IBLIS YA NEMI YA TUBA
Wata rana Iblis ya zo wajen Annabi Musa ﷺ ya ce masa "Ya Musa!, kai ne wanda Allah Ya za6eka acikin mutane da ManzancinSa da kuma zancenSa. Ni kuma ni ne na fi kowa zunubi a cikin mutane, to ina so ne na tuba. Don haka ka roqar min Allah Ya kar6i tubana".
Sai kuwa Annabi Musa ﷺ yay addu'a. Sai aka ce "Ya Musa haqiqa an kar6i roqonka, indai Iblis ya tuba za a yafe masa"
Da Annabi Musa ﷺ ya gamu da Iblis sai ya gaya masa cewa "Ya Iblis haqiqa an ce kaywa qabarin Annabi Adam sujjada za a kar6i tubanka".
Da jin haka sai Iblis yay fushi, girman kai ya kama shi, ya cewa Annabi Musa ﷺ "Ban yi masa sujjada da ransa ba sannan zan yi masa sujjada bayan ya mutu?!"
Sannan ya ce " Ya Musa lallai kana da matsayi a wajen Allah tunda har ka nemar min tuba kuma aka ba ka. To ka dinga tunawa da sharrina a wasu gurare guda uku, ni kuma ba zan ta6a halakar da kai ta hanyarsu ba.
Ya ce " Ka tuna ni lokacin da kake fushi. Domin lokacin wasu-wasi na yake shiga cikin zuciyarka, idona a cikin idonka kuma ina zagayawa a jikinka kamar yadda jini yake zagayawa.
Na biyu ka tuna da sharrina lokacin da ka hadu da abokan yaqi. Domin ina zuwarwa mutum lokacin da ya gamu da abokan gaba a filin yaqi, sai in dinga tuna masa iyalinsa da dukiyarsa".
Shaidan ya ce "Sannan na uku; kada ka kuskura ka ke6ance da wata mace wacce ba maharramarka ba. Domin lokacin zan dinga aika sha'awarka zuwa gareta da kuma sha'awarta zuwa gare ka".
(رواه أبوبكر القرشي بسنده إلى ابن عمر رضي الله عنه).
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
facebook tarbiyyah.islamiyyah.3@fb.com
https://plus.google.com/+BashirHalilu/posts/aAS3EMbDi8Z?_utm_source=1-2-2
whatsApp +2348162600700
Allah yarabamu da sherin shedan ameen.
ReplyDeleteAssalamu alaikum mallam da fatan kana lfy sunana Ismail ina Dan bibiyar karatutukar ka amma idan baka damu bah zan dan yi maka wani tambaya
Delete