TAKOBI MAI KAIFI DON YAƘI DA MUGWAYEN MASIHIRTA, BOKAYE. Darasi na ɗaya (1).
Gabatarwar mai fassara.
Ni Bashir Halilu ina gabatar muku da wannan littafi wanda na yi alƙawarin da yaddar Allah zan dinga kawo muku fassarar sa a shafina na tiktok da kuma facebook.
Littafin yana magana ne akan sihiri. Marubucin ya bayyana ma’anar sihiri, ya kuma kawo hujjoji daga Alƙur’ani mai girma da Hadisai kan gaskiyar samuwar sihiri tare da maganganun malamai game da yadda sihiri ya ke. Ya bayyana rabe-raben sihiri a fahimtar Malamai da dama, kamar Fakhruddin Al-Razi da Al-Raghib, sannan ya bayyana hanyoyin da masu sihiri ke bi don kiran Aljannu da yadda ake mallakar Aljanu da saka su ayyuka. Har ila yau, ya bayyana hukuncin sihiri a cikin shari’ar Musulunci da hukuncin Masihirta, Bokaye.
Marubucin wannan littafi "As-Sarimul -Battar Fit -Tasaddi Lis-Saharatil -Ashrar": shi ne Wahid bin Abdussalam Bali, wanda aka haifa a Masar. Ya rubuta littattafai da dama kamar Fakihatul-Majalis, Bidayatul-Muttafiqah, Arba'in Khata'an Lil-Lisan, Sahihul-Adabul -Islamiyyah, da sauransu.
Abubuwan da ke cikin littafin "As-Sarimul Battar Fit-Tasaddi Lis-Saharatil-Ashrar".
Littafin yana da babi-babi kamar haka:
Babi na farko: (1)
1- Ma’anar sihiri a harshen Larabci.
2- Ma’anar sihiri a cikin shari’a.
3- Wasu hanyoyin da masu sihiri ke bi don samun kusanci da Shaiɗan.
Babi na biyu: (2)
1- Sihiri a hasken Alƙur’ani da Sunnah .
2- Hujjoji kan tabbacin samuwar Aljannu da shaiɗanu.
a) Hujjoji daga Alƙur’ani.
b) Hujjoji daga Hadisai.
c) Maganganun malamai kan sihiri.
Babi na uku: (3)
1- Rabe-raben sihiri.
Rabe-rabensa bisa fahimtar Al-Razi da Al-Raghib.
2- Bayanin nau’o’in sihiri.
Babi na huɗu:(4)
1- Hanyoyin da masu sihiri ke bi don kiran Aljannu.
2- Yarjejeniya tsakanin masu sihiri da shaiɗanu.
3) Alamomin da za a gane mai sihiri.
Babi na biyar: (5)
1- Hukuncin mai sihiri a shari’ar Musulunci.
2- Hukuncin mai sihiri daga cikin Littafin Allah.
3- Shin ana iya warware sihiri da sihiri?
4- Shin ya halatta mutum ya koyi yadda ake sihiri?
5- Bambanci tsakanin sihiri, karama, da mu’ujiza.
Babi na shida: (6)
1- Warware sihiri:
(a) Sihirin raba aure: Alamomi da hanyoyin warwarewa.
(b) Sihirin soyayya: Alamomi, yadda ake yi, sakamako mara kyau, da hanyoyin warwarewa.
Babi na bakwai: (7)
1- Magance matsalar rashin sha’awa ga mace ko namiji.
2- Bambanci tsakanin rashin haihuwa ta dabi’a da wanda aljannu suka jawo.
3- Hanyoyin warkar da matsalar.
Babi na takwas: (8)
1- Kariya daga sihiri:
(a) Yin alwala.
(b) Sallah cikin jam’i.
(c) Tashi tsakar dare yin ibada.
(d) Neman kariya kafin shiga banɗaki da yayin saduwa da iyali.
Babi na tara: (9)
1- Maganin Kambun ido.
(a) Hujjoji daga Alƙur’ani da Hadisai kan tasirin Kambun ido.
(b) Bambanci tsakanin Kambun ido da hassadar zuciya.
Littafin dai ya haɗa da bayanai dalla-dalla da hanyoyin warware matsalolin da suka shafi sihiri da hassada a rayuwar Musulmai.
Duk mai bukatar sanin amfanin wani magani ko wani ko yadda ake magane wata cuta ko tambaya akan abubuwan da mu ka kawo zai iya rubuta mana a comment, za mu kawo, insha Allah.
Ga ma su bibiyarmu a facebook sunan shafina 'Bashir Halilu'. Masu son kallon video ta tiktok kuma sai duba 'Shafin Bashir Halilu'.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment