SARARI RUKIYYAH DA KUNNENKA
https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/41
SAURARI WADANNAN AUDIO DIN.
Idan baka iya mu'amalantar Aljani yayin rukiyyah ba.
1) Zai iya komawa jikinka ko jikin `yan kallo.
2) Zai yaudareka, yay ta baka labarai, har ya samu hanya, ya gudu.
3) Zai iya yiwuwa ka wahalar da Aljanin, ta yadda zai kasa fita daga jikin mutum.
4) Rashin sanin yadda ake fidda Aljani, ka iya sawa ka ba shi umarnin fita ta inda zai cutar da mara lafiyar ko kuma shi Aljanin ya fita tanan.
5) Yin abubuwa marasa amfani da Aljani, kamar doguwar hira, yay ta baka labarai marasa amfani ko kuma ya dinga zaginka kana ramawa, kan janyowa mara lafiyar karin tuburewar jikinsa.
6) Mafi amfanin abinda zaka tambayi Aljani su ne
a) Sunansa.
b) Dalilin shigarsa jikin mutum (asiri ne ko ba asiri bane).
c) Adadinsu ajikin mara lafiyar.
d) Ta inda yake shiga jikin mara lafiyar da kuma inda yake zama.
e) Guraren da ya sakawa mutum cuta.
f) Addinin Aljanin (don kasan yadda zaka mu'amalance shi).
In kaga dama kuma ba sai ka tambaye shi wani abu ba, don ba dole bane.
7) Mafi muhimmancin umarnin da zaka baiwa Aljani:
a) ya cire cututtukan da ya saka ajikin mara lafiyar.
b) Yayi alkawarin ba zai sake dawowa jikinsa ba, ko ya bar masa cuta, kuma yayi alkawarin ba zai sake turo masa wasu Aljanun ba.
c) Ya fita ta inda ba zai cutar da mara lafiyarba.
In kaga dama kuma umarni daya kawai zaka ba shi, wato ya fita.
Ga wasu ruqiyyoyi don ku ji yadda mukay da wasu Aljanun.
Wadannan links din na Telegram ne, don haka suna da saukin budewa a saurara.
1- Adam https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/36
2- Sulaiman https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/37
3- Maryam https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/38
4- Zainab https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/39
5- Amarya mai aman reza https://t.me/tarbiyyahislamiyyah/35
Ko lambobinmu na whatsApp 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment