantar shaiɗan tare da neman taimakonsa."

* Mallam Al-Azhari ya ce:
"Asalin tsafi shine karkatar da abu daga gaskiyarsa zuwa wani abu daban."

   *  Ibn Mandhur ya ce:
"Mai tsafi yana nuna ƙarya a matsayin gaskiya kuma yana karkatar da abu daga asalin gaskiyarsa, ya juyar da shi."

   * Shamar ya ruwaito daga Ibn Aisha ya ce:
"Larabawa sun kira tsafi ne da sunan 'sihr' saboda yana mayar da lafiya zuwa rashin lafiya."

  * Ibn Faris ya ce:
"Wasu Malaman sun ce tsafi yana nufin nuna ƙarya a matsayin gaskiya."

   * A cikin Littafin Al-Mu’jamul-Waseet, aka ce, tsafi yana nufin:
"Wani abu mai ɓoyayye wanda aka yi shi ga hanyar hikima."

  * A cikin Littafin Muheetil-Muheet kuma aka ce, tsafi yana nufin:
"Nuna abu a cikin mafi kyau ga mutane domin su ruɗu ko a ɓatar da hankalinsu."
---

b). Tsafi a Ma'anar Shari’ar Musjlunci. 

  *  Fakhruddinir-Razi ya ce:
"Tsafi a shari’a yana nufin duk wani abu da ba a ganin asalin yadda aka yi shi, wanda a ke bayyanar da abu ba kamar yadda yake ba, kuma yana aiki kamar yaudarar ido ko rufa_ido."

   * Ibn Qudama Al-Maqdisi ya ce:
"Tsafi shi ne karance-karance, maganganu ko wasu rubuce-rubuce da ake yi ko wani aiki da ke tasiri ga jikin wanda aka yi masa tsafin, zuciyarsa ko hankalinsa, ba tare da yin hulɗa kai tsaye da shi ba. Tsafi yana iya zama mai halakar da mutum, mai jawo rashin lafiya, ko kuma raba mutum da matarsa. Ya hana su kusantar juna, ko kuma ya jawo ƙiyayya ko soyayya tsakanin mutane."

    * Ibnul-Qayyim ya ce:
"Tsafi shi ne haɗuwar tasirin ruhohi masu mummunar hali da karfi na dabi’a wadanda suke aiki daga gare su, wato haɗuwar Aljanu da mutane domin a aikata sharri". 

---

Ma’anar Tsafi ko Sihiri a dunƙule. 

Tsafi shine: Cimma yarjejeniya tsakanin mai tsafi da Shaiɗan, inda mai tsafin ko Bokan zai aikata wasu abubuwa na haram ko kafirci domin samun taimakon shaiɗan wajen abin da yake so.

2- HANYOYIN DA BOKAYE SUKE BI DOMIN SAMUN KUSANCI DA SHAIƊANU. 

Bokaye ko masu neman kusanci da Shaiɗanu domin su dinga aikata sharri, Shaiɗanun suna saka su cewa, dole sai sun aikata wasu abubuwa na saɓo kafin Shaiɗanun su yarda da su. Munanan ayyukan sun haɗa da:- 

1. Sanya Alƙur’ani a ƙafafunsu su shiga banɗaki, suna taka shi a kafarsu. 

2. Rubuta ayoyin Alƙur’ani da abu mai  datti ko dauɗa. 

3. Rubuta ayoyin da jinin haila.

4. Rubuta ayoyi a ƙasan tafin ƙafafunsu.

5. Juya Suratul Fatiha a rubuce.

6. Yin sallah ba tare da tsarki ba.

7. Kasancewa cikin janaba har abada, ba sa wankan haila ko janaba. 

8. Yanka wabbobi da sunan shaiɗan ba tare da ambaton sunan Allah ba, sannan su jefar da naman a wurin da shaiɗan ya keɓance musu. 

9. Kiran taurari da sujada gare su.

10. Yin zina da mahaifiyarsu ko ‘ya’yansu na cikinsu.

11. Rubuta kalmomin kafirci cikin haruffa marasa ma’ana.
---

3- YADDA AKE ƘULLA ALƘAWARI TSAKANIN BOKA DA SHAIƊAN. 

    Shaiɗan ba ya taimaka wa mai tsafi sai da abin da zai ba shi matsayin kafirci. Idan mai tsafi ya kasa yin abin da shaiɗan ya umarta, shaiɗan zai daina yi masa hidima, ya gudu ya bar shi, bayan Mai tsafi da shaiɗan sun yi haɗin kai a kan saba wa Allah.

4- YADDA ZA KA GANE BOKA. 

    Idan aka dubi fuskar mai tsafi, za a ga duhun kafirci ya lullube fuskar, kamar hadari mai baƙi. Idan aka san shi sosai, za a gano yana cikin mummunan rayuwa tare da matarsa da ‘ya’yansa, har ma da kansa. Ba ya samun natsuwa, kuma yakan firgita a cikin barci sau da yawa. Kuma shaiɗanu suna cutar da shi da iyalansa.

Allah Madaukaki ya ce:
"Duk wanda ya juya baya daga ambaton Allah, to, zai rayu cikin tsananin damuwa."
(Suratul Taha: 124). 

Alhamdu lillahi. Wannan shi ne ƙarshen darasi mu na biyu acikin wannan littafi. Za mu tashi darasi na uku, in sha Allah. 

  Duk mai bukatar sauraron wannan littafi ta bidiyo cikin harshen Hausa sai ya duba shafina na tiktok mai suna 'Shafin Bashir Halilu' ko kuma ka karanta a rubuce ga facebook a shafina mai suna 'Bashir Halilu'. 

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da harhaɗa magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts